Tirkashi: Amurka Za Ta Taimakawa Isra'ila, Za a Kai wa Iran Sababbin Hare Hare
- Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa zai goyi bayan matakin Isra’ila na kai hari kan Iran idan har Tehran ta ci gaba da kera nukiliya
- Duk da haka, Trump ya fi son a cimma matsaya ta diflomasiyya da Iran, kamar yadda ya shaida wa Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu
- Rahotanni sun ce ba lallai ne Isra’ila ta nemi izinin Amurka kafin sake kai hari Iran ba, amma Trump na so a ci gaba da tattaunawa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa zai goyi bayan Isra'ila a hare-haren za ta kai kan Iran idan Tehran ta ci gaba da kokarin kera makamin nukiliya.
Duk da haka, Trump ya bayyana cewa ya fi son a samu matsaya ta diflomasiyya yayin ganawarsa da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, a birnin Washington DC.

Source: UGC
Matsayar Amurka kan sake kai hari Iran
Jaridar Wall Street Journal ta ruwaito cewa yayin ganawarsu a Fadar White House a ranar Litinin, Trump ya shaida wa Netanyahu cewa yana fatan Amurka ba za ta sake kai hari kan Iran ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
“Ba zan iya hango kaina ina son sake kai hari Iran ba.”
Sai dai a wata tattaunawa ta sirri, Netanyahu ya shaida wa Trump cewa idan Iran ta ci gaba da shirinta na kera makamin nukiliya, Isra’ila za ta sake kai hari.
Rahotanni sun nuna cewa Trump ya amsa da cewa ya fi son a daidaita da Tehran ta hanyar diflomasiyya, amma bai nuna adawa da shirin Isra’ila ba.
Wadannan tattaunawa sun bayyana rikicin matsin lamba da ya ke tsakanin ƙasashen uku tun bayan hare-haren Isra’ila da Amurka kan cibiyoyin nukiliyar Iran a watan da ya gabata.
Isra'ila na duba yiwuwar kai hari Iran

Kara karanta wannan
Shugaban Amurka ya gana da Firaministan Isra'ila, an ji abin da suka tattauna kan Iran
Rahotanni sun ce Trump na fatan barazanar kai harin gaba zai matsa wa Iran lamba ta yarda da yarjejeniya da za ta hana ta gina makamin nukiliya.
Isra’ila ba ta da cikakken yakinin cewa diflomasiyya za ta hana Iran sake bude shirin ta na kera makamin, yayin da Tehran ke neman tabbacin cewa ba za a sake kai mata hari ba kafin ta koma tattaunawa da Washington.
Wani babban jami’in Isra’ila ya bayyana cewa ba lallai ne Isra’ila ta nemi amincewar Amurka kafin sake kai hari kan Iran ba, a cewar rahoton WSJ.
Sai dai dangane da yadda Iran za ta himmatu wajen farfado da shirin nata, Netanyahu na iya fuskantar matsin lamba daga Trump domin a ci gaba da kokarin diflomasiyya da Tehran.

Source: Getty Images
Abubuwan da ke gaban shugabannin Iran
An ce idan shugabannin Iran suka ƙi yarda da buƙatar Trump na dakatar da nukiliya, kuma suka dawo da ayyukansu na uranium, to ana ganin harin da Isra’ila ko Amurka za su iya kaiwa ga shafe gwamnatin kasar.
Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, kamar sauran manyan jami’an gwamnatin Iran, ya bayyana a ‘yan kwanakin nan cewa Tehran na shirye don dawo da tattaunawar nukiliya.

Kara karanta wannan
Gaskiya ta fito kan rahoton Ahmed Musa ya raba tsala tsalan motoci a Kano Pillars
Sai dai ya ce hakan zai yiwuw ne kawai idan ba za a kai mata hari ba yayin da tattaunawar ke gudana, kuma Iran za ta nace a kan hakkinta na tace sinadarin uranium.
Fadar White House ta ƙi yin tsokaci kan tattaunawar Trump da Netanyahu, yayin da ofishin jakadancin Iran a Majalisar Ɗinkin Duniya ya ƙi amsa buƙatar yin jawabi.
Mummunar gobara ta yi barna a Amurka
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Donald Trump ya ziyarci Texas domin duba ambaliyar da ta yi sanadin mutuwar mutane 120 tare da bacewar wasu 160.
Trump zai gana da iyalan mamata da jami’an ceto a yankin Kudancin Texas, inda kogin Guadalupe ya balle, ya haifar da barna mai yawa.
Rahoto ya nuna cewa ambaliyar ta kashe yara 36 da ke sansanin Camp Mystic, mafi munin iftila'i tun bayan da Trump ya hau kujerar shugaban Amurka.
Asali: Legit.ng
