Trump: Sojojin Amurka Sun Tsara yadda za Su Kawo Farmaki Najeriya

Trump: Sojojin Amurka Sun Tsara yadda za Su Kawo Farmaki Najeriya

  • Sojojin Amurka na shirin kai hare-hare a Najeriya bayan umarnin Shugaba Donald Trump kan zargin karya na kisan Kiristoci
  • Rahotanni sun ce za a gabatar da farmaki har kala uku: mai nauyi, matsakaici, da mai sauƙi, domin takaita tashin hankali
  • A baya dai shugaba Trump ya gargadi gwamnatin Bola Tinubu da cewa Amurka za ta dauki mataki da sauri kan 'yan ta'adda

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amurka – Rundunar sojin Amurka ta gabatar da cikakken shiri ga ma’aikatar yaki domin yiwuwar kai hare-hare Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan umarnin shugaba Donald Trump kan zargin kisan Kiristoci da ake yadawa a kafafen yada labarai.

Danald Trump
Shugaba Trump da jiragen yakin Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jaridar New York Times ta ruwaito cewa, kwamandan rundunar sojin yankin Afirka ya aika da na'ukan farmaki uku ga ministan ma’aikatar, Pete Hegseth, a farkon wannan makon.

Kara karanta wannan

Kisan kiristoci: Kasar Rasha ta tsoma baki kan shirin Amurka na kai farmaki Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matakai 3 na farmakin Amurka a Najeriya

Rahoton ya bayyana cewa shirin ya kasu kashi uku: mai nauyi, matsakaici, da mai sauƙi — kowanne yana nufin bai wa Amurka damar yin amfani da karfin soja.

Ya kara da cewa “farmaki mai nauyi” shi ne mafi karfi, wanda zai shafi tura jiragen yaki da manyan jiragen ruwa zuwa Tekun Guinea, a kusa da Najeriya.

A karkashin wannan tsari, Amurka za ta iya amfani da jiragen yaki masu linzami ko masu nisan zango domin kai hare-hare Arewacin Najeriya.

A gefe guda kuma, “matsakaicin farmaki” ya shafi amfani da jiragen marasa matuka wajen kai farmaki kan sansanonin mayaka, motoci da sansanoni a Arewacin kasar.

Sojojin sun ce jiragen nan na iya yin sintiri na tsawon sa’o’i kafin su kai hari, yayin da sauran jami’an leken asiri za su tattara bayanai kan yadda mayakan ke motsi domin samun kai hari.

Farmaki “mai sauƙi” kuwa, ya shafi hadin gwiwa tsakanin Amurka da gwamnatin Najeriya wajen bai wa dakarun kasar horo da kayan aiki domin yakar Boko Haram da sauran 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan

"Ba don kiristoci ba ne," An jero abubuwa 3 da suka harzuka Amurka ta fara shirin kawo hari Najeriya

Martanin wasu sojojin Amurka

Wani jami’in soja ya ce babban manufar shirin ita ce “murkushe 'yan ta'adda a Arewacin Najeriya, kare Kiristoci daga hare-haren makamai, da kawo karshen tayar da kayar baya.

Sai dai wasu tsofaffin hafsoshin soja sun nuna damuwa game da wannan shiri, suna masu gargadi cewa zai iya zama kamar kuskuren yakin Iraki da Afghanistan.

Janar Paul D. Eaton da ya yi ritaya daga rundunar soja, ya bayyana cewa “zai zama babban kuskure” idan Amurka ta sake fadawa irin wannan yaki.

Bola Tinubu, Donald Trump
Shugaba Bola Tinubu da Donald Trump. Hoto: Bayo Onanuga|The White House
Source: Getty Images

Ya kara da cewa jama’an Amurka ba su da sha’awar sake maimaita irin yakin da aka yi a Iraki ko Afghanistan.

Premium Times ta rahoto cewa wasu jami’an soja sun bayyana cewa hari ta sama da Trump ke son yi zai iya tayar da hankali kuma ba zai warware matsalar ba.

Legit ta tattauna da Abdulrahim Usman

A tattaunawa da Legit Hausa, wani magidanci da ya fuskanci matsalolin rashin tsaro a Arewa maso Gabas ya ce bai kamata Amurka ta yi wa Najeriya barazana ba.

Kara karanta wannan

Janye biza: Wole Soyinka ya dura kan Trump, ya kira shi mai mulkin kama karya

Abdulrahim Usman ya ce:

"Kowa ya fuskanci matsalolin tsaro, Musulmi da Kirista. Kamata ya yi Amurka ta tallafawa Najeriya ba barazana ba."
"Najeriya ba sa'ar Amurka ba ce, kamata ya yi Trump ya rika musayar yawu da irinsu Rasha da China ba Najeriya ba."

Trump ya yi zargin kisan Kiristoci

A makon da ya gabata, mun kawo muku cewa Shugaba Donald Trump ya yi barazanar kai farmaki Najeriya kan zargin kashe Kiristoci.

Trump ya sanya Najeriya cikin jerin kasashe masu matsala (CPC), tare da dakatar da sayar da makamai da taimako ga kasar.

Matakin ya biyo bayan matsin lamba daga wasu ‘yan majalisar Amurka masu ra’ayin rikau, wadanda ke zargin Najeriya da hana ‘yancin addini.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng