Kasashe Sun Fusata, An Kunyata Firaministan Isra'ila a Taron Majalisar Dinkin Duniya

Kasashe Sun Fusata, An Kunyata Firaministan Isra'ila a Taron Majalisar Dinkin Duniya

  • Wakilan kasashen duniya sun watse daga dakin taron Majalisar Dinkin Duniya lokacin da Firaministan Isra'ila zai yi jawabi
  • A wani bidiyo, an ga yadda wakilan kasashe su na ficewa daga dakin taron don nuna adawa da abin da Isra'ila ke yi a Gaza
  • Netanyahu ya jaddada cewa Isra'ila ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yakar Hamas har sai ta kubutar da mutanenta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

New York, USA - Rahotanni sun nuna cewa Firministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya gamu da fushin kasashe da dama a taron Majalisar Dinkin Duniya.

Lamarin dai ya faru ne a lokacin da aka bai wa Netanyahu damar fitowa gaban mahalarta taron domin gabatar da jawabinsa a birnin New York na kasar Amurka.

Benjamin Netanyahu a taron Majalisar Dinkin Duniya.
Hoton Benjamin Netanyahu a taron Majalisar Duniya bayan wakilan kasashe sun fice daga dakin taron Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kasashe da dama sun fita sun bar Netanyahu

Kara karanta wannan

Trump ya ce an masa makarkashiya bayan ya samu matsaloli 3 a taron UN

A wani faifan bidiyo da Aljazeera ta wallafa a shafin Facebook, an ga yadda wakilan kasashe da dama suka kunyata Netanyahu ta hanyar ficewa daga dakin taron.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana ganin wakilan kasashen sun dauki wannan mataki ne domin nuna adawa da taurin kan Isra'ila, wacce ke ci gaba da yiwa Falasdinawa kisan kare dangi a Gaza.

Lokacin da shugaban zaman ya nemi a kwantar da hankali, an ji kururuwa na kin amincewa yayin da wakilai suka fara fita daga dakin, suka bar kujeru da dama babu kowa.

Firaministan Isra'ila ya aika sako Gaza

Benjamin Netanyahu ya yi amfani da jawabinsa wajen yin magana kai tsaye da yahudawan da ke tsare a Gaza da kuma wadanda suka kama su watau Hamas.

Ya ce an kafa lasifikoki a yankin da ake tsare da mutanen Isra'ila kuma yan leken asiri sun kutsa cikin wayoyin salula a Gaza domin muryarsa ta isa gare su, in ji rahoton Sky News.

Da yake aika sako kai tsare ga wadanda kungiyar Falasdinawa watau Hamas ke tsare da su, Netanyahu ya ce:

Kara karanta wannan

Matsala ta kunno kai a Najeriya, miliyoyin yara na fuskantar hadarin mutuwa a Arewa

“Ba mu manta da ku ba, ba za mu yi kasa a gwiwa ba kuma ba za mu huta ba har sai mun dawo da kowa gida.”

Netanyahu ya kafa sharadin daina yaki a Gaza

Ga shugabannin kungiyar Hamas kuwa, Firminista Netanyahu ya ce:

"Ku ajiye makamai kuma ku saki mutanen mu da kuka kama nan take. Idan kuka yi haka, za ku rayu, idan kuka ki, Isra’ila za ta bi ku har gida ta kamo ku.”

Ya karyata “zargin kisan kare dangi” inda ya ce, “Idan Hamas ta amince da bukatunmu, yaki zai iya ƙarewa.”

Netanyahu ya nuna wata taswira ta yankin inda ya goge barazanar da ya ce Isra’ila ta kawar, kamar su Hezbollah da shirin makaman nukiliyar Iran.

An fara goyon bayan kafa kasar Falasdinu

A wani rahoton, kun ji cewa mamyan kasashen duniya sun fara fitowa fili su na tabbatar da amincewarsu da kafa kasar Falasdinu.

Kasashen kamar irinsu Biritaniya, Kanada da Australia sun amince da Falasɗinu a matsayin kasa mai 'yanci domin kawo karshen yakin Gaza.

Ana yi wa wannan matakin kallon wanda aka ɗauka sakamakon gajiya da yakin Gaza da kuma kokarin karfafa mafitar kafa kasashe biyu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262