‘Ban Tsammanin Zan Shiga Aljanna’: Donald Trump Ya Magantu kan Sulhu a Gaza
- Shugaban Amurka Donald Trump ya yi magana game da rawar da yake takawa wurin tabbatar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.
- Shugaba Trump da kansa ya ce “bai da tabbacin shiga Aljanna”, duk da irin rawar da ya taka wajen kawo ƙarshen yaƙin Isra’ila da Hamas
- Trump ya bayyana cewa ya kawo ƙarshen yaƙin Gaza da ya daɗe yana addabar yankin, inda aka samu fursunoni daga ɓangarori biyu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US — Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi karin haske kan yadda yake kallon makomarsa bayan barin wannan duniya da ake ciki.
Shugaba Trump ya ce ba shi da tabbacin zai shiga Aljanna, duk da irin kokarinsa wajen kawo zaman lafiya a duniya.

Source: Getty Images
Rawar da Trump ya taka a rikicin Gaza
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton CNN ya ce Trump ya samu da yabo daga ƙasashe da dama bayan rawar da ya taka wajen kawo ƙarshen yaƙin shekaru tsakanin Isra’ila da Hamas a zirin Gaza.
Yaƙin da ya hallaka dubban mutane yanzu ya lafa, kuma aka saki fursunoni daga ɓangarorin biyu, abin da ya kawo sake haɗuwar iyalai da dama da aka raba.
Trump, wanda ya sha alwashin kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe a duniya tun lokacin da yake neman shugabanci, ya taba cewa idan ya kawo zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine, hakan zai iya saka shi a cikin Aljanna.
“Ina so in shiga Aljanna idan zai yiwu."
“Na ji cewa abubuwa ba sa tafiya min daidai a can. Amma idan na iya shiga, wannan zai kasance ɗaya daga cikin dalilai, ƙoƙarina na kawo zaman lafiya tsakanin Ukraine da Rasha.”
- Donald Trump

Source: Twitter
Trump na kokwanton shiga aljanna a rayuwarsa
Sai dai a ranar Litinin, yayin da yake cikin jirgin sojojin sama zuwa Isra’ila domin kaddamar da sakin fursunonin farko, Trump ya yi barkwanci cewa bai da tabbacin cewa zai shiga Aljanna.

Kara karanta wannan
Atiku da fitattun 'yan Najeriya, kungiyoyi da jam'iyyu da suka yi adawa da afuwar Tinubu
Trump ya kuma sake jaddada cewa da ba a tafka magudi a zaben 2020 ba, da ya hana Rasha kai wa Ukraine hari.
Ya kara da cewa:
“Ina wasa ne kadan, amma gaskiya ba na ganin akwai wani abu da zai sa in shiga Aljanna. Wataƙila yanzu haka ina cikin Aljanna ne a cikin wannan jirgi. Ba ni da tabbacin zan iya shiga, amma na taimaka wa mutane da yawa su rayu cikin farin ciki.
A baya-bayan nan, Trump da Shugaban Rasha, Vladimir Putin sun gana a Alaska, ganawa ta farko tun bayan taron su na Helsinki a 2018, domin tattauna rikicin Ukraine.
Sai dai duk da tsananin fata da ake yi, tattaunawar ta kare ba tare da cimma matsaya ba, abin da ya rage wa jama’a fatan ganin karshen wannan rikici, cewar rahoton USA Today.
Trump ya je asibiti duba lafiyarsa
A wani labarin, Shugaba Donald Trump zai sake yin gwajin lafiya karo na biyu a cikin shekara guda, abin da ya jawo maganganu daga jama’a.
Majiyoyi sun bayyana cewa Donald Trump, mai shekara 79, zai yi gwajin ne a asibitin sojoji na Walter Reed da ke kasar Amurka.
Fadar White House ba ta bayyana dalilin sake gwajin lafiyar ba, duk da cewa an riga an duba shi da farko a watan Afrilun 2025.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

