Malawi: Shugaban Kasa Ya Yi Koyi da Jonathan, Ya Amince da Shan Kaye a Zabe
- Mulki zai sauya hannu a kasar Malawi bayan shugaban kasa, Lazarus Chakwera ya amince da shan kaye a zabe
- Lazarus Chakwera ya bayyana cewa ya amince abokin hamayyarsa ya ba shi tazara mai nisa da ba zai iya kamo shi ba
- Shugaban kasan ya sanar da cewa tuni ya kira abokin hamayyar ta sa domin taya shi murnar nasarar da ya samu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Kasar Malawi - Shugaban kasar Malawi, Lazarus Chakwera, ya amince da kayen da ya sha a hannun abokin hamayyarsa, Peter Mutharika.
Lazarus Chakwera ya amince da shan kayen ne a zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar.

Source: Twitter
Tashar BBC ta ce Lazarus Chakwera ya bayyana hakan ne a cikin jawabin da ya gabatar a ranar Laraba, 24 ga watan Satumban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lazarus Chakwera ya sha kaye a zabe

Kara karanta wannan
Atiku zai fifita Fulani idan ya samu mulki? Wazirin Adamawa ya kare kansa ga Yarbawa
Shugaban kasan na Malawi ya tabbatar da cewa ya kira Peter Mutharika domin taya shi murna, tashar TRT Africa ta tabbatar da labarin.
"Yan mintoci kaɗan da suka wuce, na kira Farfesa Mutharika domin yi masa fatan alheri. A bayyane yake cewa abokin hamayya ta, Peter Mutharika, ya ba ni tazara mai yawa."
"Abin da ya dace shi ne na amince da shan kaye saboda girmama zabin ku a matsayinku na ’yan kasa, da kuma girmama kundin tsarin mulki.”
- Lazarus Chakwera
A sakamakon da aka sanar daga jihohi 24 cikin 36, Chakwera ya samu kuri’u sama da 700,000, yayin da Mutharika ya samu 2,000,000.
Sai dai hukumar zabe ta kasar ba ta fitar da sakamakon zaben ba a sauran jihohi 12 da suka rage.
Mutharika zai koma kan mulkin Malawi
Peter Mutharika, mai shekara 85, tsohon shugaban kasar ne wanda ya yi mulki daga watan Mayu 2014 zuwa watan Yuni 2020.
Lazarus Chakwera wanda yake tsohon Fasto, ya hau mulki a 2020 bayan kayar da Peter Mutharika.
Zaben wanda aka gudanar a ranar 16 ga Satumba, ya fi karkata kan fushin jama’a wajen tabarbarewar tattalin arziki, rashin ayyukan yi, da tsadar rayuwa.
A lokacin mulkin Chakwera, hauhawar farashin kayayyaki ya kai kaso 33%, sannan farashin masara da takin zamani, muhimman kayan abinci a ƙasar da ke dogaro da noma, sun yi tashin gwauron zabi.
Masu sukarsa sun zarge shi da rashin iya mulki, rashin yanke shawara a kan lokaci, da kuma kasa cika alkawuran samar da ayyukan yi da yaki da cin hanci da rashawa.

Source: Twitter
Chakwera zai mika mulki cikin lumana
Duk da kayen da ya sha, Chakwera ya yi alkawarin mika mulki cikin lumana ga wanda ya yi nasara.
"A cikin kwanakin da suka rage, ina so ku sani cewa na kuduri aniyar mika mulki cikin lumana. Na san da yawa daga cikin masu goyon bayana za su yi bakin ciki da wannan sakamako."
- Lazarus Chakwera
Jonathan ya bada shawara game da shugabanni
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya bukaci a rika gudanar da sahihin zabe a nahiyar Afrika.
Goodluck Jonathan ya bayyana cewa ya kamata a rika kawar da shugabannin da ba sa yi wa jama'a aiki.
Tsohon shugaban kasan ya koka kan yadda shugabanni suke amfani da danniya da magudin zabe don ci gaba da zama a kan madafun iko.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
