Yaki Zai Kare: Donald Trump Ya Sanar da Shirin Tsagaita Wuta a Gaza
- Akwai alamun yakin da kasar Isra'ila take yi da kungiyar Hamas a zirin Gaza ya kusa zuwa karshe
- Shugaban kasan Amurka, Donald Trump, ya sanar da shirin tsagaita wuta tsakanin bangarorin guda biyu
- Trump ya yi gargadin cewa idan Hamas ta ki amincewa da yarjejeniyar, zai goyi bayan Isra'ila ta kammala yakin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Amurka - Shugaban kasan Amurka, Donald Trump, ya bayyana shirin kawo karshen yaƙin Isra’ila a Gaza.
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya nuna cikakken goyon bayansa ga shirin kawo karshen yakin.

Source: Getty Images
Tashar TRT ta kawo rahoton cewa Trump ya sanar da shirin ne yayin wani taro da Benjamin Netanyahu a ranar Litinin, 29 ga watan Satumban 2025.
Trump da Netanyahu sun ja kunnen Hamas
Trump ya ce idan Hamas ta ki rattaba hannu kan yarjejeniyar, Isra'ila za ta samu cikakken goyon bayan Amurka wajen ci gaba da yakin har sai an kawar da kungiyar.

Kara karanta wannan
"Sai an je gaban kotu," Fadar shugaban kasa ta kara tabo batun takarar Jonathan a 2027
Yarjejeniyar dai za ta wajabtawa kungiyar Hamas ta ajiye makamai kuma ta daina taka rawa a cikin Gaza
“Idan Hamas ta ki yarjejeniyar, Bibi (Netanyahu), kuna da cikakken goyon bayanmu ku yi abin da ya kamata ku yi.”
Benjamin Netanyahu ya ce ya na tare da shirin Trump na kawo ƙarshen yaƙin a Gaza.
"Idan wannan kungiya ta kasa da kasa ta yi nasara, za mu daina yakin gaba ɗaya."
"Amma idan Hamas ta ki ko kuma ta ɓata yarjejeniyar, Isra’ila za ta kammala aikin da kanta. Wannan abu ne da za a iya yi cikin sauki ko cikin wahala. Amma za a yi shi."
- Benjamin Netanyahu
Me shirin tsagaita wutar ya kunsa?
Shirin ya tanadi cewa za a sako dukkan mutanen Isra’ila da ke hannun Hamas cikin awa 72, rahoton Time Magazine ya tabbatar.
Haka kuma, shirin ya tanadi kafa wata hukuma karkashin jagorancin Trump, wadda za ta ci gaba da kula da harkokin mulki bayan kammala yakin.
Bayan haka, Isra’ila za ta saki fursunonin Falasɗinu 250 wadanda aka yankewa hukuncin rai da rai a kurkuku da kuma wasu mutane 1,700 da aka tsare bayan harin Hamas a Isra’ila a ranar 7 ga Oktoba, 2023.
Haka kuma, Isra’ila za ta dawo da jigilar shigar da taimakon jin kai tare da fara gyaran ruwa, lantarki da tsarin magudanun ruwa a Gaza.

Source: Twitter
A karkashin yarjejeniyar, dole ne Hamas ta amince da rashin shiga cikin mulkin Gaza. Wadanda suka amince da sharuddan kuma suka yanke shawarar barin Gaza, za a ba su damar barin yankin ba tare da tsangwama ba.
Rundunar sojojin Isra’ila za ta fara janyewa daga sassan Gaza a hankali, amma za ta ci gaba da zama a wasu shingen tsaro na dindindin a kan iyakoki uku.
Haka kuma, Amurka za ta kafa tattaunawa tsakanin Isra’ilawa da Falasɗinu don cimma zaman lafiya da ci gaba.
Hakazalika, shirin ya yi tanadin cewa dole ne kungiyar Hamas ta ajiye makamanta.
Birtaniya ta amince da kasar Falasdinu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Birtaniya ta amince da kasar Falasdinu mai cikakken 'yanci.
Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya bayyana sanar da amincewar ne a ranar Lahadi, 21 ga watan Satumban 2025.
Keir Steirmer ya ce Birtaniya ta dauki matakin ne don dawo da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
