Kirk: Trump, Netanyahu Sun Shiga Takaici bayan Harbe na Hannun Daman Isra'ila

Kirk: Trump, Netanyahu Sun Shiga Takaici bayan Harbe na Hannun Daman Isra'ila

  • 'Dan gwagwarmaya mai ba Isra'ila kariya, Charlie Kirk, ya mutu bayan an harbe shi a wani taro a jami’a a Utah a Amurka
  • Shugaba Donald Trump da takwaransa, Benjamin Netanyahu na Isra'ila, sun yi jimami da cewa mutuwarsa babban rashi ne
  • Hukumomin Utah sun tabbatar da cewa an harbe shi da harsashi daya ne, inda suka bayyana cewa kisan gilla aka masa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amurka – Manyan shugabanni a Amurka da kasashen waje sun nuna alhini kan kisan Charlie Kirk a wani taron jami’a a Utah.

Mutuwar Kirk, wanda ya kasance babban mai goyon bayan Shugaba Donald Trump, ta tayar da jijiyoyin wuya a fadin duniya.

Charlie Kirk da aka harbe a kasar Amurka
Charlie Kirk da aka harbe a kasar Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Benjamin Netanyahu ya wallafa a X cewa an harbe shi da harsashi yayin da yake halartar wani taro, wanda hakan ya jawo mahalarta suka watse.

Kara karanta wannan

NDLEA ta kama wiwi mai nauyin kilo 112 a wajen hadarin mota a Kano

Hukumomin yankin Utah na kasar Amurka sun ce suna kallon lamarin a matsayin kisan gilla da aka tsara domin kawar da shi.

Trump da Netanyahu sun yi jimamin Charlie Kirk

Shugaba Donald Trump ya bayyana Kirk a matsayin “babba, kuma mashahuri” wanda ya fahimci matasa a Amurka fiye da kowa.

Trump ya sanar da cewa an umurci a sauke tutoci kasa a fadin Amurka har zuwa ranar Lahadi a matsayin girmamawa ga marigayin.

A wani sako da fadar White House ta wallafa a X, Trump ya danganta mutuwar Kirk da abin da ya kira da tasirin masu tsattsauran ra’ayi.

Ya yi kira da cewa lokaci ya yi da Amurkawa za su gane cewa kalaman kiyayya kan kai ga tashin hankali da kisan gilla.

Shugaba Trump tare da Benjamin Netanyahu
Shugaba Trump tare da Benjamin Netanyahu na Isra'ila. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shugaban Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce Kirk aboki ne nagari mai kare Isra'ila tare da nuna kishin al’ummar Yahudawa.

Ya bayyana cewa jimlar mutuwarsa babban rashi ne ga duniya baki ɗaya, musamman ga kasar Isra'ila.

Kara karanta wannan

Waye Larry Ellison? Makusancin shugaban kasa da ya fi kowa kudi yau a duniya

Netanyahu ya tuna cewa sun yi magana da Kirk mako biyu da suka gabata inda ya gayyace shi zuwa Isra’ila, amma ba zai samu damar zuwa ba saboda mutuwarsa.

Tarihin rayuwa da rawar da Kirk ya taka

Rahoton Al-Jazeera ya nuna cewa Charlie Kirk mai shekaru 31, ya kafa TP USA domin wayar da kan matasa kan ra’ayin mazan jiya da kishin kasa.

Kungiyar ta zama muryar matasa masu goyon bayan manufofin Trump da kare tsarin siyasa na mazan jiya.

Kirk ya kasance jigo a harkokin siyasa, musamman wajen shirya tarurrukan matasa da yaƙin neman zabe.

Har yanzu hukumomin Utah na ci gaba da bincike kan wanda ya aikata kisan, inda suka bayyana shi a matsayin harin da aka tsara.

Legit ta tattauna da Muhammad

Yayin zantawa da Legit Hausa, Muhammad Abubakar ya bayyana cewa bai ji wani bakin ciki ba kan kisan gillan da aka yi wa Kirk.

Muhammad ya ce:

"Na dauki kisan shi a matsayin wata alama ta nuna adawa da kisan kare dangi da ake yi wa Falasdinawa a Gaza."

Kara karanta wannan

Wike ya laftawa Ganduje da wasu manya tarar miliyoyin Naira a kan filaye

Trump zai hana 'yan Iran yin sayayya

A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Donald Trump na shirin sanya wa 'yan Iran da za su shiga Amurka takunkumin sayayya.

Hakan na zuwa ne yayin da kasashen duniya da suka hada da Iran za su taru a Amurka domin taron majalisar dinkin duniya.

Wakilan Iran na amfani da damar wajen sayayya a manyan shagunan Amurka, wanda hakan Trump ke son hanawa a bana.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng