Saudiyya Ta ba Ƴan Najeriya Damar Mallakar Gidaje a Makkah, kusa da Ɗakin Harami

Saudiyya Ta ba Ƴan Najeriya Damar Mallakar Gidaje a Makkah, kusa da Ɗakin Harami

  • Saudiyya ta kaddamar da aikin “King Salman Gate” don ba ‘yan Najeriya da kasashen duniya damar mallakar kadarori a Makkah
  • Za a yi wannan katafaren ginin ne a kusa da Masallacin Harami, inda zai kunshi gidaje, wurin ibada, kasuwannni da otal otal
  • Aikin KSG zai samar da ayyukan yi 300,000 nan da 2036, tare da tallafawa burin Saudiyya na Vision 2030 kan tattalin arziki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Saudiyya - Gwamnatin Saudiyya ta bude sabon shirin da zai bai wa ‘yan Najeriya da sauran ‘yan kasashen duniya damar mallakar kadarori a Makkah.

Wannan na zuwa ne bayan kaddamar da babban aikin “King Salman Gate”, wanda zai bunkasa zuba jari, ci gaban birni da inganta tattalin arzikin Makkah.

Saudiyya za ta gina gidaje, otal otal, kasuwanni da wurin bauta a shirin King Salman Gate, a Makkah.
Hoton yariman Saudiyya mai jiran gado, Shahzada Mohammed bin Salman bin Abdulaziz Al Saud. Hoto: @insharifain
Source: Twitter

Damar mallakar kadarori a Makkah

Wannan shiri ne na mai jiran gadon sarautar Saudiyya, Shahzada Mohammed bin Salman bin Abdulaziz Al Saud, kamar yadda jaridar Times of India ta rahoto.

Kara karanta wannan

Dangote ya ba 'yan Najeriya mafita kan hanyar samun ayyukan yi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya nuna cewa Yarima Shahzada shi ne Firayim Minista kuma shugaban kamfanin RUA Al Haram Al Makki, wani kamfani da ke karkashin asusun bunkasa jama'a na PIF.

Kamfanin RUA ne zai samar da kudaden da za a aiwatar da shirin King Salman Gate, wanda zai ba 'yan Najeriya da sauran kasashe damar mallakar kadarori a Makkah.

A cewar sanarwar fadar masarautar Saudiyya, aikin zai mamaye fili mai girman murabba’in mita miliyan 12 (12m sqm) a kusa da Masallacin Harami.

Tasirin aikin King Salman Gate a Makkah

Shirin KSG zai kasance cibiyar kasuwanci, masauki, ibada da al’adu, inda za a gina sabbin wuraren zama, otal-otal na zamani, shagunan kasuwanci, da wuraren cin abinci, inji rahoton Punch.

Wannan gagarumin shiri zai samar da wurin ibada mai daukar mutane 900,000 a ciki da wajen ginin, tare da hade shi da hanyoyin sufuri na zamani domin saukaka zirga-zirgar masu aikin Hajji da Umarah.

Kara karanta wannan

Dakarun soji sun fafata da ƴan bindiga, an gano ƴan China da aka yi garkuwa da su

A cewar kamfanin, King Salman Gate zai hada tsarin gine-ginen Makkah na gargajiya da salon zamani, domin bai wa matafiya da mazauna birnin damar jin zama a wajen.

Aikin zai kuma mayar da hankali kan gyara da adana wuraren tarihi da suka kai murabba’in mita 19,000, domin kare al’adun Makkah da tarihin addinin Musulunci.

An ce akalla mutane 300,000 ne za su samu ayyukan yi idan an kammala aikin King Salman Gate a Makkah
Hoton wani bangare na birnin Saudiyya. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Mutane 300,000 za su samu aiki a Makkah

A cewar sanarwar, shirin zai samar da ayyukan yi ga mutane sama da 300,000 nan da 2036, tare da habaka tattalin arzikin Saudiyya a karkashin burin Saudi Vision 2030.

Kamfanin RUA Al Haram Al Makki ya ce ya mayar da hankali kan ayyukan ci gaba masu dorewa, da inganta albarkatun kasa, da kuma kare yanayin al’adu da muhalli na Makkah.

Wannan dama, kamar yadda masana suka ce, ta bude kofa ga ‘yan Najeriya da sauran Musulmi su saka jari ko su mallaki kadarori kusa da Masallacin Harami — abin da zai kara darajar Makkah a matsayin cibiyar kasuwanci da ibada a duniya.

Saudiyya ta tsaurara sharuda ga aikin Hajji

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Saudiyya ta ja hankalin kasashen musulmi game da ka'idojin lafiya yayin da ake shirye-shiryen aikin Hajjin 2026.

Kara karanta wannan

'Babbar matsalar da Najeriya ke fuskanta yanzu,' Atiku ya ba Tinubu shawarwari

Ma'aikatar Lafiya ta Saudiyya ta fitar da ka'idoji da sharuddan lafiya da take bukatar kowane mahajjaci ya kiyaye tun kafin ya baro kasarsa.

Tuni dai Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta shawarci maniyyata su cika duka sharuddan da Saudiyya ta gindaya don gudun samu matsala.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com