Ginin Makaranta Ya Rufta kan Dalibai Suna tsakiyar Karatu, An Samu Asarar Rayuka
- Ginin makarantar gwamnati ya rushe kan dalibai sakamakon ruwan sama mai ƙarfi, inda yara bakwai suka mutu, wasu 20 suka jikkata
- Rahotanni sun bayyana cewa ginin ya dade yana cikin yanayi marar kyau, kuma gwamnatin India ba ta dauki mataki a kai ba
- Bayan wannan iftila'i, gwamnan jihar Rajasthan ya ba da umarni a duba lafiyar gine-ginen gwamnati da suka haɗa da makarantu, asibitoci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
India – Wani ɓangare na ginin makarantar gwamnati ya rushe a gundumar Jhalawar da ke jihar Rajasthan a ranar Juma’a, 25 ga Yuli, 2025, inda yara bakwai suka mutu.
Hukumomi sun tabbatar da cewa dukkan waɗanda suka mutu dalibai ne, sannan yara 20 sun jikkata a iftila'in da ya faru sakamakon rushewar rufin ajinsu.

Asali: UGC
Ginin makaranta ya rufta kan dalibai a India
Ginin makarantar tsoho ne kuma ya rushe sakamakon ruwan sama mai ƙarfi a yankin, kamar yadda Amit Kumar, wani jami'in ƴan sanda na yankin, ya shaida wa Reuters.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani dalibi da ba a bayyana sunansa ba ya shaidawa manema labarai cewa:
“Duwatsu ne suka fara faɗowa cikin ajin... sai kwatsam rufin ya rushe gaba ɗaya, muka fito waje cikin gaggawa. Ana sanya dalibai 30 ne a cikin kowane aji."
Bidiyon da tashoshin talabijin suka wallafa ya nuna yadda mutane suka taru a wurin da ginin ya rushe, yayin da iyayen daliban da abin ya shafa ke kuka, sannan jami’ai na amfani da mota wajen cire tarkacen ginin.
Zargin sakaci daga bangaren hukumomi
Mutanen yankin sun bayyana fushinsu tare da zargin cewa sun sha fadawa hukumomi irin matsalar ginin, amma ba a ɗauki mataki ba har iftila'in ya faru.
“Wannan ya faru ne saboda sakaci daga bangaren gwamnati,” inji wani mazaunin yankin mai suna Balkishan a wata hira da jaridar The Hindu.
Ya kara da cewa:
“Ni da wasu ne muka yi gaggawar kai dauki wurin ginin, muka fara cire duwatsu da bangwayen ginin da hannu domin ceton yara.
“Kowa ya rude, yara na ta kuka, kowa na ƙoƙarin ceto su. Wasu daga cikinmu suka ɗauki yaran da aka ciro zuwa wata cibiyar lafiya da ke kusa."

Asali: Twitter
Gwamnatin jiha ta ɗauki matakan gaggawa
Gwamnan Rajasthan, Bhajanlal Sharma, ya bayyana alhinin sa a shafinsa na X:
“Wannan ifti'lai mai matuƙar tayar da hankali da ya faru sakamakon rushewar rufin makaranta a Peeplodi, Jhalawar, abin bakin ciki ne ƙwarai.
“An ba da umarni ga hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da kulawa da yaran da suka jikkata."
A safiyar ranar Juma’a, Bhajanlal Sharma ya kara wallafawa a shafinsa na X cewa:
“An bayar da umarni ga shugabannin hukumomi da dukkan kwamishinonin kananan hukumomi da su binciki lafiyar dukkanin gine-ginen gwamnati.

Kara karanta wannan
Gudumar majalisa za ta hau manyan gwamnati, za a hana su zuwa makarantu da asibitin kuɗi
“Gine-ginen da za a duba sun haɗa da makarantu, cibiyoyin kula da yara, asibitoci da sauran gine-ginen gwamnati, tare da aiwatar da gyare-gyare cikin gaggawa.”
Gini ya rufta kan dalibai a Yobe
A wani labarin, mun ruwaito cewa, bangon wani aji a makarantar sakandaren mata (GGSS) Potiskum da ke jihar Yobe ya rushe, inda ya yi sanadiyyar mutuwar wata daliba.
Rahotanni sun ce bangon ajin ya rufta kan daliban ne a lokacin da suke zaune suna karatu, ba tare da wani malami a cikin ajin ba.
Gwamnatin jihar Yobe ta bayyana cewa ta kaddamar da bincike domin gano ainihin musabbabin rushewar ginin, tare da daukar matakan gaggawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng