'Yaki Ya Kare,' An Saki Falasdinawa yayin da Hamas Ta saki Mutanen Isra'ila

'Yaki Ya Kare,' An Saki Falasdinawa yayin da Hamas Ta saki Mutanen Isra'ila

  • Kungiyar Hamas ta saki ‘yan Isra’ila 20 da ta ke rike da su, yayin da Isra’ila ta saki Falasɗinu fiye da 1,900 a matsayin yarjejeniyar tsagaita wuta
  • An yi farin ciki a Ramallah da Gaza yayin da motocin daukar mutane suka isa dauke da wadanda suka shaki 'yanci daga gidajen yarin Isra'ila
  • Shugaban Amurka Donald Trump ya isa yankin don tattaunawa kan yarjejeniyar zaman lafiya, inda ya ce yakin ya riga ya gama karewa a halin yanzu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Gaza – Bayan shekaru biyu na rikici mai muni, Hamas ta saki dukkan ‘yan Isra’ila 20 da suke raye a hannunta.

A daya bangaren, Isra’ila ta fara sakin daruruwan Falasɗinawa a wani mataki na tsagaita wuta a Gaza.

Wasu mutanen Gaza da suka dawo gida
'Yan uwa sun karbi wasu daga cikin mutanen Gaza da Isra'ila ta sake. Hoto: @SuppressedNws1
Source: Twitter

Rahoton Al-Jazeera ya nuna cewa lamarin ya kawo farin ciki a Gaza da Isra'ila yayin da ake fatan zai kawo karshen rikicin da ya yi sanadin mutuwar dubban fararen hula a yankin.

Kara karanta wannan

'Ban adawa da Falasɗinu': Ɗan majalisar tarayya bayan ganawa da jakadan Isra'ila

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutanen Isra'ila da Hamas ta sake

Rahotanni sun bayyana cewa wadanda aka sako daga bangaren Isra’ila duk maza ne, kuma sun isa gida inda za su gana da iyalansu tare da fuskantar binciken lafiya.

Haka kuma, an bayyana cewa za a mika gawar wadanda suka mutu su 28 saboda yarjejeniyar da aka kulla a Masar.

A lokaci guda, Isra’ila ta fara sakin Falasdinawan da ta rufe daga gidajen yarin Ofer da ke yankin Yammacin Kogin Urdun, inda akalla mutane 1,900 suka riga suka samu ‘yanci.

Ana farin ciki a Ramallah da Gaza

Motocin da ke dauke da wadanda aka sake sun isa birnin Ramallah, inda jama’a suka fito da murna, cike da farin ciki.

Rahoton CTV ya nuna cewa wata motar kuma ta shiga Gaza, inda jami’an Hamas suka tabbatar da karbar wadanda aka sake.

Yarjejeniyar ta kuma ba da damar shigo da taimakon jin kai a yankin Gaza, wanda ke fama da yunwa da rushewar gine-gine sakamakon yaƙin da ya shafe shekaru biyu.

Kara karanta wannan

Shehi ya nemi zama da Kiristoci kan zuwan Isra'ila Najeriya da barazanar yaki

Hamas ta saki yan Isra'ila
Motoci dauke da 'yan Isra'ila da Hamas ta sake a Gaza. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ziyarar Trump da fatan zaman lafiya

Shugaban Amurka Donald Trump ya isa Isra’ila a ranar Litinin domin ganawa da shugabannin yankin da kuma wasu daga cikin mutanen da aka sake bayan tsayar da yakin.

A cikin wani jawabi, ya ce “yaƙin ya ƙare,” kodayake akwai kalubale kan makomar Hamas da tsaron Gaza.

Donald Trump zai kuma ziyarci kasar Masar domin tattaunawa da shugabannin yankin kan shirin gina zaman lafiya mai dorewa da tabbatar da tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya.

Mutanen Gaza sun koma gidajensu

A wani rahoton, kun ji cewa mutanen Gaza sun fara koma wa gidajen su da suka bari sakamakon hare haren Isra'ila.

Daruruwan Falasdinawa ne suka koma gidajensu bayan shirin tsgaita wuta da aka fara a kasar Masar.

Shugaban Amurka, Donald Trump ne ya sanar da tsagaita wuta bayan zaman da aka yi a Masar tsakanin Hamas da Isra'ila.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng