Baltasar: Kotu Ta Hukunta Jami'in Gwamnatin da Bidiyoyin Lalatarsa da Mata Suka Yadu

Baltasar: Kotu Ta Hukunta Jami'in Gwamnatin da Bidiyoyin Lalatarsa da Mata Suka Yadu

  • Baltasar Ebang Engonga ya fuskanci hukunci bayan an gurfanar da shi a gaban kotu kan zarge-zargen da suka shafi almundahanar kudade
  • Tsohon shugaban na hukumar ANIF ta kasar Equatorial Guinea, ya yi suna ne bayan wasu bidiyoyinsa na batsa sun karade duniya
  • Bayan dogon lokaci ana shari'a, kotun ta same shi da laifi inda aka tura shi zuwa gidan gyaran hali tare da lafta masa tara

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Equatorial Guinea - Wata kotu a kasar Equatorial ta yanke hukunci ga babban jami'in gwamnati, Baltasar Ebang Engonga.

Kotun ta yanke hukuncin daurin shekara takwas a gidan gyaran hali bisa samunsa da laifin wawure kuɗi.

Kotu ta yankewa Baltasar hukunci
Hoton Baltasar Ebang Engonga wanda bidiyoyinsa sun karade duniya Hoto: @kabumba_justin
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an yankewa Baltasar Ebang Engonga hukunci ne a ranar Laraba, 27 ga watan Agustan 2027.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta yankewa Baltasar hukunci

Daraktan yada labaran Kotun Koli, Hilario Mitogo ya sanar wa manema labarai hukuncin da aka yanke ta sakon WhatsApp.

Kara karanta wannan

'Dan shugaban ƙasa ya sayar da jirgin gwamnati, kotu ta ɗaure shi shekara 6 a Guinea

Kotun ta lardin Bioko ta same shi da laifin karkatar da kuɗaɗen da aka ce na alawus ɗin tafiyar aiki ne, inda ya yi amfani da su don bukatunsa na kashin kai, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Hilario Mitogo ya ce kotun lardin ta yanke wa Engonga hukuncin daurin shekara takwas tare da biyan tarar da ta kai dala 220,000

Ana tuhumar Baltasar Ebang Engonga, wanda ya riga ya yi aure kuma tsohon shugaban hukumar binciken harkokin kuɗi ta kasar ne, tare da wasu manyan jami’ai guda biyar, kan wawure kuɗaɗe masu yawa.

Kudaden da ake tuhumarsu da wawurewa sun kai dubban daloli a kasar mai arzikin mai da ke yankin tsakiyar Afirka.

Baltasar ya girgiza duniya da zargin lalata

Baltasar Ebang Engonga ya kuma shahara ne saboda bayyanarsa a cikin bidiyon batsa yana lalata tare da matan wasu manyan jami’an gwamnati.

Ebang Engonga wanda aka fi saninsa da lakabin “Bello”, shiga labaran duniya a watan Nuwamban 2024, bayan bayyanar bidiyoyinsa na batsa, yana lalata da mata daban-daban.

Wasu daga cikin bidiyoyin wadanda suka bayyana, an yi su ne a ofishinsa da ke a ma’aikatar kuɗi.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Sarkin da ya 'kunyata' Najeriya a Amurka

Bidiyoyin dai sun bayyana ne yayin da yake tsare don shari’ar wawure kuɗi.

Kotu ta hukunta Baltasar Ebang Engonga
Hotunan tsohon shugaban ANIF, Baltasar Ebang Engonga Hoto: Baltasar Ebang Engonga
Source: Facebook

Bidiyon sun haddasa barkewar barkwanci da annashuwa a kafafen sada zumunta, ciki har da waka, rawa, da kuma wallafa magani na barkwanci da aka kira “Balthazariem”.

Bayan bayyanar bidiyoyon nasa, gwamnatin kasar ta dauki matakin kare aukuwar irin abubuwan da ya aikata a cikin ofisoshi.

Gwamnatin ta sanar da shirinta na sanya kyamarori a ofisoshi domin sanya idanu kan.abubuwan da ke faruwa.

Gwamnati ta kori Baltasar daga mukaminsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin kasar Equatorial Guinea ta dauki matakin ladabtarwa kan Baltasar Ebang Engonga.

Gwamnatin ta kori Baltasar daga kan mukaminsa na shugavan hukumar binciken kudi (ANIF).

An dai dauki wannan matakin ne bayan bayyana bidiyoyinsa masu dumbin yawa yana lalata da mata daban-daban, ciki har da matan manyan jami'an gwamnati.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng