Amurka na Shirin Kawo Farmaki Najeriya, Jirgi Ya Fado kan Masana'antu, An Rasa Rayuka
- Jirgin sama mai dakon kaya na kamfanin UPS ya gamu da hatsari jim kadan bayan tashinsa daga filin jirgin Louisville Muhammad Ali a Amurka
- Gwamnan jihar Kentucky, Andy Beshear ya ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon hatsarin jirgin sun kai tara
- Ya ce har yanzu jami'an kashe gobara na kokarin kashe wutar da ta kama a wurin da jirgin ya fado kuma da yiwuwar a samu karin gawarwaki
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Amurka - Adadin mutanen da suka mutu sun kai tara yayin da wani jirgin sama mai dakon kaya ya yi hatsari a kasar Amurka.
Jirgin saman na kamfanin UPS ya yi hatsarin ne birnin Louisville da yammacin ranar Talata, kuma ana zaton adadin mutanen da suka mutu zai iya karuwa.

Source: Getty Images
Gwamnan Jihar Kentucky da ke kasar Amurka, Andy Beshear, a ranar Laraba ya tabbatar da aukuwar hatsarin, ya ce ana ci gaba da aikin ceto, cewar rahoton NBC News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jirgin sama ya rikito kan masana'antu
Jirgin saman kirar McDonnell Douglas MD-11, ya fado ne a hanyarsa ta zuwa Hawaii da misalin ƙarfe 5:15 na yamma jim kadan bayan tashinsa daga Filin jirgin Louisville Muhammad Ali.
Jirgin ya kama da wuta bayan ya faɗa cikin wasu masana’antun kasuwanci da ke kusa da filin jirgin saman.
Gwamna Beshear ya bayyana wannan mummunan lamari da cewa, “abin tausayi ne da ba za a iya kwatanta shi ba.”
"Adadin mutanen da aka rasa ya kai akalla tara yanzu, kuma akwai yiwuwar samun kari. Wannan lokaci ne da iyalan waɗannan mutane ke buƙatar addu’a, ƙauna da tallafi.”
Gwamna Beshear ya ce iyalai 16 ne suka sanar da cewa ba su san inda ‘yan uwansu suke ba, yayin da ake ci gaba da aikin ceto da bincike tun daren Talata zuwa safiyar Laraba.
Kamfanin jiragen UPS ya yi magana
Kamfanin UPS ya tabbatar da cewa ma'aikatan jirgi uku ne ke cikin jirgin lokacin hatsarin, amma ya ce har yanzu ba a tabbatar da adadin waɗanda suka jikkata ko suka mutu ba.
Rahotanni sun nuna cewa wannan hatsari ne mafi muni a tarihin kamfanin sufurin jiragen sama na UPS.

Source: Getty Images
Hotuna daga wurin hatsarin sun nuna hayakin da ya tashi yayin da ma’aikatan kashe gobara ke zuba ruwa domin kashe wuta da ta tashi daga wajen.
Hukumomin Amurka sun fara gudanar da bincike domin gano abin da ya haddasa wannan hatsari, kamar yadda BBC News ta kawo.
Jirgi ya fada cikin teku a China
A wani labarin, kun ji cewa jirgin sama na dakon kaya ya sauka daga kan titinsa, ya fada cikin tekun da ke bayan filin jirgi a birnin Hong Kong na kasar China.
An ruwaito cewa jirgin ya bugi wata motar sintiri kafin daga bisani ya afka cikin teku, lamarin da ya zama ajalin mutane biyu da ke cikin motar.
Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Hong Kong ta kaddamar da bincike na musamman don gano musabbabin wannan hadari.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


