Sanatan Amurka Ya Taso Najeriya, Zai Gabatar da Kudin Hana Shari'ar Musulunci da Batanci
- Sanata Ted Cruz na kasar Amurka ya sha alwashin gabatar da kudiri domin haramta aiwatar da shari'ar Musulunci a Najeriya
- Wannan na zuwa ne bayan shugaban Amurka, Donald Trump ya ce akwai babbar damuwa kan zargin zaluntar Kiristoci a kasar
- A halin yanzu akwai jihohi 12 da ke amfani da dokar shari'a a Arewacin Najeriya, wadanda mafi yawancin jama'arsu musulmai ne
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Amurka - Sanatan Amurka, Ted Cruz ya sha alwashin gabatar da kudirin doka domin hana aiwatar da dokokin Shari’a da batanci a Najeriya.

Kara karanta wannan
Tinubu ya maida martani ga Shugaban Amurka, Trump kan zargin kisan kiristoci a Najeriya
Hakan na zuwa ne bayan Shugaba Donald Trump ya sanya sunan kasar cikin jerin “Kasashen da ke da Babban Damuwa kan ’Yancin Addini” saboda zargin yi wa Kiristoci kisan kare dangi.

Source: Getty Images
A cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafinsa na X, Sanata Cruz, dan jam’iyyar Republican daga jihar Texas, ya ce zai gabatar da kudirin don dakile aiwatar da dokokin shari'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatan Amurka ya taso Najeriya gaba
Ya ce wannan mataki ya yi daidai da kokarinsa na kare yancin Kiristocin da ake zargin ana zalunta a Najeriya.
"Na yi matukar jin dadi da wannan matakin da Shugaba Trump ya dauka. Na dade ina fafutukar dakile kashe-kashe da zaluncin Kiristoci a Najeriya.
"A wannan shekarar na gabatar da kudirin doka da zai tabbatar da wannan matsayin da aka dauka yau.”
Ted Cruz na son hana shari'a a Najeriya
Ya kara da cewa kudirin da zai gabatar zai tanadi takunkumi da matakan ladabtarwa ga jami’an Najeriya da ke aiwatar da ko goyon bayan dokokin batanci da Shari’a.
“Wannan matsaya da Amurka ta dauka tana da matukar muhimmanci wajen ladabtar da jami’an Najeriya da suka halitta yanayi mai cike da zalunci da keta hakkin dan Adam,” in ji Cruz.
Shirin sanatan na zuwa ne bayan da shugaban Amurka, Trump ya bayyana cewa Najeriya ta koma cikin jerin da ake zargin ana zaluntar Kiristoci.
Wane zargi Shugaba Trump ya yi?
Trump ya yi ikirarin cewa Kiristoci a Najeriya na fuskantar barazanar shudewa, yana zargin cewa “an kashe dubban Kiristoci ta hannun masu tsattsauran ra’ayi na Musulunci.”
Ya ce ya umarci wasu ’yan majalisa kamar Riley Moore (R-W.Va.) da Tom Cole (R-Okla.) su gudanar da bincike kan kashe-kashen da ake zargi, sannan su gabatar da rahoto.
“Amurka ba za ta tsaya gefe tana kallo ba yayin da irin wadannan mummunan abubuwa ke faruwa a Najeriya. Za mu tsaya tsayin daka wajen kare Kiristocin duniya," in ji Trump.

Source: Getty Images
Shin ana shari'ar musulunci a Najeriya?
A Najeriya, dokar Shari’a tana aiki ne a jihohi 12 na Arewa, inda yawancin jama’a Musulmai ne, kamar yadda Premium Times ta kawo.

Kara karanta wannan
Najeriya ta yi wa Trump martani mai zafi kan zargin kashe Kiristoci, ta ce karya ne
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun dade suna suka kan dokokin batanci, suna cewa ana amfani da su wajen kashe mutane ko hukunta su ta hanyar shari’ar addini.
Najeriya ta musanta ikirarin Trump
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta ce ikirarin Donald Trump na cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya ba gaskiya ba ne.
A wata sanarwa da ma'aikatar harkokin waje ta Najeriya ta fitar, ta ce yan Najeriya na rayuwa da juna cikin zaman lafiya ba tare da nuna banbancin addini ba.
Haka kuma ta bayyana cewa, a karkashin jagorancin shugaba Bola Tinubu, Najeriya ta jajirce wajen yaƙi da ta’addanci, ƙarfafa zumuncin addinai, da kare rayuka da haƙƙin dukkan ’yan ƙasa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
