'A Ina Ka Koyi Turanci Mai Kyau Haka': Trump Ya Yi Mamakin Shugaban Ƙasa a Afirka

'A Ina Ka Koyi Turanci Mai Kyau Haka': Trump Ya Yi Mamakin Shugaban Ƙasa a Afirka

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya yaba da Turanci na shugaban Liberia, Joseph Boakai, yana mamakin yadda yake magana cikin kwazo
  • Boakai ya ce, “Liberia abokiyar Amurka ce tun tuni,” inda ya gode wa Trump bisa damar ganawa da shi
  • Trump ya tambayi Boakai inda ya koya Turanci mai kyau haka inda ya ce abin ban sha’awa ne kuma ya yi mamaki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Liberia - Shugaban Amurka Donald Trump a ranar Laraba ya yaba da yadda shugaban kasa a Afirka ya ke Turanci mai kyau.

Trump ya yabi shugaban Liberia, Joseph Boakai ke amfani da harshen Turanci a wata ganawa da shugabannin Afirka.

Trump ya yi shagube ga shugaban kasa a Afirka
Trump ya yi mamakin Turancin shugaban Liberia. Hoto: Donald Trump.
Source: Twitter

BBC News ta yada bidiyon Trump inda yake mamakin yadda Boakai ya ke amfani da harshen Turanci.

Kara karanta wannan

Shugaban Amurka ya gana da Firaministan Isra'ila, an ji abin da suka tattauna kan Iran

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Trump ya ki gayyatar Najeriya a Afrika

Hakan ya biyo bayan ziyarar Trump a Afirka inda ya gayyaci shugabannin kasashen Nahiyar da dama.

Sai dai Trump bai gayyaci Najeriya daga cikin waɗanda zai yi ganawar da su ba wanda ya sa yan adawa su ke shagube ga Bola Tinubu.

Atiku Abubakar ya ce ƙin gayyatar Najeriya a taron kasashen Afirka biyar da Donald Trump zai yi wulakanci ne ga Bola Tinubu.

Ya ce rashin gayyatar ba kuskure ba ne, illa hukunci ne mai zafi kan gazawar Najeriya a ƙarƙashin jagorancin Tinubu.

Atiku ya kuma ce Bola Tinubu ya lalata martabar Najeriya a idon duniya, inda ya jaddada cewa ADC na shirin ceto ƙasar.

Trump na ziyarar aiki a Nahiyar Afirka
Donald Trump ya gana da shugaban kasar Laberia. Hoto: Donald J Trump.
Source: Getty Images

Trump na ganawa da shugabannin Afrika

Trump yana karɓar jawaban wasu shugabannin Afirka da da dama cikinsu suka yi amfani da yaren su na gida, sai Boakai ya yi magana da Turanci.

Kara karanta wannan

'Ya yi masa halacci': An fadi alakar Buhari da Tinubu bayan zargin sabani

Boakai ya ce:

“Liberia abokiyar Amurka ce tun tuni kuma muna goyon bayan manufarka ta ‘Mayar da Amurka babba, Muna godiya da wannan dama.”

Trump ya bayyana sha’awa da mamaki game da yadda Boakai ya yi jawabi da kyau, inda ya tambaya:

“Ingilishi mai kyau. Ina ka koya haka?”

Boakai ya yi dariya kafin ya amsa, sai Trump ya sake tambaya:

“A Liberia?”

Boakai ya ce:

“Eh, ranka ya dade.”

Trump ya ce:

“Wannan abin ban sha’awa ne. Akwai wasu a wannan teburin da ba sa magana da kyau haka ma.”

An kafa Liberia ne a 1822 daga tsofaffin bayin bakar fata daga Amurka, kuma Turanci ne harshensu a hukumance tun daga wancan lokaci, cewar Tribune.

Duk da cewa ana amfani da yarukan gargajiya daban-daban, Turanci ne yaren ilimi, gwamnati da diflomasiyya a fadin kasar Liberia.

Trump ya gana da Firaministan Isra'ila, Netanyahu

Mun ba ku labarin cewa Firaministan Isra'ila ya kai ziyara ƙasar Amurka a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa domin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

Kara karanta wannan

Yobe: Hadimin gwamna ya yi murabus, ya faɗi dalilansa na shiga jam'iyyar ADC

Benjamin Netanyahu ya gana da Shugaba Donald Trump a fadar White House, kuma sun tattauna kan batatutuwa da dama ciki har da yakin Iran.

Netanyahu ya jaddada cewa Isra'ila na nan a kan bakarta na shafe ƙungiyar Hamas mai mulki a Gaza nan ba da jimawa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.