Minista Ta Sha Suka Ta ko Ina bayan Kalamanta game da Hana Sanya Hijabi a Makaranta

Minista Ta Sha Suka Ta ko Ina bayan Kalamanta game da Hana Sanya Hijabi a Makaranta

  • Ministan Tsaron Jama’a na Finland, Sanni Grahn-Laasonen ta jawo ce-ce-ku-ce kan kalamanta game da sanya hijabi a makaranta
  • Minstar ta ce hijabi ba su dace da makarantu ba a kasar lamarin ya jawo suka daga Musulmi da aka sani da yawan lullube jikinsu
  • Sakatare a kungiyar Musulmi, Pia Jardi ta ce babu 'yan ta'adda a Finland, ta gargadi cewa tattaunawar na iya kaiwa har a hana hijabi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Helsinki, Finland - Ministar Tsaron Jama’a ta Finland, Sanni Grahn-Laasonen (NCP), ta sha suka bayan kalamanta game da saka hijabi a makaranta.

Sanni Grahn-Laasonen ta bayyana cewa hijabi da nikabi ga dalibai Musulmi ba su dace a makarantu na kasar Finland ba.

An caccaki minista kan kokarin hana sanya hijabi a makaranta
Musulma sanye da niqabi. (Wannan hoto bai da alaka da labarin, an yi amfani da shi ne saboda misali). Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

Hijabi: An taso minista a gaba a Finland

Shugaban kungiyar 'Muslim Forum of Finland' ya ce batun ya yi yawa fiye da kima, musamman ganin cewa a Finland ba a yin hakan sosai, cewar Helsinki Times.

Kara karanta wannan

Mummunan hadari a Kano ya jawo asarar rayuka sama da 10

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun farkon shekarar karatu, batun hijabin daliban Musulmi ya zama magana a siyasa, amma maganar minista ta haifar da karin ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta.

Pia Jardi, Sakatare-Janar na kungiyar Musulmi ta Finland, ta bayyana cewa batun yara masu rufe fuska a makaranta ba shi da amfani a Finland.

Ta ce kusan babu wanda ke sanyawa a Finland, musamman a makarantun firamare da sakandare, don haka tattaunawar ta yi kama da wuce gona da iri.

Jardi ta gargadi cewa fara magana kan hijabi ko nikabi na iya zama hanyar kai ga haramta hijabi gaba ɗaya, kamar yadda ya faru a Faransa.

Grahn-Laasonen ta kare matsayinta da cewa yara su yi rayuwa cikin ‘yanci a al’umma, don tabbatar da daidaito, sadarwa da kuma tsaro a makaranta.

Jardi ta ce sanya hijabi wani ɓangare ne na ‘yancin addini, kuma kowa na da damar saka kaya yadda ya ga dama a Finland.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Gwamatin Tinubu za ta kashe Naira tiriliyan 3.6 a gyaran gada 1 kacal

Ana son hana mata saka hijabi a makaranta
Daliba sanye da hijabi a makaranta. (Hoton bai da alaka da labarin, an saka ne domin misali). Hoto: Vesa Moilanen / Lehtikuva.
Asali: Getty Images

Tsokacinn wasu ministoci kan lamarin

Wasu ministoci a Finland sun yi tsokaci kan batun, ciki har da Riikka Purra da ta ce a haramta hijabi da nikabi ga kananan yara gaba ɗaya, Daily Trust ta tabbatar da zancen.

Ministan Ilimi Anders Adlercreutz ya ce za a iya tattauna batun suturar da ke rufe fuska ta fuskar tsaro da gano mutum, amma ba da doka ba.

Laura Francke daga hukumar ilimi ta Finland ta ce rufe fuska da hijabi yana da wuya a makarantun Finland, kuma babu dokar hana hakan.

Ta bayyana cewa idan ana son kafa dokar hana, dole a yi canji a tsarin doka, abin da a yanzu ba a aiwatar da shi ba.

Dokokin makaranta na Finland suna iya buƙatar ɗalibai su saka sutura mafi dacewa da tsaro ko tsafta, kamar wajen iyo ko aikin fasaha a dakin gwaje-gwaje.

Majalisar Tajikistan za ta hana sanya Hijabi

Kara karanta wannan

Gungun 'yan ta'adda sun kutsa masallaci a Sakkwato, sun budewa masallata wuta

Kun ji cewa Majalisar tarayya ta kasar Tajikistan ta amince da wani kudurin doka na haramta sanya hijabi ga mata musulmi a kasar.

'Yan majalisar sun ce hijabi "bakin tufafi" ne da ke da alaka da masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama.

Gwamnatin Tajik karkashin jagorancin Emomali Rahmon ta zartar da kudirin dokar da ya haramta wa yara yin bukukuwan Sallah.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.