Duniya Ta Yi Sabon Attajirin da Ya Fi Kowa Kudi, An Sha gaban Elon Musk Mai N570tr

Duniya Ta Yi Sabon Attajirin da Ya Fi Kowa Kudi, An Sha gaban Elon Musk Mai N570tr

  • Larry Ellison ya zama mutum mafi arziki a duniya bayan hannayen jarin kamfanin Oracle sun tashi da 40% a kasuwar hada hada
  • Alkaluma sun nuna cewa Ellison ya mallaki $393bn (kimanin ₦591.9trn), inda ya zarce Elon Musk, wanda ya mallaki kimanin ₦578.4trn
  • Duk da cewa yawancin kudin Ellison yana fitowa ne daga kamfanin Oracle, yana da wasu hanyoyi da dama da yake samun kudi da su

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Larry Ellison, wanda ya kafa kamfanin Oracle, ya samu karuwar dukiya ta ban mamaki, inda a yanzu ya zama mutum mafi arziki a duniya.

Larry Ellison ya samu wannan matsayi ne bayan hannayen jarin kamfaninsa sun yi tashin gwauron zabo a kasuwar hada-hadar hannayen jari a ranar Laraba.

Larry Ellison ya zama mutum mafi kudi a duniya bayan arzikinsa ya karu zuwa $393bn
Larry Ellison, shugaban kamfanin Oracle, wanda yanzu ya zama mutum mafi kudi a duniya. Hoto: @larryellison/X
Source: Getty Images

Larry Ellison ya zama mafi kudi duniya

Kara karanta wannan

Mele Kyari: Tsohon shugaban NNPCL ya fada komar EFCC, an ji dalili

Farashin kowane hannun jarin Oracle ya tashi da 40% zuwa $340, lamarin da ya sa darajar kamfanin ta haura zuwa $958bn (kimanin ₦1,443.1trn), inji rahoton The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar rahoton Bloomberg Billionaires Index, wannan karin ya sa dukiyar Ellison ta kai $393bn (kimanin ₦591.9trn), inda ya zarce Elon Musk wanda ke da $384bn (kimanin ₦578.4trn).

Wannan ya sanya Ellison ya shiga sahun gaba a jerin masu arziki na duniya, inda ya bar Musk a matsayi na biyu.

Hakan ya kuma sanya Ellison ya shiga gaban sauran attajiran duniya irin su Mark Zuckerberg na Facebook da kuma Jeff Bezos na Amazon.

Alakar Larry Ellison da Elon Musk

Duk da cewa yawancin kudin Ellison yana fitowa ne daga kamfanin Oracle, yana da wasu kadarori da dama da yake samun kudi da su, inji rahoton AP.

Yana da hannun jari a Tesla, tsibirin Lanai a Hawaii, tawagar tseren jiragen ruwa, da kuma gasar kwallon teburi ta Indian Wells.

Haka kuma ya taimaka wajen sayen Twitter (X) inda ya zuba jarin $1bn (kimanin ₦1.5trn) domin kyakkyawar alakarsa da Elon Musk.

Kara karanta wannan

Kotun Amurka ta kama tsohon shugaba a NNPCL da cin hanci, zai sha daurin sama da shekaru 10

Ellison ya taba zama a kwamitin Tesla daga 2018 zuwa 2022, kuma na lokacin sayen Twitter, ya amince da zuba jari ba tare da jinkiri ba.

Har ila yau, littafin tarihin Musk da Walter Isaacson ya rubuta, ya nuna cewa Ellison ya sha gayyatar Musk zuwa tsibirinsa na Hawaii domin tattaunawa da kuma hutawa.

Larry Ellison ya zama mutum mafi kudi a duniya bayan da darajara kamfaninsa ta karu a kasuwar hannun jari.
Larry Ellison, shugaban kamfanin Oracle, wanda ya fi kowa kudi a duniya yana magana a wani taro. Hoto: @larryellison/X
Source: AFP

Abin da ya daga darajar mai kudin duniya

Darajar Oracle ta karu ne saboda karuwar bukatar kamfanonin AI da ke amfani da sabis na gajimare, ciki har da OpenAI, masu tafiyar da ChatGPT.

Wadannan sabis suna bukatar manyan cibiyoyin sadarwa irinsu Oracle domin gudanar da ayyukansu. Wannan karuwar bukata ta kara darajar kamfanin da kuma dukiyar Ellison.

Larry Ellison mai shekaru 81 ya zama mutum mafi arziki a duniya bayan ya zarce Elon Musk, inda kamfanin Oracle ya shi damar limancin attajiran duniya.

Trump na barazanar korar Musk daga Amurka

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Donald Trump ya gargadi Elon Musk da cewa yana dab da rufe harkokinsa a Amurka, ya koma Afirka ta Kudu.

Kara karanta wannan

Tashin farashin mai a duniya ya shafi Najeriya bayan harin Isra'ila a Qatar

Kalaman Trump na zuwa ne bayan da Elon Musk ya yi barazanar hana duk sanatan Amurka da ya goyi bayan dokar "Big Beautiful Bill" cin zabe.

Sai dai Trump ya tunatar da Elon Musk cewa ya dogara ne da tallafin da Amurka ke ba shi, kuma idan ya janye shi, ba zai iya ci gaba da kasuwanci a kasar ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com