Ana Shirin Amincewa da Kasar Falasdinu, Trump Ya Kawo Babban Cikas
- Kasar Amurka ta hana shugabannin Falasɗinu shiga taron UNGA a New York, ciki har da Shugaba Mahmoud Abbas
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da soke biza da ƙin bayarwa ga jami’an PLO da PA kafin taron
- Wannan mataki ya biyo bayan shirin wasu ƙasashen Yamma na amincewa da ƙasar Falasɗinu a hukumance
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Kasar Amurka ta kuma kawo cikas yayin da ake shirin gudanar da taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA).
Za a gudanar da taron ne a watan Satumbar 2025 a birnin New York da ke kasar Amurka domin tattauna batutuwa da dama da wadanda suka shafi yancin Falasdinawa.

Source: Getty Images
Trump ya hana jami'an Falasdinawa biza
Rahoton Aljazeera ya ce Shugaba Donald Trump ya hana jami’an Falasɗinu, ciki har da Shugaba Mahmoud Abbas, halartar babban taron.

Kara karanta wannan
'Yan daba sun tarwatsa taron ƴan adawa da El Rufa'i ya halarta a Kaduna, an ji raunuka
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan matakin na zuwa ne yayin da wasu ƙasashen Yamma ke shirin amincewa da ƙasar Falasɗinu.
Hakan na cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta tabbatar a ranar 29 ga Agustan 2025 da muke ciki.
Sakataren Harkokin Waje, Marco Rubio, ya tabbatar da ƙin bayar da biza da kuma soke waɗanda aka bayar.
Gwamnatin Donald Trump ta bayyana a fili cewa:
"Yana cikin muradin tsaron ƙasarmu, mu riƙa ɗaukar PLO da PA da alhakin rashin cika alkawurransu, da kuma ɓata damar samun zaman lafiya."

Source: Facebook
Rangwamen da Amurka za ta yi ga Falasdinu
Rubio ya ce wadanda abin ya shafa sun hada da mambobin Ƙungiyar ’Yancin Falasɗinu (PLO) da Hukumar Falasɗinu (PA) kafin zaman taron, cewar Washington Post.
Har yanzu ba a tabbatar da jami’ai da takunkumin zai shafa ba, domin mambobin MDD da masu zaman benci kamar Falasɗinu kan aika manyan tawaga zuwa UNGA.
A cikin sanarwar, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce za ta bayar da rangwame ga Ofishin Hukumar Falasɗinu a MDD, wanda Jakada Riyad Mansour ke jagoranta a halin yanzu.
Abin da Jakadan kasar Falasdinu ya fada
Yayin da yake magana da ’yan jarida jim kaɗan bayan sanarwar, Mansour ya ce Shugaban Falasɗinu, Mahmoud Abbas na shirin halartar taron MDD na watan gobe.
Ya ce ba a bayyana ba ko wannan matakin na Amurka zai shafi ziyarar Abbas da aka tsara a watan Satumbar 2025 da ke tafe.
“Za mu ga daidai abin da hakan ke nufi da yadda zai shafi kowane daga cikin tawagarmu, sannan mu mayar da martani yadda ya dace."
- Cewar Mansur
An caccaki Tinubu kan kama shugaban Falasdinawa
Kun ji cewa kungiyoyin farar hula sun bukaci a gaggauta sakin shugaban al’ummar Falasdinawa da aka kama a birnin Abuja da ke Najeriya.
Bayanin da suka fitar ya zargi jami’an tsaro da karya dokokin kare hakkin Bil’adama wajen kama shugaban.
Kungiyoyin sun gargadi gwamnati da ka da Najeriya ta shiga rikicin Gabas ta Tsakiya ta hanyar nuna son kai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
