Mintuna 30 a tsakani, Jirage Sama 2 na Rundunar Sojoji Sun Yi Hatsari, Sun Fada Teku
- Rundunar Sojojin Ruwa ta kasar Amurka ta tabbatar da cewa jiragenta biyu sun yi hatsari a tekun kudancin China ranar Lahadi
- Rahotanni sun nuna cewa mintuna 30 tsakanin hatsarin jirgin sojoji na farko da na biyu amma dai babu wanda ya rasa ransa
- Wannan lamari na zuwa ne yayin da shugaban Amurka, Donald Trump ya fara ziyara a yankin Asiya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Tekun Kudancin China – Jirage biyu na rundunar sojojin ruwa ta kasar Amurka sun yi hatsari a lokuta daban-daban a tekun da ke kudancin China ranar Lahadi da ta shige.
Rundunar Sojin Ruwa ta Amurka ta tabbatar da cewa jiragen saman biyu sun yi hatsari a lokuta daban-daban yayin gudanar da wasu ayyukan atisaye a yankin Tekun Kudancin China.

Source: Facebook
Jiragen Sojoji 2 sun yi hatsari a China

Kara karanta wannan
Dalilin Buhari da Tinubu na korar Janar 500 daga rundunar tsaro duk da matsalar ta'addanci
A cewar sanarwar Rundunar Pacific Fleet ta Amurka ta fitar, hatsarin farko ya shafi jirgin sama mai saukar ungulu kirar MH-60R Sea Hawk, in ji rahoton Reuters.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce jirgin ya gamu da hatsari ne yayin gudanar da atisayen da aka saba na yau da kullum.
Rahotanni sun bayyana cewa jami'an hukumomin ba da agajin gaggawa sun isa wurin cikin gaggawa kuma duk ma’aikatan jirgin uku an ceto su lafiya ba tare da asarar rai ba.
Bayan kusan mintuna 30 da hatsarin farko, wani jirgin yakin rundunar sojin ruwan Amurka kirar Boeing F/A-18F Super Hornet ya fado a cikin Tekun Kudancin China.
Rundunar ta ce jirgin ya rikito cikin ruwa ne yayin da yake aiwatar da atisayen da jami'ai suka saba yi na yau da kullum daga jirgin ruwan USS Nimitz.
Shin an rasa rayuka a hadurran jiragen 2?
Sojojin ruwa sun ce matukan jirgin biyu sun samu nasarar yin tsalle daga cikin su kafin ya kife, kuma an ceto su cikin kankanin lokaci.
Sanarwar rundunar sojojin ta tabbatar da cewa, “Dukkan jami’an da abin ya shafa suna cikin koshin lafiya kuma an kwantar da su a asibiti cikin yanayi mai kyau.”
Haka kuma, hukumomi sun fara gudanar da bincike domin gano ainihin musabbabin hadurran biyu, cewar rahoton CNN.

Source: Getty Images
Hatsarin ya faru ne a daidai lokacin da Shugaban Amurka Donald Trump ke ci gaba da ziyarar farko ta Asiya tun bayan fara wa’adin mulkinsa na biyu.
Bugu da kari, Babban Sakataren Tsaron Amurka Pete Hegseth na shirin fara ziyara a yankin Asiya, inda ake sa ran zai ziyarci kasashe da dama.
Jirgin Emirates ya fada teku a China
A wani rahoton, kun ji cewa jirgin sama na dakon kaya ya sauka daga kan titinsa, ya fada cikin tekun da ke bayan filin jirgi a birnin Hong Kong na kasar China.
Rahotanni sun bayyana cewa jirgin na kamfanin sufuri na Emirate ya bugi wata motar sintiri kafin daga bisani ya afka cikin teku, lamarin da ya zama ajalin mutane biyu da ke cikin motar.
Jami’an ceto sun isa wurin a kan lokaci kuma sun yi nasarar kubutar da matuka da ma'aikatan jirgin guda hudu cikin koshin lafiya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
