'Uban Kuturu Ya Yi Kaɗan': Netanyahu Ya Faɗi Fargaba kan Tabbatuwar Falasɗinu

'Uban Kuturu Ya Yi Kaɗan': Netanyahu Ya Faɗi Fargaba kan Tabbatuwar Falasɗinu

  • Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi martani bayan wasu kasashe sun amince da kasar Falasdinu
  • Netanyahu ya ce ba za su amince da kasar Falasdinu ba, inda da ya aika gargadi ga shugabannin wasu kasashe
  • Ya ce bayan kisan gilla na 7 ga Oktobar bara bai kamata a amince da kasar ba inda gargadin cewa kasar Falasdinu ba za ta tabbata ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tel Aviv, Isra'ila - Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya nuna bacin ransa kan matakin wasu kasashen duniya.

Netanyahu ya magantu a ranar Lahadi 21 ga watan Satumbar 2025 bayan wasu kasashe sun amince da kasar Falasdinu.

Isra'ila ta magantu kan amincewa da kasar Falasdinu
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Getty Images

Rahoton Times of Israel ya ce ba za a taba kafa kasar Falasdinu ba idan dai sunanan saboda kisan gilla da take yi.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta samu koma baya, Birtaniya da wasu manyan kasashe 2 sun amince da kasar Falasdinu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kasashen da suka amince da Falasdinu

Hakan ya biyo bayan matakin wasu kasashen duniya na nuna goyon baya ga kasancewar kasar Falasdinu.

Falasdinawa sun samu tagomashi a burinsu na ganin sun samu kasa mai 'yanci da cin gashin kanta.

Kasashen Birtaniya, Canada da Australia sun amince da Falasdinu a matsayin kasa mai 'yanci a hukumance.

Sai dai, matakin bai yi wa kasar Isra'ila dadi ba, inda ministan tsaronta ya fito ya soki amincewa da Falasdinu.

Netanyahu ya gargadi kasashe kan Falasdinu
Benjamin Netanyahu yayin taro da shugabannin duniya. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Getty Images

Falasdinu: Gargadin Netanyahu ga kasashen duniya

Firayim ministan ya aika sakon gargadi ga shugabannin Birtaniya, Australia da Kanada bayan amincewarsu da Falasdinu, cewar rahoton Punch.

Ya ce:

"Ina sako na musamman ga kasashen da suka amince da kasar Falasdinu bayan mummunan kisan gilla a ranar 7 ga watan Oktoba.
"Wannan ya nuna kuna goyon bayan ta'addanci da kuma sakawa wadanda ake zargi da kisan kiyashi.
"Kuma ina da wani sako gare ku, hakan ba zai taba faruwa ba, babu yadda za a yi a samu kasar Falasdinu a Yammacin kogin Jordan."

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Malamin da ya fi 'tsufa' yana wa'azi ya bar duniya yana shekaru 95

Netanyahu ya kuma yi alkawarin fadada matsugunan Yahudawa a yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.

Ya ce ya dauki shekaru yana yaki da wannan yunuri da ake yi wanda ya ce ba zai taba bata loakcin da ya yi kan haka ba domin ganin an dakile faruwar hakan.

Ya kara da cewa:

“Shekara da shekaru, na dakile kirkirar wannan kasa ta ta'addanci duk da yawan matsin lamba daga gida da kuma waje.
“Mun yi hakan ne cikin jajircewa da kuma fikirar siyasa, duk da haka, mun kara fadada daular Yahudawa a Judea da kuma Samaria kuma za mu ci gaba a kan wannan hanya."

Harin Qatar: Trump ya saba da Isra'ila

A baya, mun ba ku labarin cewa kasar Isra’ila ta yi magana kan harin da ta kai a birnin Doha duk da ikirarin Shugaba Donald Trump na Amurka.

Kasar ta kare harin da ta kai kan shugabannin Hamas a Qatar bayan sukar hakan daga Trump, wanda ya bayyana rashin amincewa.

Kara karanta wannan

kafa kasar Gaza: Kasashen Afrika 4 da ba su goyi bayan Falasdinu ko Isra'ila ba

Jakadan Isra’ila a Majalisar Dinkin Duniya, Danny Danon, ya ce ba hari kan Qatar ba ne, hari ne kan 'yan kungiyar Hamas.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.