Ran Masoyin Buhari Ya Ɓaci, Ya Dura kan Masarautar Daura saboda Naɗa Rarara Sarkin Waka

Ran Masoyin Buhari Ya Ɓaci, Ya Dura kan Masarautar Daura saboda Naɗa Rarara Sarkin Waka

  • Wani ɗan gani kashe nin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Abdullahi Haruna Izge, ya yi kakkausar suka ga masarautar Daura
  • Ya bayyana cewa masarautar ba ta karrama ko mutunta marigayi tsohon Shugaban ba, duk da yadda ya riki Sarkin Daura kamar uba
  • Abdullahi Izge ya bayyana cewa kowa ya san yadda mawaki Dauda Kahutu Rarara ya muzanta Buhari, kuma ko ta'aziyyar rasuwarsa bai yi ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina – Abdullahi Haruna Izge, masoyin tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana mamaki da fushi a kan yadda masarautar Daura ta nada Rarara sarauta.

Kwanaki kamar hudu da su ka wuce ne Sarkin Daura, Mai Martaba Umar Faruk ya nada mawaki Dauda Kahutu Rarara a matsayin Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa.

Kara karanta wannan

"Sai an je gaban kotu," Fadar shugaban kasa ta kara tabo batun takarar Jonathan a 2027

Masoya Buhari sun fusata
H-D: Marigayi Buhari tare da Sarkin Daura, Mai Martaba Umar Faruka na mika wa Rarara takardar nadin sarauta Hoto: Abdullahi Haruna Izge/Dauda Kahutu Rarara
Source: Facebook

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, mai taken 'Mu masoya Buhari, mun ji an ci amanarmu,' Izge ya ce wannan mataki na masarautar cin amana ne ga magoya bayan Buhari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masarautar Daura ta fusata masoya Buhari

A cikin sakon wanda da alama ya rubuta shi a fusace, Abdullahi Haruna Izge ya ce bai dace masarautar Daura ta dauki irin wannan mataki babu duba da yadda Rarara bai mutunta Buhari.

Yace:

"Mu a matsayina na masoya Buhari, mun ji an ci amana ƙwarai bayan masarautar Daura ta ba wa Rarara sarauta, a masarautar da tsohon Shugaba Buhari ya dauka da kima da daraja, kuma ya ke karbar shawarwari.”

Izge ya ce tsohon Shugaba Buhari ya ji hulɗa da Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq, kuma ya dauke shi tamkar uba kuma abokin shawara.

Izge ya soki masarautar Daura

Izge ya ce abin da ya ba su mamaki shi ne yadda masarautar Daura ta iya kawar da kai daga yadda ta ke da Buhari, ta kuma yi nadin sarauta ga mutumin da ya zage shi a bainar jama'a.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Hadimin Gwamna Bago ya yi bankwana da duniya

Abdullahi Haruna Izge ya ce:

“Mun san halin Rarara na cin amana tun da farko, ya yi haka ga duk wanda ya taɓa taimaka masa kafin Buhari. Amma abin mamaki shi ya samu sarauta daga masarautar da ake girmamawa."
Izge ya ce masarautar Daura ba ta kyauta masu ba
Hoton Mai Martaba Umar Faruk yana gaisawa da Marigayi Shugaba Buhari Hoto: Abdullahi Haruna Izge
Source: Facebook

Ya ƙara da cewa:

“Bayan rasuwar Buhari ma, Rarara bai taɓa neman yafiya ba, ko ziyartar makabarsa, ko kuma yin gaisuwa ga iyalansa ba. Wannan raini ne, kuma ya sa nadin da aka yi masa ya yi wa mu masu kaunar Buhari zafi.”

Izge ya yi tambaya kai tsaye ga Sarkin Daura:

“Ya mai martaba, ta yaya za a ba wa Rarara sarauta duk da irin rainin da ya yi wa wanda ya ɗauke ka tamkar uba da aboki?”

Ya jaddada cewa darajar da Daura ta samu a idon duniya ta samo asali daga mutuncin Buhari, yana mai cewa da ba Buhari ba, Daura ba za ta samu irin wannan martaba ba.

An soki Rarara kan ta'aziyyar Buhari

Kara karanta wannan

"Za ku iya rasa kimarku": Tinubu ya aika da gagarumin saƙo ga Majalisar Ɗinkin Duniya

A wani labarin, mun wallafa cewa jama'a sun dura a kan mawaki, Dauda Kahutu Rarara a kan yadda ya ki ya fito kai tsaye domin ta'aziyyar tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari.

Rarara ya saka wani bidiyo inda ya ce “Allah ya jiƙan maza, Allah ya sa mutuwa hutuce.” Sai dai bai ambaci sunan tsohon Shugaba Buhari kai tsaye a cikin wannan saƙo ba.

Masoyan Buhari sun soki Rarara da cewa babu ya kamata a cikin abin da ya aikata, musamman ganin yadda tsohon Shugaban kasan ya goyi bayansa a baya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng