Isra'ila Ta Yi Biris da Trump, Ta Kashe Bayin Allah a Sabon Harin da Ta Kai Gaza
- Mutane 45 sun mutu a wasu sababbin hare-haren sama da Isra’ila ta kai a Zirin Gaza duk da yarjejeniyar tsagaita wuta
- Harin ya auku a yankuna da dama, inda asibitoci hudu suka tabbatar da mutuwar fararen hula, mata, yara da ‘yan jarida
- Isra’ila ta ce ta kai farmaki kan Hamas amma daga bisani ta sanar da dawowa bin yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Gaza - Akalla mutane 45 ne suka mutu sakamakon jerin hare-haren sama da sojojin Isra’ila suka kai a sassan Gaza a ranar Lahadi, 19 ga Oktoba, 2025.
Ma’aikatar agaji ta Gaza da asibitocin birnin ne suka tabbatar da hakan, wanda ke nufin kafi ga alkaluman farko na mutane 33 da aka bayyana a baya.

Source: Getty Images
Isra'ila ta kashe gomman mutane a Gaza
Rundunar sojojin Isra’ila ta tabbatar da cewa ta kai farmaki a wurare da dama da ta ce na kungiyar Hamas ne, kamar yadda rahoton France 24 ya nuna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yanzu haka dai Isra'ila da Hamas na zargin juna da karya yarjejeniyar tsagaita wuta wadda ta shiga rana ta tara tun bayan shiga tsakani da Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi.
Mai magana da yawun hukumar agaji ta Gaza, Mahmud Bassal, ya ce:
“Akalla mutane 45 ne suka mutu sakamakon hare-haren da Isra’ila ta kai a wurare daban-daban na Zirin Gaza.”
Asibitoci sun tabbatar da mutuwar mutane 45
Asibitoci guda hudu a Gaza — Al-Awda, Al-Aqsa, Nasser, da Al-Shifa — sun tabbatar da yawan mutanen da suka mutu da kuma wadanda suka jikkata.
Asibitin Al-Awda a Nuseirat ya ce mutane 24 ne suka mutu yayin da mutum 73 suka jikkata, yayin da Al-Aqsa ya karbi gawar mutane 12, asibitin Nasser ya tabbatar da mutane 5, asibitin sannan Al-Shifa ya tabbatar da mutane 4.
Jaridar The Guardian ta rahoto Bassal ya bayyana cewa hare-haren sun shafi fararen hula, ciki har da mata da yara, yana mai cewa:

Kara karanta wannan
Dakarun soji sun fafata da ƴan bindiga, an gano ƴan China da aka yi garkuwa da su
“Mutane shida sun mutu a garin Zuwaida, sannan wasu shida, ciki har da yara, sun mutu a kusa da Nuseirat.
"Wata mata da ‘ya’yanta biyu sun mutu bayan jirgin yaki marar matuki ya kai hari kan wani tanti da ke dauke da ‘yan gudun hijira a Arewacin Khan Yunis.”

Source: Getty Images
Harin Isra'ila ya hallaka dan jarida da wasu
Ya kara da cewa wani dan jarida da mutum daya sun mutu a harin da aka kai a yammacin garin Zuwaida, sannan mutane biyu sun mutu a yankin Al-Ahli Club na Nuseirat, da kuma wasu biyu a Jabalia da ke Arewacin Gaza.
“Harin da aka kai kan wani gini a Gaza City ya kashe mutum daya, yayin da wasu daga cikin wadanda suka jikkata daga baya suka rasu."
- Mahmud Bassal.
Masana na ganin cewa ci gaba da kai hare-hare da Isra'ila ke yi a Gaza zai iya lalata yarjejeniyar tsagaita wuta da Donald Trump ya yi kokarin assassawa tsakanin bangarorin biyu.
Isra'ila da Hamas sun fara musayar fursunoni
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Hamas ta saki ‘yan Isra’ila 20 da ta ke rike da su, yayin da Isra’ila ta saki Falasɗinu fiye da 1,900 a matsayin yarjejeniyar tsagaita wuta.
An yi farin ciki a Ramallah da Gaza yayin da motocin daukar mutane suka isa dauke da wadanda suka shaki 'yanci daga gidajen yarin Isra'ila.
Shugaban Amurka Donald Trump ya isa yankin don tattaunawa kan yarjejeniyar zaman lafiya, inda ya ce yakin ya riga ya gama karewa a halin yanzu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

