Jirgin Sama na Emirates Ya Gamu Tangarda Ya Fada cikin Teku, An Rasa Rayuka
- Jirgin sama na dakon kaya ya sauka daga kan titinsa, ya fada cikin tekun da ke bayan filin jirgi a birnin Hong Kong na kasar China
- An tattaro cewa jirgin ya bugi wata motar sintiri da ke aiki a filin, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar ma'aikata biyu
- Hukumomin China tare da kamfanin jiragen sama na Emirates sun fara gudanar da bincike don gano musabbabin hatsarin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Hong Kong, China - Wani jirgin sama na dakon kaya ya gamu da hatsari a filin jirgi na kasa da kasa da ke birnin Hong Kong na kasar China.
Rahotanni sun bayyana cewa hatsarin ya faru ne lokacin da wani jirgin dakon kaya na kamfanin Emirates, mai lamba EK9788, ya kauce daga hanya kuma ya fada cikin teku.

Source: Getty Images
Rahoton BBC News ya nuna cewa jirgin ya bugi wata motar sintiri kafin daga bisani ya afka cikin teku, lamarin da ya zama ajalin mutane biyu da ke cikin motar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutum 2 sun mutu a hatsarin jirgin sama
An gano cewa jirgin kirar Boeing 747, wanda ya taso daga Dubai, ya sauka daga hanya ne da misalin karfe 3:50 na safe agogon Hong Kong (7:50 na yamma agogon GMT) yayin da yake kokarin sauka a titinsa da ya jike saboda ruwan sama.
A kokarin tsayawa, jirgin ya buge motar sintiri da ke kusa da hanyar tashi kafin ya fada cikin ruwa da ke bayan filin.
Rahoton hukumomi ya bayyana cewa mutane biyu da ke cikin motar, wadanda dukkansu mambobi ne na ƙungiyar kula filin jirgi, sun mutu nan take sakamakon karfin bugun.
An ceto matukan jirgin sama a raye
Jami’an ceto sun isa wurin a kan lokaci kuma sun yi nasarar kubutar da matuka da ma'aikatan jirgin guda hudu, wadanda duk sun tsira da raunuka kadan.
Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Hong Kong ta kaddamar da bincike na musamman don gano musabbabin wannan hadari, cewar rahoton Leadership.
Rahotannin farko sun nuna cewa rashin kyaun yanayi, iska da matsalar injin jirgin na cikin abubuwan da suka jawo hatsarin.
Shugaban Filin Jirgin Saman Honh Kong, Mr. Raymond Chiu, ya bayyana lamarin a matsayin “daya daga cikin manyan haduran jiragen sama mafi muni da suka taba faruwa a Hong Kong cikin shekaru."
Mista Chiu ya yi jimami tare da mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu sakamakon wannan hatsari.

Source: Getty Images
Matakan da aka dauka bayan hatsarin
A sakamakon haka, an dakatar da zirga-zirga a titin jirgi mai lamba 07R/25L domin gudanar da bincike, wanda ya janyo jinkiri da karkatar da wasu jirage zuwa wasu filayen jirgi.
Kamfanin Emirates Airlines, a wata sanarwa da ya fitar daga bisani, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa ya hada kai da hukumomi wajen bincike.
Karamin jirgi ya yi hatsari a Jamus
A wani rahoton, kun ji cewa wani karamin jirgin sama ya gamu da hatsari a Yammacin kasar Jamus jim kadan bayan hukumomi sun sanarda bacewarsa.
Rundunar ‘yan sanda a Jamus ta tabbatar da mutuwar mutane biyu a hatsarin jirgin wanda ya auku a kusa da garin Bitburg.
An bayyana cewa hukumar binciken hadurran jiragen sama ta Jamus ta fara gudanar da bincike domin gano dalilin da ya sa jirgin ya fado.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


