Kashim Shettima na Shirin Dauko Gawar Buhari, Jirgin Sama Ya Yi Hatsari a London
- Wani ƙaramin jirgin sama ya yi hatsari a filin jirgin Southend da ke London, lamarin da ya sa aka dakatar da dukkanin ayyukan jirage
- Jami’an ceto da masu bincike daga hukumar AAIB sun isa wurin hatsarin, amma har yanzu ba a san adadin mutanen cikin jirgin ba
- Wannan ya faru ne kafin Kashim Shettima da wasu jami’an gwamnati suka isa London domin karɓar gawar Muhammadu Buhari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
London – Wani ƙaramin jirgi ya yi hatsari a saman hanyar sauka da tashi na filin jirgin saman Southend da ke Essex, London.
Filin jirgin sama ta Southend ta dakatar da dukkanin ayyukanta har sai baba ta gani sakamakon wannan hatsarin da ya auku ranar Lahadi.

Source: Twitter
Jirgin sama ya yi hatsari a London
A cikin wata sanarwa da filin jirgin ya fitar a shafinsa na X, an bayyana cewa an soke dukkan jiragen da ke shirin sauka ko tashi daga filin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar ‘yan sandan Essex ta tabbatar da cewa an kira su zuwa wajen da hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 4:00 na yamma, bayan samun rahoton hadarin da ya shafi jirgin da tsawonsa ya kai mita 12 (kimanin ƙafa 39.4).
Har yanzu ba a bayyana yawan mutanen da ke cikin jirgin ba, kuma hukumomi ba su tabbatar da ko an samu asarar rayuka ba.
'Yan sandan Essex sun fitar da sanarwa cewa:
“Har yanzu muna nan a wurin da lamarin ya faru a filin jirgin sama na Southend. Jami’an ceto da masu binciken hadurra na jiragen sama suna ci gaba da gudanar da aiki.”
An tura motocin agaji zuwa filin jirgin
Bidiyon da wasu kafafen watsa labarai na Birtaniya suka wallafa – ko da yake ba a tabbatar da sahihancinsa ba – ya nuna wata guguwa mai kama da tashin wuta tana tashi daga saman tashar jirgin bayan hatsarin.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Gabashin Ingila ta tura motocin daukar marasa lafiya guda huɗu da wasu motocin agaji na musamman zuwa wurin da hatsarin ya faru.
Filin jirgin Southend ya bayyana cewa an dakatar da dukkanin jirage tare da rufe wurin, a matsayin matakin kariya yayin da bincike ke gudana.
Hukumar AAIB za ta gudanar da bincike
Shafin yanar gizon tashar jirgin ya nuna cewa akalla jiragen ƙasa da ƙasa guda biyar ne aka soke ayyukansu sakamakon wannan lamari.
An sanar da hukumar binciken hadurran jiragen sama (AAIB) kuma ana sa ran za ta jagoranci binciken kan abin da ya jawo hatsarin.
Filin jirgin sama na Southend yana a gabashin birnin London, kimanin mil 35 daga tsakiyar garin, kuma yana daukar zirga-zirgar jiragen ƙasa da ƙasa masu yawa.
Har yanzu babu tabbacin lokacin da za a dawo da ayyukan jiragen a filin.

Source: Twitter
Shettima ya isa London dauko gawar Buhari
Wannan na faruwa ne yayin da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da , suka isa birnin London domin dauko gawar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Channels TV ta ruwaito cewa Shettima da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ne suka jagoranci tawagar gwamnatin Najeriya zuwa Ingila.
Ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar, da gwamnan Borno, Babagana Zulum, na daga cikin manyan jami’an Najeriya da suka tarbe su.
Tinubu ya tura Shettima ya dauko gawar Buhari
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a Landan a yammacin Lahadi.
Bayan samun labarin, Tinubu ya tuntubi uwargidansa Aisha Buhari domin jajanta mata, sannan ya umarci mataimakinsa, Kashim Shettima, da ya tafi London domin rako gawar.
Buhari dai ya mulki Najeriya a matsayin shugaban soja da kuma shugaban farar hula, inda Tinubu ya umarci a sauke tutoci domin girmama rayuwar marigayin.
Asali: Legit.ng


