Babban Malami a Masallacin Annabi Muhammad SAW Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Malamin addini a masallacin Annabi Muhammad (SAW) da ke Madinah ya rasu a kasar Saudiyya
- Musulmi a faɗin duniya na alhinin rasuwar fitaccen malamin, Sheikh Dr. Rabi’ ibn Hadi al-Madkhali ya rasu a ranar Laraba
- Hukumar kula da Harami ta tabbatar da rasuwar malamin, tana mai mika ta'aziyya ga iyalansa, dalibansa da dukan masu kaunar iliminsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Madinah, Saudiyya - Duniyar Musulunci ta yi babban rashi bayan sanar da rasuwar shahararren malami a Saudiyya.
An tabbatar da rasuwar Sheikh Dr. Rabi ibn Hadi al-Madkhali a jiya Laraba 9 ga watan Yulin 2025.

Source: Facebook
Shafin Inside the Haramain ne ya tabbatar da haka a yau Alhamis 10 ga watan Yulin 2025 a manhajar X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadi al-Madkhali: Gudunmawar marigayin ga addinin Musulunci

Kara karanta wannan
Gwamna Abba ya ɗauko Mai Martaba Sarkin Lafiya, ya ba shi shirgegen muƙami a Kano
An gudanar da sallar jana’izar marigayin a Masallacin Annabi (Al-Masjid an-Nabawi) a Madinah, kuma an binne shi a Makabartar Al-Baqi‘ mai tsarki.
Dalibansa da masoyansa da manyan malamai daga sassa daban-daban na duniya ke alhinin rasuwarsa.
Ya rasu a cikin birni mai albarka na Manzon Allah bayan rayuwa cike da ilimi, gwagwarmaya a tafarkin Allah ta hanyar alkalami da magana, kare Sunnah, yakar bidi’o’i, da tsayawa kan ka’idojin sahihin tsarin addini.
Sheikh Rabi’ yana daga cikin fitattun masana a fannin al-Jarh wa al-Ta‘dil (nazarin amincewa da korar ruwayoyi), fannin da kusan ya bace a wannan zamanin.
Ya kasance mai tsayawa kan gaskiya ba tare da jin tsoro ba, mai tausayi ga mutane amma mai tsauri a kan masu son zuciya da masu kawo sababbin bidi’o’i.

Source: Facebook
Ana jimamin rasuwar Sheikh Rabi Hadi al-Madkhali
Sanarwar ta ce marigayin ya rasu a jiya Laraba inda ta yi addu'ar Ubangiji ya gafarta masa ya sanya shi gidan aljanna.
Sanarwar ta ce:
"Fadar Hukumar Kula da Harkokin Addini a Harami guda biyu, Harami Mai alfarma na Makka da na Annabi (SAW) tana mika ta'aziyyarta ta musamman da alhini ga iyalan marigayin, 'yan uwansa, dalibansa, malamai da masu wa'azi na Harami, bisa rasuwar Fitaccen Malami Sheikh Dr. Rabie bin Hadi Al-Madkhali.
"Malamin wanda ke koyarwa a Masallacin Annabi, ya rasu jiya, Allah ya jikansa.
"Muna rokon Allah ya masa rahama, ya sanya shi gidan Aljanna makomarsa, ya bai wa iyalansa da masoyansa hakuri da juriya, ya saka musu da lada mai yawa, ya kuma warkar da zukatansu daga radadin rashin sa."
An yi jana'izar Dantata a masallacin Annabi (SAW)
Mun ba ku labarin cewa bayan cika dukan sharuɗɗan Saudiyya, an yi jana'izar marigayi Alhaji Aminu Ɗantata a birnin Manzon Allah S.A.W.
Kamar yadda ya bar wasiyya, an yi wa fitaccen ɗan kasuwar sallah ta jana'iza a masallacin Annabi kuma an birne shi a maƙabartar Baqi'a.
Manyan jiga-jigai daga Najeriya da wakilan gwamnatin tarayya, ƴan uwa da iyalai sun halarci jana'izar ranar Talata, 1 ga watan Yuli 2025.
Asali: Legit.ng
