An Yi Babban Rashi: Fitacciyar Jarumar Fim da Ta Lashe Kyautar Oscar Ta Mutu

An Yi Babban Rashi: Fitacciyar Jarumar Fim da Ta Lashe Kyautar Oscar Ta Mutu

  • Fitacciyar jarumar Hollywood, Diane Keaton, wacce ta yi suna a cikin fina-finai kamar “Annie Hall” da “The Godfather,” ta rasu
  • Ta lashe lambar yabo ta Oscar, tare da samun nasarori da dama, inda ta zamo ɗaya daga cikin jarumai mata mafi tasiri a Hollywood
  • Keaton ta kasance mai fasaha da salo na musamman, kuma ta ce ba ta yi nadamar kai wa shekaru 79 ba tare da yin aure ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Rahotanni sun tabbatar da cewa fitacciyar jarumar fina-finai ta Amurka, Diane Keaton, ta mutu tana da shekaru 79 a duniya.

Jaruma Diane Keaton, wacce ta shahara saboda rawar da ta taka a cikin fina finan “Annie Hall” da “The Godfather,” ta mutu a makon nan.

Fitacciyar jarumar Hollywood, Diane Keaton ta mutu tana da shekaru 79
Jarumar fina-finan Amurka Diane Keaton ta isa wurin taron ba da kyaututtuka na LACMA Art+Film a Los Angeles a ranar 6 ga Nuwamba, 2021. Hoto: Michael Tran / AFP
Source: Getty Images

Jarumar fina-finan Amurka, Keaton ta mutu

Kara karanta wannan

Maryam Sanda da wasu sanannun mutane 5 da suka shiga cikin wadanda Tinubu ya yi wa afuwa

Jaridar The New York Times ta rahoto cewa jarumar ta mutu ne a jihar California, inda iyalanta suka roƙi a bar su su yi jimami cikin sirri yayin da ake jiran bayanai kan rasuwarta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Diane Keaton ta zama ɗaya daga cikin fitattun jarumai mata a tarihin Hollywood, saboda yadda take haɗa barkwanci da kamala a cikin fina-finai.

Dori Rath, wadda ta shirya mafi yawan fina-finan Ms Keaton ne ya sanar da rasuwar jarumar. Sai dai ba ta bayyana yaushe ko a ina Ms. Keaton ta mutu ba.

Diane Keaton, ta kasance 'yar wasan kwaikwayo da jama'a ke son kallonta, kuma ta fito a fina-finai sama da 100, kuma ta na taka rawa a kowane irin matsayi da aka ba ta.

Lambobin yabo da tasirin jarumar a fina-finai

Keaton ta lashe lambar yabo ta Oscar saboda kyakkyawar rawar da ta taka a cikin shirin “Annie Hall” (1977), wanda ya lashe kyaututtuka hudu, ciki har da 'mafi kyawun hoto' da 'mafi kyawun 'yar wasa.'

Ta kuma yi aiki tare da darakta Woody Allen a fina-finai takwas, daga “Play It Again, Sam” (1972) zuwa “Manhattan Murder Mystery” (1993).

Kara karanta wannan

Ana batun zargin kisan Kiristoci, yan bindiga sun yi ta'asa a masallacin Katsina

Duk da rikicin da ya taso a 2017 kan zarge-zargen lalata da ake yi wa Allen, Keaton ta tsaya tsayin daka a kansa, tana mai cewa ta yarda da shi.

Baya ga Oscar, Keaton ta lashe BAFTA da Golden Globe, tare da karin zabarta sau uku saboda fina-finanta kamar “Reds,” “Marvin’s Room,” da “Something’s Gotta Give.”

Ta kuma fito a matsayin Kay Adams, matar Michael Corleone (Al Pacino) a cikin shirin fim din “The Godfather,” inji rahoton Channels TV.

Fitacciyar jarumar Hollywood, Diane Keaton ta mutu tana da shekaru 79
Diane Keaton ta na magana bayan lashe kyautar Oscar, wanda aka gudanar a Los Angeles a ranar 3 ga Afrilu, 1978. Hoto: Bettmann / Contributor
Source: Getty Images

Rayuwa, soyayya da shekarun jarumar na ƙarshe

A ƙarshe, Keaton ta fito a fina-finai kamar “Book Club” (2018) da “Poms” (2019), waɗanda suka nuna yadda soyayya da nishaɗi ke ci tasiri har a lokacin tsufa.

A wata hira da ta yi a 2019, ta bayyana cewa, “Rayuwa tana da sauƙi idan ka tsufa, saboda babu abin da za ka rasa a lokacin.”

Duk da soyayyar da ta sha da fitattun jarumai kamar Woody Allen, Al Pacino, da Warren Beatty, jaruma Keaton bata taɓa yin aure ba.

Ta taba cewa, “Ban taɓa yin aure ba, amma hakan bai dame ni sosai ba. Kowa ba zai iya samun komai a rayuwa ba.”

Kara karanta wannan

Durkusa wa wada: Gwamnatin Tinubu ta roki ASUU, ta dauki sabon alkawarin hana yajin aiki

Rahama Sadau ta je masa'antar Hollywood

A wani labarinmu na baya, mun ruwaito cewa, jaruma Rahama Sadau ta kai ziyara Hollywood bayan ta samu takardar gayyata daga mawakin Amurka Akon da kuma darakta Jeta Amata.

Rahama Sadau ta amsa gayyatar zuwa Hollywood ne jim kadan bayan da aka kore ta daga Kannywood saboda ta yi bidiyon waka da Classiq.

An ce Rahama Sadau ta samu rakiyar Jeta Amata wanda ya karbi lambar yabo na shirya fina-finan Najeria wanda ke zaune a kasar Amurka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com