Tangardar Na'ura: Jirgin Sojin Sama Ya Yi Mummunan Hatsari, Mutane 7 Sun Mutu
- Jirgin sojin Venezuela ɗauke da mutane 10 ya yi hatsari a dajin Amazon inda aka rahoto cewa mutane uku ne kacal suka tsira
- Wadanda suka mutu a wannan hatsarin sun haɗa da mataimakin matukin jirgin, da wasu ma'aikatan lafiya da 'yan ƙabilar Yanomami
- Hatsarin jirgin sojin saman Venezuela ya shiga cikin jerin haɗurran jiragen sama da suka faru a duniya a kasa da wata biyu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Venezuela – Wani ƙaramin jirgin sojin sama da ke ɗauke da 'yan wata ƙabilar Amazon ya fadi a dajin kasar Venezuela a ranar Talata, inda mutane bakwai suka mutu.
Ma’aikatar tsaron Venezuela ta ce mutum uku sun tsira daga haɗarin, ciki har da matukin jirgin, kuma haɗarin ya faru ne sanadiyyar matsalar na'ura.

Source: Getty Images
Jirgin sojoji ya yi hatsari a Venezuela

Kara karanta wannan
Ba kunya ba tsoron Allah, matashi ya yaudari surukarsa ya caka mata adda har lahira
The Times of India ta rahoto cewa akwai akalla mutane 10 a cikin jirgin lokacin da ya yi hatsarin, ciki har da 'yan ƙabilar Yanomami, jami’an lafiya, da ma’aikatan jirgin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanda suka rasu sun haɗa da mataimakin matukin jirgin, da wasu sojoji da kuma 'yan ƙabilar Yanomami.
Jirgin dai na rundunar sojin saman Venezuela ne, kuma an tanade shi musamman don taimaka wa al’ummomin yankin Amazon a muhimman zirga-zirgarsu.
Ana fargabar mutane 50 sun mutu a Rasha
Wannan mummunan haɗari ya faru ne kwanaki kaɗan bayan wani jirgin fasinja mai ɗauke da kusan mutane 50 ya fadi a gabashin Rasha (Amur) a ranar Alhamis da ta gabata.
Jirgin, nau’in Antonov-24, mallakin kamfanin Angara Airlines, yana kan hanyar zuwa garin Tynda daga Blagoveshchensk ne lokacin da ya ɓace daga na’urar sa-ido kan jirage.
Hukumomi sun bayyana cewa babu wani mutum ko daya da ake tunanin ya tsira daga wannan hatsari, inji rahoton Channels TV.
Hatsarin jirgin saman Venezuela ya shiga jerin jerin haɗurran jiragen sama da aka ruwaito a duniya cikin kasa da wata biyu.

Source: UGC
Hatsarin jirgi a makarantar Bangladesh

Kara karanta wannan
Sojojin Najeriya sun fafata da ƴan bindiga, an cafke wani baƙon ɗan ta'adda a Yobe
A ranar 21 ga Yulin 2025, muka ruwaito cewa aƙalla mutane 27, mafi yawansu yara ‘yan makaranta, suka mutu bayan wani jirgin sojin Bangladesh ya fadi a cikin makarantarsu da ke Dhaka, babban birnin kasar.
Jirgin, nau’in F-7 BJI da aka ƙera a kasar China, ya fadi kai-tsaye a cikin makarantar Milestone School and College lokacin da yaran ke karatu.
Wannan haɗari ya kasance mafi muni da kasar ta Bangladesh ta taba fuskanta a fannin sufurin sama cikin shekaru da dama, inda ya jikkata fiye da mutane 170.
Hatsarin Air India ya hallaka mutane 260
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani jirgin Air India nau’in Boeing 787-8 Dreamliner da ke cike da mai ya tarwatse bayan tashi sama, inda ya hallaka mutane 260.
Mutane 242 daga cikin fasinjojin jirgin da wasu 19 da ke a ƙasa sun mutu, sai mutum guda kacal da ya tsira daga cikin jirgin da ke hanyar zuwa London.
Binciken farko da aka bayyana a ranar 12 ga Yulin 2025 ya nuna cewa an samu na’urorin kula da man jirgin a kashe, wanda ya katse isar man fetur ga injinan jirgin biyu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng