'Ta Sama ko ta Kasa,' Donald Trump Ya Fadi Shirinsa kan Kai Hare Hare Najeriya
- Shugaba Donald Trump ya ce Amurka na iya tura sojojinta ko kai hare-haren sama don dakatar da kashe Kiristoci a Najeriya
- Najeriya dai ta ce za ta karɓi taimakon Amurka idan za ta mutunta ikon ƙasar, yayin da ta soki kalaman Trump na baya bayan nan
- Shugaba Tinubu ya kare Najeriya daga zargin wariyar addini, yana mai cewa ƙasar tana kiyaye ‘yancin addini ga kowa da kowa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amurka - Shugaba Donald Trump, ya yi barazanar cewa sojojin Amurka na iya shiga Najeriya ko kuma su kai hari ta sama domin hana abin da ya kira “kisan kare dangi kan Kiristoci.”
A cikin sakon da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Trump ya zargi “’yan ta’adda masu jihadi' da laifin “kashe Kiristoci,” yana mai cewa Kiristanci na fuskantar barazana a Najeriya.

Source: Facebook
Trump na barazanar kai hari Najeriya
Kafar watsa labarai ta Sky News ta rahoto Trump, lokacin da yake magana da ’yan jarida a cikin jirgin Air Force One a ranar Lahadi, yana cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ana kashe Kiristoci da yawa a Najeriya... Ba za mu bar hakan ya ci gaba ba.”
Trump bai bayar da hujja ba, amma ya ce Amurka na iya daukar matakin soja, ciki har da tura dakarun sojojin kasa ko kai hare-hare ta sama.
Najeriya ta gargaɗi Amurka kan tsoma baki
A martaninta, Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa tana maraba da taimakon Amurka wajen yaƙi da ta’addanci, amma ta jaddada cewa dole ne ta mutunta ikon ƙasarta.
Daniel Bwala, mai ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan yada manufofin gwamnati, ya faɗa wa kafar labaran Reuters cewa:
“Za mu karɓi taimakon Amurka muddin za ta mutunta ikon ƙasarmu.”
Sai dai Bwala ya yi ƙoƙarin rage zafin maganganun, yana mai cewa Najeriya na amfani da diflomasiyya wajen martani ga kalaman Trump da ya kira Najeriya “wulaƙantacciyar ƙasa.”

Kara karanta wannan
Tsohon hafsan tsaro ya gargadi Trump bayan barazanar kawo hari Najeriya, Buratai ya bada mafita
Hakazalika, Shugaba Tinubu ya mayar da martani ga kalaman Trump, yana cewa Najeriya na ci gaba da kare ‘yancin addini da imani ga kowane ɗan ƙasa.
Ya bukaci ƙasashen duniya su gane cewa Najeriya ƙasa ce mai hadin kai tsakanin addinai, inda Musulmai da Kiristoci ke rayuwa tare duk da barazanar ‘yan ta’adda.

Source: Getty Images
Amurka ta dade tana sa ido kan Najeriya
Najeriya na cikin jerin kasashen da Amurka ke zargi da take hakkin ‘yancin addini tare da Koriya ta Arewa, Iran, Rasha, Saudiya, da China.
Kungiyar Boko Haram, wadda ta sace ‘yan matan Chibok a 2014, ta kasance cikin wadanda suka fi yin laifuffukan keta ‘yancin addini.
Rahoton hukumar Amurka ta 2021 ya ce mutane fiye da 37,000 ne suka mutu sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda a Najeriya tun 2011.
Duk da cewa Trump ya yi ikirarin cewa ana kashe Kiristoci, masana sun bayyana cewa yawancin wadanda ake kashewa Musulmai ne a yankin Arewacin ƙasar.
Gumi ya ba Tinubu shawara kan Amurka
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sheikh Ahmad Gumi ya ba Shugaba Bola Tinubu shawara bayan barazanar kasar Amurka na kawo hari Najeriya.
Malamin addinin ya bukaci Shugaba Tinubu ya dauki mataki kan barazanar Donald Trump ga Najeriya, yayin da ya kira hakan cin mutunci.
Gumi ya ce Najeriya na da sauran zabin bunkasar tattalin arziki da hadin kan soja, ba lallai sai ta dogara da Amurka ba don cimma haka ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

