Jirgin Ruwa Dauke da Fasinjoji 571 Ya Kama da Wuta a tsakiyar Teku, Mutane Sun Mutu
- A kasar Indonesia, jirgin fasinja KM Barcelona 5 dauke da akalla fasinjoji 571 ya kama da wuta yayin da yake tafiya a tsakiyar teku
- Jami’an ceto sun tura jiragen ruwa da kwale-kwale don aikin agaji, inda suka yi nasarar ceto sama da mutane 650 daga cikin ruwan
- Jiragen ruwa a Indonesia na yawan fuskantar hadurra saboda cunkoso da rashin bin ka’idoji, kuma ana samu yawan mace-mace
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Indonesia - Masu aikin ceto a kasar Indonesia sun ceto akalla mutane 560 daga wani jirgin fasinja da ya kama da wuta a tsakiyar teku, yayin da mutane hudu suka mutu.
Jirgin KM Barcelona 5 ya kama da wuta ne da misalin karfe 12:00 na ranar Lahadi, a kan hanyarsa ta zuwa Manado, babban birnin jihar North Sulawesi, daga tsibirin Talaud.

Source: AFP
Indonesia: Jirgin fasinjoji ya kama da wuta
Franky Pasuna Sihombing, babban jami’in sojan ruwa na Manado ya tabbatar da faruwar lamarin ga kafar labaran AP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Franky Pasuna Sihombing, an tura jirgin ruwan tsaro, jiragen agaji guda shida da kwale-kwale masu amfani da iska domin aikin ceto.
Jami’an agaji sun ceto mutane da dama daga cikin teku, inda suka kai su tsibiran da ke kusa, sai kuma wasu masu kamun kifi da suka ceci wasu fasinjojin da ke sanye da rigunan ceto.
Hotuna da faya-fayan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna fasinjoji da dama cikin firgici suna tsalle daga cikin jirgin suna fadawa cikin ruwa yayin da wuta da hayaki mai kauri ke tashi daga cikin jirgin.
Aikin neman ceto ya ci gaba har yanzu, ko da yake babu rahoton wadanda ake zargin sun bace.
Sabani kan yawan mutanen da ke cikin jirgin
A baya hukumomi sun ce mutane biyar sun mutu, amma hukumar ceto ta kasa ta sake sabunta alkaluman zuwa uku da safiyar Litinin.
Hakan ta faru ne bayan da aka gano wasu fasinjoji biyu da aka ce sun mutu a jerin wadanda aka ceto kuma suke kwance a asibiti, ciki har da wani jariri dan wata biyu.
Franky Pasuna Sihombing ya shaidawa manema labarai cewa an riga da an kashe wutar da ta tashi daga bayan jirgin cikin sa’a daya.
Jadawalin fasinjojin jirgin ya nuna cewa mutane 280 ne kacal suka yi rajistar shiga cikin jirgin, sai kuma ma’aikata 15, inji rahoton Euro News.
Amma hukumar ceto ta kasa ta tabbatar da cewa 568 ne aka ceto, kuma an gano gawarwaki uku, ciki har da wata mata mai juna biyu.

Source: AFP
Yawan hadarin jirgin ruwa a Indonesia
Ana yawan samun irin wannan matsalar a Indonesia, inda za a ga cewa adadin fasinjoji a cikin jirgi ya bambanta da na rajista, abin da ke kara janyo hadurra da kuma wahalar aikin ceto, a cewar Sihombing.
Indonesia na da tsibirai fiye da 17,000, kuma jiragen ruwa na daga cikin hanyoyin sufuri da aka fi yawan amfani da su. Hadurran jirgin ruwa na faruwa akai-akai saboda rashin tsauraran matakan tsaro.
A ranar 14 ga Yuli, wani karamin jirgin ruwa da ke dauke da mutane 18 ya kife a tsakiyar teku, amma an yi nasarar ceto dukkaninsu a washegarin ranar.
A farkon watan nan ne wani jirgin ruwa ya nitse kusa da tsibirin shakatawa na Bali, inda mutane 19 suka mutu, yayin da 16 suka bace.
Jirgi ya kife da mutane a cikin teku
A wani labarin, mun ruwaito cewa, NEMA ta tabbatar da aukuwar hatsarin kwale-kwale a kauyen Sullubawa da ke cikin ƙaramar hukumar Shagari a jihar Sokoto.
Aƙalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu a haɗarin da ya faru da ranar Litinin, 2 ga Yuni, 2025, da misalin ƙarfe 9:30 na safe.
Rahotanni na farko sun bayyana cewa matsananciyar iska ce ta haddasa kifewar kwale-kwalen a tsakiyar kogin da ake amfani da shi wajen zirga-zirgar jama’a.
Asali: Legit.ng


