Sheikh Al-Sabuni: An yi jana’izar tsohon limamin masallacin Harami

Sheikh Al-Sabuni: An yi jana’izar tsohon limamin masallacin Harami

- An yi jana'izar tsohon Limamin Masallacin Harami da ke birnin Makkah, Sheikh Muhammad Ali Al-Sabuni

- Ya kasance daya daga cikin limaman da ke jagorantar sallar Taraweeh a Masallacin Harami a watan Ramadan kimanin shekara 57 da suka gabata

- Sheikh Muhammad Ali Al-Sabuni ya rasu yana da shekaru 91 a duniya

Rahotanni sun kawo cewa an yi jana’izar tsohon Limamin Masallacin Harami da ke birnin Makkah, Sheikh Muhammad Ali Al-Sabuni a kasar Turkiyya.

Babban malamin, Sheikh Muhammad Ali Al-Sabuni, ya kasance daya daga cikin limaman da ke jagorantar sallar Taraweeh a Masallacin Harami a watan Ramadan kimanin shekara 57 da suka gabata.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Yarbawa ta yi Allah wadai da ziyara da kuma gudunmawar da Tinubu ya bayar a jihar Katsina

Sheikh Al-Sabuni: An yi jana’izar tsohon limamin masallacin Harami
Sheikh Al-Sabuni: An yi jana’izar tsohon limamin masallacin Harami Hoto: Aminiya
Source: UGC

Sheikh Al-Sabuni mai shekaru 91 ya kwanta dama a garin Yelwa a kasar Turkiyya, a ranar Juma’a, 6 ga watan Sha’aban 1442 Hijiriyya.

An haifi Sheikh Al-Sabuni ne a kasar Syria, kuma ya rubuta litittafai masu yawa a kan ilimin tafsirin Al-Kur’ani mai girma, ciki har da “Taisiru Karimur Rahman Fi Tafsiri Kalamul Mannan,” wanda aka fi sani da suna Tafsirin Sabuni.

Marigayin ya shafe kimanin shekara 28 yana koyarwa a Tsangayar Shari’ar Musulunci da ke Jami’ar Ummul Kura da kuma Tsangayar Ilimi da Tarbiyya ta Jami’ar Musulunci ta Sarki Abdul Aziz, dukkansu a birnin Makkah, jaridar Aminiya ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Dalla-dalla: Hanyoyin da za ka bi don yin rijistar jarabawar UTME na 2021

A wani labarin, mun ji cewa manyan Limaman Harami sun hadu domin tsara Jadawalin sallolin Taraweeh da Tahajjud na watan Ramadana.

Tuni dai hukumomin kasar ta Saudiyya suka fitar da jerin sunayen manyan limaman da za su jagoranci bayar da sallolin Tarawi da Tuhajjud a masallacin Harami da ke kasa mai tsarki a azumin wannan shekarar ta 2021.

Hakan na kunshe ne a cikin wata wallafa da shafin Twitter na Haramain Sharifain ya yi a ranar Laraba, 24 ga watan Maris.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit

Online view pixel