Masu kamun kifi sun ceto matar da tayi shekara 2 da bacewa a cikin teku

Masu kamun kifi sun ceto matar da tayi shekara 2 da bacewa a cikin teku

- Angelica Gaitan, ta tsallake rijiya da baya, inda masu kamun kifi suka samu nasarar tsintar ta a tsakiyar teku

- Da farko masu kamun kifin sun yi burus da ita, sai da suka hango ta tana daga musu hannu don neman taimako

- An ciro Angelica daga tekun ne tana cikin mawuyacin hali, wanda yanzu haka tana asibiti ana kula da lafiyarta

Shekaru 2 da sanarwar bacewar wata mata mai suna Angelica Gaitan, an samu nasarar cetota makon da ya gabata, bayan kwararowar gabar tekun arewancin kasar Colombia.

An gano cewa Angelica na can cikin tekun, tazarar mil daya daga birinin Puerto Colombia. Bayan nan ne aka kai ta gabar teku don amsar magani.

Kamar yadda jaridar La Libertad ta wallafa, masu kamun kifin da suka samu nasarar ceto ta da farko sun kyaleta ne tana yawo a saman ruwan, daga baya suka hango tana daga hannunta don neman taimako.

Kamar yadda wani bidiyo da Rolando Bisbal ya dauka ya nuna, bayan masu kamun kifin sun fito da ita daga ruwan, sun shigar da ita cikin kwale-kwale ne, inda suka zaunar da ita akan kujera a can gefen tekun.

Kamar yadda Bidiyon ya nuna, ko da aka fitar da Angelica daga ruwan, bata cikin hayyacinta.

A wata tattaunawa da gidan rediyon Kwalombiya suka yi da ita, ta sanar da su yadda aka hango ta a saman teku kafin a samu nasarar fito da ita.

Ta kara da yiwa Ubangiji godiya, inda take cewa, "hakika ina godiya ga Ubangiji da ya rayani, kuma bai sa na mutu a cikin tekun nan ba."

A cewar Angelica, "An kawo ni asibiti, inda ake kula da lafiya ta."

A wata tattaunawa da Angelica tayi da gidan Rediyon RCN, ta sanar da su yadda ta bar gida tun 2018 sakamakon rabuwarta da mijinta.

KU KARANTA: Bidiyo da hotunan budurwa ta garzaya wurin aikin saurayinta cikin shigar amare, ta bukaci a daura musu aure

Masu kamun kifi sun ceto matar da tayi shekara 2 da bacewa a cikin teku
Masu kamun kifi sun ceto matar da tayi shekara 2 da bacewa a cikin teku. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kotu ta yanke wa gagarumin makashin jama'a hukuncin kisa a Delta

A wani labari na daban, 'yan sanda sun balle kofar wani gida a Benin inda suka riski mutane 7 a mawuyacin hali. Mutum 1 daga cikinsu ya rasu, 6 kuma suna asibiti.

Ana zargin sun ci abinci sai suka kwanta, basu tashi washegari ba. Wani dan sanda ya sanar da jaridar Daily Trust cewa watakil hayakin janareto da suka kunna ne ya jawo wannan matsalar.

Al'amarin ya faru ne a gida mai lamba 40 akan titin Otete, kusa da layin masaka a Ogida quarters a cikin Benin City.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel