Garin Dadi na Nesa: Jerin Kasashe 5 da Ake Bai Wa Samari Kudi domin Su Yi Aure
A wannan zamani da soyayya da aure ke ƙara tsada, wasu ƙasashe guda biyar sun ɗauki sabuwar hanya domin taimakawa samari su shiga daga ciki.
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kasashen suna biyan kuɗi ga mutane domin su yi aure. Wannan mataki yana nufin ƙarfafa soyayya da gina iyali ta hanyar tallafin kuɗi kai tsaye.

Source: Getty Images
Vanguard ta ruwaito cewa daga Asiya zuwa Turai, raguwar yawan haihuwa da tsufan mutane sun tilasta wa waɗannan ƙasashe ɗaukar matakin gaggawa domin farfaɗo da tsarin iyali.
Jerin kasashe 5 da ake ba da tallafin aure
Ga ƙasashe biyar da ke bayar da tallafin kuɗi ko taimako ga waɗanda suka yi aure:
1. Koriya ta Kudu
Koriya ta Kudu na fama da matsalar ƙarancin haihuwa, wanda ya zama babban abin damuwa ga ƙasar.
Sakamakon haka, wasu hukumomin yankuna sun ƙaddamar da shirye-shiryen biyan kuɗi, tallafin tafiye-tafiye, da kuma tallafin kama gidan haya ga sababbin ma’aurata.

Kara karanta wannan
Maryam Sanda da wasu sanannun mutane 5 da suka shiga cikin wadanda Tinubu ya yi wa afuwa
Akwai buƙatar duk wanda zai cike neman wannan tallafi ya kasance ƙasa da wasu adadin shekaru kuma ya kasance mazaunin yankin na tsawon wasu shekaru.
Manufar wannan tallafi da ake bayarwa a Koriya ta Kudu ita ce sauƙaƙa rayuwar aure da kuma ƙarfafa matasa su gina iyali.
2. Japan
Raguwar yawan jama’a a Japan ta kai matakin da ba a taba gani ba a tarihi, hakan ya sa wasu birane suke bayar da kudin biyan haya, canza wuri, da kuɗin kashe wa na yau da kullum ga sababbin ma’aurata.
A wasu garuruwa a Japan, ana bai wa matasa tallafin kudi domin su koma zama a yankin kuma su yi aure.
Duk da cewa ba ko'ina ake samun wannan garabasa ba, amma ya nuna yadda Japan ke ɗaukar batun farfaɗo da tsarin iyali da muhimmanci.
3. Hungary
Hungary ta shahara da shirin ta mai suna “Family Protection Action Plan” wato Shirin Kariya Ga Iyali.
A ƙarƙashin wannan shiri, sababbin ma’aurata na iya samun rancen kuɗi ba tare da riba ba har kimanin Dala $28,000 (sama da Naira miliyan 40).
Idan ma’auratan suka haifi yara a tsakankanin wani wa'adi da aka kayyade, ana iya yafe musu wani ɓangare na bashin.
Wannan ya sa Hungary ta zama ɗaya daga cikin ƙasashen Turai da ke bayar da mafi girman tallafi ga auren matasa da ƙara haihuwa.
4. China
Sakamakon yawaitar tuzurai da rashin daidaiton jinsi, wasu yankuna a China sun fara biyan kuɗi ga waɗanda suka yi aure da wuri.
A wasu yankunan kasar China, ana bada ƙarin kuɗi ga sababbin ma’aurata, musamman idan amarya ba ta kai wani adadi na shekaru ba.
Haka kuma, masu haɗa ma’aurata na iya samun lada daga hukumomi idan suka taimaka wajen kulla aure, in ji rahoton Bussiness Day.
5. Iran
Jamhuriyar musulunci ta Iran ma ta ɗauki matakin bayar da tallafin kuɗi domin rage gwauraye a kasar.
Ta hanyar shirye-shiryen gwamnati, ma’aurata na iya neman rancen aure ba tare da riba ba, samun filaye, da sauran tallafin kayan more rayuwa.

Source: Getty Images
Ko da yake tattalin arziki ya kawo cikas ga shirin, har yanzu Iran na ci gaba da ƙoƙarin ƙarfafa aure da tabbatar da zaman lafiya a cikin iyalai.
An sa dokar gwajin aure a Kebbi
A wani labarin, kun ji cewa Majalisar dokokin Kebbi ta amince da dokar gwajin lafiya kafin aure, 2025, wacce za ta kawo sauyi a tsarin daura aure a fadin jihar.
A karkashin wannan doka, duk masoyan da ke shirin yin aure dole ne.su yi wasu muhimman gwaje-gwaje, ciki har da gwajin jini da nau’in kwayoyin halitta da na cututtuka.
Dokar ta tanadi cewa za a yi wadannan gwaje-gwaje ne a cibiyoyin lafiya da gwamnati ta amince da su, watanni uku da makonni biyu kafin daura aure.
Asali: Legit.ng

