Isra'ila Ta Jefa Bama Bamai kan Asibitin Nasser, Sama da Mutane 15 Sun Mutu a Gaza

Isra'ila Ta Jefa Bama Bamai kan Asibitin Nasser, Sama da Mutane 15 Sun Mutu a Gaza

  • Harin bama bamai da Isra’ila ta kai asibitin Gaza ya kashe mutum 15 ciki har da ‘yan jarida hudu, yayin da wasu suka ji raunuka
  • An ce Isra'ila ta kai hari ne sau biyu, inda ta kai na biyun a dai dai lokacin da masu ceto da ‘yan jarida suka je wurin harin farko
  • Bayan ci gaba da kai hari don kwace birnin Gaza, Hamas ta nuna cewa hare-haren sun nuna Isra'ila ba ta da niyyar tsagaita wuta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Gaza - Isra’ila ta kai hari a asibitin Nasser da ke Gaza a ranar Litinin, inda aka kashe aƙalla mutum 15 ciki har da ‘yan jarida hudu.

Mai daukar hoto da bidiyo, Hussam al-Masri, ɗaya daga cikin ‘yan jaridar da aka kashe a harin farko, yana aiki ne da Reuters, in ji jami’an lafiya na Falasɗinu.

Kara karanta wannan

Al'umma sun samu sauƙi: Sojoji sun damƙe hatsabibin ɗan bindiga, yaransa 13

Isra'ila ta kai hare-hare biyu a wani asibitin Nasser da ke Gaza, inda mutane 14, ciki har da 'yan jarida suka mutu.
Masu aikin ceto, 'yan jarida da gungun mutane sun taru a asibitin Nasser da Isra'ila ta farmaka a Gaza. Hoto: Anadolu / Contributor
Source: Getty Images

An kuma ce Hatem Khaled, mai daukar hoto wanda shima yana aiki a matsayin ma'aikacin Reuters, ya samu raunuka a hari na biyu, inji rahoton kafar labaran.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Harin Isra'ila a Gaza ya kashe mutane 14

Rahoton ya nuna cewa rundunar sojin Isra’ila da ofishin Firayim Ministan kasar ba su yi wani tsokaci ba kan harin.

Shaidu sun ce harin na biyu ya faru ne bayan ma’aikatan ceto, ‘yan jarida da wasu mutane sun ruga zuwa wajen da aka kai harin farko.

Hussam al-Masri ne yake daukar bidiyo kai tsaye a daidai lokacin da aka kai harin farko, wanda ya sa bidiyo ya tsaya cak, alamar lalacewar layukan sadarwa.

Jami’an lafiya a Gaza sun bayyana sunayen sauran ‘yan jaridar da aka kashe da Mariam Abu Dagga, Mohammed Salama da Moaz Abu Taha, inda suka ƙara da cewa ɗaya daga cikin ma’aikatan ceto shima ya rasu a cikin harin.

Kara karanta wannan

'Mun sha azaba,' Adadin bayin Allah da 'yan ta'adda su ka hallaka a Katsina ya haura 55

Shirin Isra'ila na kwace birnin Gaza

A ranar Lahadi, sojojin Isra’ila suka koma kai hari a Jabalia don lalata mabuyar ‘yan gwagwarmaya da kuma ƙarfafa ikon rundunar a yankin, inji rahoton The Guardian.

Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya rantse da ci gaba da yaƙi kan birnin Gaza har sai ya kwace birnin, lamarin da ya tayar da hankula a ƙasashen waje da kuma adawa a cikin gida.

Katz ya ce za a ruguza birnin Gaza gaba ɗaya muddin Hamas ba ta amince ta kawo ƙarshen yaƙi bisa sharuɗɗan Isra’ila ba, wanda ya hada da sakin dukkan fursunoninta.

Hamas ta ce Isra'ila ba ta da niyyar tsagaita wuta yayin da ta ci gaba da yunkurin kwace birnin Gaza
Wasu daga cikin iyalan Falasdinawa da suka mutu suna kuka bayan Isra'ila ta kai hari birnin Gaza. Hoto: Anadolu / Contributor
Source: Getty Images

Martanin Hamas ga bukatar Isra'ila

A nata bangaren, kungiyar Hamas ta fitar da sanarwa a ranar Lahadi tana cewa shirin Isra’ila na kwace birnin Gaza ya nuna ba ta da niyyar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Ta ce yarjejeniyar tsagaita wuta ita ce “kadai hanya da za a saki fursunoni”, inda ta ɗora alhakin rayukan fursunonin a kan Firayim Minista Benjamin Netanyahu.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: An gano yadda ake amfani da siyasa wajen zafafa hare hare a Najeriya

Shirin da ke teburin tattaunawa ya hada da tsagaita wuta na kwanaki 60 da sakin fursunoni 10 da kuma mayar da gawarwaki 18. A madadin haka, Isra’ila za ta saki Falasɗinu kusan 200 da suke tsare a kurkuku.

Isra'ila ta amince da tsagaita wuta

A wani labarin, mun ruwaito cewa, an kama hanyar kawo karshen kashe-kashen Falasɗinawa da Isra'ila ke yi a zirin Gaza na tsawon wata da watanni.

Shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da cewa Isra'ila ta amince da duka sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 60.

Ya yabawa ƙasashen Qatar da Masar da suka shiga tsakanin don kawo zaman lafiya, yana mai fatan Hamas ta amince da wannan yarjejeniyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com