Zaben Kamaru: Matasa Sun Barke da Zanga Zanga, An Yi Arangama da 'Yan Sanda
- An kama aƙalla mutum 20 a Kamaru sakamakon zanga-zangar da ta biyo bayan zaben shugaban kasa na 12 ga Oktoba, 2025
- Ministan harkokin cikin gida, Paul Atanga Nji, ya ce za a gurfanar da wasu matasa a kotun soja bisa zargin tayar da fitina
- 'Yan jam'iyyun adawa a kasar sun yi zargin an buga magudin zabe, yayin da ake jiran sakamakon karshe daga hukumomi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kamaru – Hukumomin Kamaru sun tabbatar da kama mutum aƙalla 20 da ake zargi da hannu a zanga-zangar da ta biyo bayan zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 12 ga Oktoba, 2025
Ministan harkokin cikin gida, Paul Atanga Nji, ne ya bayyana haka a ranar Talata, inda ya ce za a gurfanar wasu daga cikin wadanda aka kama yayin arangama da 'yan sanda.

Source: Getty Images
Rahoton AP ya nuna cewa hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zaman dar-dar a kasar kafin bayyana sakamakon zaben da ake sa ran fitarwa a karshen wannan mako.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama masu zanga-zanga a Kamaru
A cikin wata sanarwa, Atanga Nji ya ce an kama masu tayar da hankali da dama a birnin Garoua, yayin da wasu kuma aka tura su birnin Yaounde domin ci gaba da bincike.
Rahoton Washinton Post ya nuna cewa ya ce:
“Gwamnati tana lura yadda wasu ke aikata munanan ayyuka da nufin tada rikici. Wadanda aka kama suna karkashin tafiyar wasu ‘yan siyasa.”
Sanarwar ta kara da cewa mutum 20 daga cikin wadanda aka kama za su fuskanci hukunci a kotun soja bisa zargin tayar da fitina da tada hankali a cikin al’umma.
'Yan adawa na zargin magudi a Kamaru
Dan takarar jam;uyyar adawa, Issa Tchiroma Bakary da ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben, ya yi kira ga shugaban kasa Paul Biya, mai shekaru 92, da ya amince da shan kaye.
Sai dai jam’iyya mai mulki ta karyata wannan ikirari, tana mai zargin Tchiroma da yunkurin dagula tsarin zabe.
Jam'iyyar mai ci a kamaru ta ce majalisar tsarin mulki ce ke da alhakin fitar da sakamakon karshe a ranar 26 ga Oktoba.
Masana siyasa sun ce ana sa ran Biya zai sake lashe zaben, kasancewar jam’iyyun adawa ba su da hadin kai.
Rahotanni kan kura-kurai a zaben Kamaru
Kungiyoyin farar hula da na addini da suka sa ido kan zaben sun bayyana cewa an samu kura-kurai da dama yayin kada kuri’a.
Kungiyar majami’u ta Kamaru ta ce an samu matsalolin kamar sauya wuraren zabe da kuma gazawar sabunta rajistar masu kada kuri’a, wanda har sunayen mamata ke ciki.
Kungiyoyi takwas na farar hula da suka sa ido kan zaben sun ce an samu rashin isassun takardun kuri’a a wasu rumfuna da kuma yunkurin cike akwati da kuri’u.

Source: Getty Images
Shugaba Paul Biya da ya karbi mulki tun 1982, ya kasance shugaban kasa na biyu tun bayan samun ‘yancin Kamaru daga hannun Faransa a 1960.
An yi kone-kone kan zabe a Kamaru
A wani rahoton, kun ji cewa an fara tayar da hankula a kamaru bayan kada kuri'a da jama'ar kasar suka yi.
Matasa sun fito kan tituna a wasu birane suna kone-kone domin nuna adawa da sakamakin da aka fara fitarwa.
Jam'iyyar shugaban kasa Paul Biya da ke mulki a Kamaru ta ce masu-zanga zangar sun kona mata ofis a wani yanki na kasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


