Trump Ya Kara Nuna Yatsa ga Najeriya, Ya Ce ba za a Ji da Dadi ba
- Shugaban Amurka, Donald J Trump ya sake nanata barazanar kawo hari zuwa kasar bayan barazanar da ya yi a makon da ya wuce
- Shugaban ya kafe kai da fata cewa an ware kiristoci, ana masu kisan kare dangi yayin da gwamnati ta zura ido ba ta dauki mataki ba
- Duk da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta karyata zargin, Donald J. Trump ya fi yarda kalamansa na cewa ana kashe kiristoci da gangan
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
United States of America – Shugaban Amurka Donald Trump ya kara yin maganganu masu tsauri a kan yiwuwar amfani da karfin soja a kan Najeriya saboda ikirarinsa kisan kiristoci.
A ranar 31 ga Oktoba Shugaban Amurka ya sanya Najeriya a cikin jerin kasashen da ke kashe kiristoci saboda banbamcin addininsu.

Kara karanta wannan
Kisan kiristoci: Kasar Rasha ta tsoma baki kan shirin Amurka na kai farmaki Najeriya

Source: Getty Images
A cikin wani bidiyo da ya saki a shafinsa na Facebook, Trump ya gargadi gwamnatin Najeriya da ta kuka da kanta, ta kuma fara daukar matakin gyara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Donald Trump ya sake gargadin Najeriya
The Cable ta wallafa cewa Trump ya yi tir da kisan da ya ce Musulmi masu tsattsauran ra'ayi na yi wa kiristocin Najeriya.
Ya kara da gargaɗin cewa zai ɗauki mataki nan da nan idan hukumomin Najeriya suka gaza takawa wadanda ke kashe-kashen nan burki.

Source: Twitter
Trump ya ce Amurka za ta dakatar da duk wani tallafi ga Najeriya idan tashin hankali ya ci gaba, ya zai turo dakarun soji ko ta sama ko ta kasa zuwa kasar.
Ya umarci Ma’aikatar Yaki da ta fara shiri don yiwuwar daukar matakin soja, yana mai cewa duk wani hari da za a kawo zai zama mai tsanani kuma ba za a ji dadinsa ba.
Trump ya nuna damuwa kan kiristoci
Shugaban kasar Amurka, ya bayyana cewa addinin Kirista a Najeriya na fuskantar barazana inda ake kashe dubunnan 'yan uwansa a tafarkin Yesu.
Trump ya umarci dan majalisa Riley Moore da Tom Cole su yi bincike gaggawa su ba shi rahoto, domim Amurka ba za ta zuba ido ana kashe masu 'yan uwa' ba.
Ya ce Amurka ba za ta tsaya ta kalle su ba yayin da irin wannan barna ke faruwa a Najeriya da wasu kasashe, tana mai cewa tana shirye ta kare Kiristoci a duniya.
Masu sharhi da masana tsaro a Najeriya sun bambanta ra'ayi: wasu na cewa barazanar na iya jefa yankin cikin rikici, wasu na ganin tilas gwamnati ta kara himma wajen kare jama'a.
Jama'a sun yi martani kan barazanar Trump
Mazauna Kano kamar Jamil Ahmed da Muhammad Lawan na ganin Amurka magana ne kawai, amma ba za ta kawo hari ba.
Jamila ta. ce:
"Idan ma sun kawo hari, lokacinmu ne ya yi. Amma ina ga ba za su kawo hari ba.
Muhammad Lawan na cewa:
"Dama Amurka munafukai ne. A gama da Gaza an taho Najeriya."
Trump: Amurka ta sako Miyetti Allah a gaba
A baya, mun wallafa cewa majalisar wakilai ta ƙasa ta kai wani kudiri mai lamba H. Res. 860, wanda Christopher Smith ya gabatar tare da hadin gwiwar Paul Huizenga.
Kudirin ya bukaci ma’aikatar harkokin wajen Amurka da kuma ma’aikatar kudi su kakaba takunkumi a kan Miyetti Allah da wasu kungiyoyi da ake zargin suna taka rawa wajen ta'addanci.
‘Yan majalisar sun nuna damuwa kan yadda ake zargin ana kisan Kiristoci, lalata wuraren ibada, da kuma rashin hukunci ga masu laifin da su ka shafi ta'addanci a Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

