Haraji: Trump Ya Yi Sabuwar Barazana ga Najeriya da Kasashen BRICS
- Shugaban Amurka, Donald Trump, na shirin kakabawa kasashen BRICS karin harajin kashi 10 cikin 100
- Najeriya na cikin jerin kasashen da harajin zai shafa, wanda zai iya janyo koma-baya ga fitar da kayayyaki ketare
- Masana sun ce wannan karin haraji zai kara dagula tattalin arzikin Najeriya da ke fama da hauhawar farashi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Tattalin Najeriya na iya sake fuskantar matsin lamba idan shugaban Amurka, Donald Trump, ya aiwatar da shirin kara harajin kashi 10 ga kasashen da ke goyon bayan BRICS.
Wannan mataki na zuwa ne bayan taron BRICS da aka kammala a Brazil, inda shugabannin kungiyar suka soki harajin Trump.

Source: Twitter
Al-Jazeera ta wallafa cewa shugabannin BRICS sun soki matakin suna cewa ya saba doka kuma zai cutar da tattalin arzikin duniya.
Hakan na zuwa ne yayin da Najeriya ke cigaba da kokarin fadada hanyoyin samun kudin shiga ta fitar da kayayyaki, musamman bayan faduwar darajar man fetur.
Harajin zai shafi fitar da kaya zuwa Amurka
Tun a ranar 2 ga Afrilu 2024, Trump ya fara maganar kakabawa kasashe 185 harajin kashi 10 cikin 100, ciki har da Najeriya.
Yanzu kuma ya ce za a kara wani karin haraji na kashi 10, wanda zai kai jimillar haraji da Najeriya ke biya zuwa kashi 24 cikin 100.
Masana tattalin arziki sun bayyana cewa karin harajin zai shafi fitar da kayayyaki kamar danyen mai, sauran sinadarai, da kayayyakin noma zuwa Amurka.
Trump ya ba kasashe wa’adin tattaunawa
Trump ya ba kasashen da abin ya shafa wa’adin watanni uku don kulla yarjejeniya da Amurka kafin 1 ga Agusta.
Rahotanni sun nuna cewa Birtaniya da Vietnam ne kadai suka cimma matsaya da kasar Amurka kan lamarin.
Sai dai Najeriya na ci gaba da kasancewa cikin kasashen da ba su kai ga amincewa da sharuddan ba, lamarin da ke kara jefa kasuwancin tsakanin bangarorin biyu cikin hadari.

Source: Facebook
Halin da tattalin Najeriya ke ciki
Najeriya na fama da hauhawar farashi tun daga 2023, inda rahotannin CBN suka ce hauhawar farashi ta kai kashi 34.2 cikin 100 a Yuni 2024, sai dai daga baya ya ragu zuwa kashi 27.5.
Sai dai sabon harajin da Amurka ke kokarin aiwatarwa na iya kassara kokarin da Najeriya ke yi na fitar da kaya da bunkasa masana’antu.
Yadda matakin Trump zai shafi Najeriya
Vanguard ta wallafa cewa fiye da kashi 90 cikin 100 na kayayyakin da Najeriya ke fitarwa zuwa Amurka danyen mai ne da kayayyakin da suka shafi man fetur.
Masana sun yi gargadi da cewa idan har Amurka ta aiwatar da wannan karin haraji, zai iya janyo cikas ga burin Najeriya na fita daga dogaro da fetur kadai wajen samun kudin shiga.
Dan Najeriya ya sace kudin taron Trump
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta gano wani dan Najeriya da ake zargi da damfara a kasar.
Wani dan Najeriya ne ake zargi da damfarar wani mutum ya tura masa makudan kudi kan rantsar da shugaba Donald Trump a wa'adi na biyu.
A yanzu haka an gano yadda mutumin ya yi amfani da imel din bogi ya karbi miliyoyin kudin kuma ya tura su ta wasu asusun ajiya.
Asali: Legit.ng


