Taro Ya Rikice: Trump Ya Shiga Dimuwa bayan Wani Ya Suma Ana tsaka da Ganawa
- Wani bako ya fadi a lokacin wani taro da Shugaba Donald Trump ya jagoranta a Fadar White House a Amurka
- Majiyoyin kasar wajen sun tabbatar da cewa hakan ya faru ne yayin da ake magana kan rage farashin maganin kiba
- Shugaba Trump da sauran jami’ai sun dakatar da taron na ɗan lokaci yayin da likitoci suka taimaka wa mutumin da ya suma
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washigton DC, US - Shugaba Donald Trump ya kadu bayan wani jami'in kiwon lafiya ya suma lokacin da ake cikin taro.
An tabbatar da cewa mutumin ya fadi ne kusa da Donald Trump yayin da yake jagorantar wata ganawa a fadar 'White House' da ke Amurka.

Source: Youtube
Wani jami'in lafiya ya suma a gaban Trump
New York Post ta ce bakon ya fadi ne a lokacin da Shugaban Amurka, Donald Trump, ke sauraron jawabin yayin taron a yau Alhamis 6 ga watan Nuwambar 2025.

Kara karanta wannan
Kisan kiristoci: Yan Majalisa 31 sun goyi bayan matakin da Amurka ta dauka kan Najeriya
Lamarin ya faru ne yayin da ake bayyana shirin rage farashin magungunan kiba, inda wani bako daga cikin wakilan kamfanonin kiwon lafiya ya firgita ya fadi ya suma.
Shugabar yada labarai ta Fadar, Karoline Leavitt, ta bayyana cewa mutumin da ya suma, wakilin daya daga cikin kamfanonin kiwon lafiya ne, kuma lamarin ya faru ne yayin da Shugaban kamfanin Eli Lilly, David Ricks, ke magana.
Shaidu sun ce mutumin yana tsaye a bayan teburin shugaban kasa tare da wasu jami’an gwamnati da manyan shugabannin masana’antar magunguna lokacin da ya fara firgita ya fadi ƙasa.
“Lafiya kalau?” in ji Ricks yayin da jami’in kula da Medicare da Medicaid, Mehmet Oz, da wasu suka yi gaggawar taimaka masa.

Source: Getty Images
Abin da Trump ya yi bayan faruwar lamarin
Shugaba Trump ya tashi daga kan teburinsa don kallon halin da ake ciki, yayin da ‘yan jarida suka fita daga ɗakin na ɗan lokaci.
Bayan wani lokaci, Fadar ta tabbatar cewa mutumin ya samu kulawar gaggawa kuma yana cikin koshin lafiya,Trump ya ce:
“Kun ga ya fadi amma yanzu yana lafiya. Likitoci sun kula da shi.”
Wannan dai shi ne karo na biyu da irin wannan lamari ke faruwa a White House a bana, bayan wata yarinya ta suma a watan Afrilu lokacin rantsar da Mehmet Oz, kafin daga baya ta farfado.
Rahoton Sky News Australia ya ce Trump yana sanar da yarjejeniya da za ta faɗaɗa damar samun magungunan kiba ga miliyoyin ‘yan Amurka cikin sauƙi da rahusa.
Barazanar Trump: Yan majalisa 31 sun goyi bayansa
Kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya samu goyon baya kan matakin da ya dauka na sanya Najeriya cikin kasashe masu matsala.
An tabbatar da cewa wasu yan Majalisar Dokoki 31 sun yaba wa Trump, suna mai cewa hakan ya farfado da kimar Kiristoci da ake kashewa a Najeriya.
A cewar yan Majalisar, kungiyoyi 'yan ta'adda masu tsattsauran ra'ayin addini na kashe dubban Kiristoci a kowace shekara, inda suka ce ya kamata a dakile hakan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
