Minista Ya Tafi Kasar Waje, Ya Je Duba Jiragen Yakin Sojojin Najeriya da Ake Kerawa

Minista Ya Tafi Kasar Waje, Ya Je Duba Jiragen Yakin Sojojin Najeriya da Ake Kerawa

  • Ministan tsaro, Mohammed Badaru, ya ziyarci masana’antun Italiya, inda ake kera jiragen yakin sojojin saman Najeriya
  • Akwai jiragen AW109 Trekker guda 10 da jiragen M-346 Fighter Jets guda 24 da ake haɗawa don ƙarfafa rundunar sojin
  • Wannan mataki na cikin shirin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na inganta tsaron ƙasa da sabunta kayan aikin soja

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Italiya - Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya kai ziyara zuwa masana’antun da ake kera jiragen sojojojin Najeriya da ke a Leonardo S.p.A., Arewacin Italiya.

An rahoto cewa a wadannan masana'antu ne ake ci gaba da kera sababbin jiragen yaƙi da masu saukar ungulu na rundunar sojojin saman Najeriya (NAF).

Ministan tsaro, Mohammed Badaru ya ziyarci Italiya, inda ake kera jiragen yakin sojojin Najeriya
Ministan tsaro, Mohammed Badaru na sanya hannu kan daya daga cikin jiragen yakin Najeriya da aka kera a Italiya. Hoto: fmino.gov.ng
Source: UGC

Minista ya ziyarci wurin kera jiragen soji

Badaru ya ziyarci sashen kera jirgi mai saukar ungulu da ke Vergiate da sashen kera jiragen yaki a Venegono, kamar yadda rahoton shafin ma'aikatar yada labarai ya nuna.

Kara karanta wannan

An yi yunkurin juyin mulki har Tinubu ya soke bikin ranar 'yanci? An samu bayanai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar da Mati Ali, mai magana da yawun ministan ya fitar, wadannan masana'antu ne ake haɗa muhimman jiragen da Najeriya ta siya domin ƙarfafa rundunar sojin sama.

Ziyarar ta biyo bayan kasancewar Badaru cikin tawagar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta halarci taron AQABA Process a Jordan.

Sanarwar da aka fitar a ranar Asabar a Abuja, ta bayyana cewa ziyarar ta zama wata muhimmiyar nasara ga shirin sabunta kayan aikin tsaron ƙasar Najeriya.

Jiragen yaki sun kusa isowa Najeriya

Mati Ali ya bayyana cewa ministan ya duba aikin kera jiragen AW109 Trekker guda 10, inda aka riga aka kammala kera guda uku, kuma suna shirin isowa Najeriya.

Ana sa ran za a kammala kera wasu guda uku kafin ƙarshen shekarar 2025, yayin da guda hudu na ƙarshe za su iso Najeriya cikin farkon 2026.

Haka kuma, Ministan ya duba aikin jiragen M-346 Fighter Attack Jets guda shida, inda yanzu ake ake gwajin tashi kan guda uku yayin da sauran ke cikin matakin ƙarshe na haɗawa.

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu: Amurka ta fitar da gargadi bayan saka ranar zanga zanga a Najeriya

Gaba ɗaya, jirage 24 ne za a kawo Najeriya cikin rukuni hudu, kowanne rukuni zai kunshi jirage shida, tare da makamai, kayan gyara, kayan horo, da kayan aiki na musamman.

Rundunar sojin saman Najeriya ta sayo jiragen yaki daga Italiya.
Wani jirgin yaki da gwamnati ta saya wa sojojin saman Najeriya. Hoto: @DHQNigeria
Source: Facebook

Gwamnatin Tinubu na ƙarfafa tsaro

Badaru ya nuna jin daɗinsa da yadda kamfanin Leonardo ke aiwatar da aikin da inganci da kwarewa, yana mai yabawa da ƙwazon injiniyoyin da ke aikin, inji rahoton Punch.

Ya ce wannan ziyarar ta sake tabbatar da ƙudurin gwamnatin Tinubu na ƙarfafa rundunar tsaro da kuma sabunta kayan aikin zamani domin tabbatar da zaman lafiya.

Ministan ya ƙara da cewa gwamnati na aiki tuƙuru wajen gina dangantaka mai ƙarfi da ƙasashen duniya, musamman a fannin fasahar tsaro da horo.

Najeriya ta sayo jiragen yaki daga Faransa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar sojin saman Najeriya ta sanar da cewa gwamnati ta sayo jiragen yaki kirar Alpha Jets guda 12 daga kasar Faransa.

Hassan Abubakar, mai magana da yawun rundunar tsaro ya bayyana cewa rundunar sojin sama za ta karbi jiragen yaki kirar M-346FA, T-129 da kuma masu saukar angulu.

Rahoto ya nuna cewa jiragen Alpha Jets na da tasiri ga ayyukan sojin saman Najeriya, wajen daukar makamai da kai harin kusa ga 'yan ta'adda.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com