'Yan Bindiga Sun Farmaki Bayin Allah Suna Ibada, An Rasa Rayukan Mutane 22 a Nijar

'Yan Bindiga Sun Farmaki Bayin Allah Suna Ibada, An Rasa Rayukan Mutane 22 a Nijar

  • Mahara dauke da bindigogi a kan babura sun hallaka akalla mutane 22 a jihar Tillaberi da ke yammacin Jamhuriyar Nijar
  • An ce mafi yawan wadanda aka kashe suna wajen taron ibada ne lokacin da aka kai harin, yayin da aka kashe wasu a Takoubatt
  • Kungiyoyin jihadi masu alaka da Al-Qaeda da ISIS na ci gaba da kai hare-hare a yankin, lamarin da ya jefa jama’a cikin firgici

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Nijar – Gungun mahara dauke da miyagun makamai a kan babura sun kai hari wani kauye da ke yammacin Nijar, inda suka kashe mutane 22, da ke halartar taron ibada.

Rahotanni sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin a yankin Tillaberi, kusa da iyakokin Mali da Burkina Faso, inda kungiyoyin jihadi ke ta da zaune tsaye.

Kara karanta wannan

Dan majalisar Filato da ake nema ruwa a jallo ya mika kansa, ICPC ta tsare shi

'Yan ta'adda sun kashe masu ibada a yankin Tillaberi da ke yammacin Nijar.
Dakarun yaki da kungiyoyin jihadi a Tillaberi, yammacin Jamhuriyyar Nijar, suna rangadi a motarsu. Hoto: BOUREIMA HAMA
Source: Getty Images

Yadda aka kashe masu ibada 22 a Nijar

Wani mazaunin yankin ya shaida wa AFP cewa an fara kashe mutane 15 a wajen da ake gudanar da ayyukan ibadar a kauyen Takoubatt.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga nan ne kuma 'yan bindigar, suka hau baburansu, suka nufi wajen garin inda suka sake kashe wasu mutane bakwai.

Gidan talabijin na Elmaestro ya rahoto wani mazaunin yankin, da ya nemi a saka sunansa yana cewa:

"Sun yi wa mutane 22 da ba su ji ba ba su gani ba kisan gilla, sam babu imani a abin da suka aikata."

Dawowar hare-hare a yankin Tillaberi

Wani mai rajin kare hakkin bil’adama a Nijar, Maikoul Zodi, ya bayyana cewa:

“Yankin Tillaberi ya sake shiga cikin tashin hankali da asarar rayuka da dukiyoyi, sakamakon hare-haren miyagun 'yan ta'adda.”

Sai dai duk da kasancewar sojoji da dama a yankin, gwamnatin sojin da ta karbi mulki shekaru biyu da suka gabata ta kasa magance matsalar 'yan jihadi a yankin.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Ƴan bindiga sun sace ƴar NYSC da ɗalibar jami'a, suna neman N50m

A makon da ya gabata kadai, an kashe akalla sojoji 20 a yankin, wanda ya sa kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka fara kira ga gwamnati ta dauki matakan gaggawa.

Kungiyar Human Rights Watch ta bukaci hukumomin Nijar da su kara kokari wajen kare fararen hula daga hare-haren jihadi, inji rahoton Channels TV.

'Yan ta'adda na ci gaba da kai hare-hare yankin Tillaberi duk da sojoji ne ke mulki a Jamhuriyyar Nijar.
Wasu sojojin Nijar suna gadin ofisoshin jakadancin Faransa da Nijar a birnin Niamey. Hoto: -/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

An kashe fiye da mutane 1,800 a Nijar

Kungiyar ta ce tun daga watan Maris zuwa yanzu, kungiyar ISIS ta kashe mutane sama da 127 a hare-hare biyar.

Kungiyar ACLED kuma ta kiyasta cewa sama da mutane 1,800 aka kashe a Nijar tun daga Oktobar 2024, inda kashi uku cikin hudu aka kashe su a yankin Tillaberi.

Wannan harin na zuwa ne bayan makonni kadan da aka kashe mutane 37 ciki har da yara 14 a kauyen Darey Dey, wanda ke cikin yankin Tillaberi, cewar rahoton Aljeera.

'Yan ta'addar dauke da makamai sun kai harin ne lokacin da jama’a ke aiki a gonaki, lamarin da ya kara tabbatar da hadarin da ke ci gaba da addabar yankin.

Makiyaya sun kashe masu ibada a Benue

Kara karanta wannan

Mutane sun mutu da wani karamin jirgin sama ya gamu da hatsari, an samu bayanai

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu makiyaya dauke da mugayen makamai sun farmaki jihar Benue, suka kashe 10 da ke kan hanyar coci.

Wani mazauni ya bayyana cewa an kai harin da misalin karfe 6:00 na safe, inda aka harbe mata da yara, tare da jikkata mutane 25.

Kwamishinan yada labarai ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa an samu yawaitar makiyaya dauke da makamai a kwanaki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com