Rahama Sadau zata je Hollywood
- An kori fitacciyyar jarumar Kannywood Rahama Sadau daga Kannywood saboda ta rungumi wani mawaki a cikin wani bidiyo
- An yanzu ta bayyana cewa zata kai ziyara Hollywood bayan ta samu wani takardan gayyata daga jarimin Amurka Akon da kuma daraktan Najeriya Jeta Amata

Rahama Sadau ta kasance fitacciyar jarumar Kannywood wacce aka kora daga Kannywood saboda ta fito a kasetin wakar da ClassiQ yayi inda ta rungume shi. Labarin ya samu cece-kuce ya kuma ja hankalin mutane da dama.
Tun daga lokacin ake ta ta’anzartar da jarumar kamar yadda ta fito a wani sashi na wasan talbijin din Nollywood mai suna Sons of the Caliphate wanda gidan talbijin din Mo Abudu EbonyLife ya shirya.
KU KARANTA KUMA: Saraki ya goyi bayan hirar Aisha Buhari
A yanzu jarumar da samu albishir din da suka fi wannan dadi kamar yadda zata kai ziyara Hollywood nan bada jimawa ba. Ta rubata labarin mai dadi a shafinta na tweeter a ranar 15 ga watan Oktoba.
Muna da tabbacin cewa ziyarar nata zai yi sanadi ga abubuwa masu inganci. Zata samu rakiyar Jeta Amata wanda ya karbi lambar yabo na shirya fina-finan Najeria wanda ke zaune a kasar Amurka.
Zata kasance tare de babban mawakin kasar Amurka, Akon wanda baya bukatar a sanar ko wanene shi. Ya kasance mawaki mai nasarori yana kuma amfani da fasaharsa a wasan Hollywood kamar irinsu Black November.
Muna nan muna sauraron jin cikakken labara kan yadda abubuwea ke tafiya daga kyayyawar jarumar.

Asali: Legit.ng