Me Ya Yi Zafi?: Trump na Barazanar Korar Attajirin Duniya Elon Musk daga Amurka

Me Ya Yi Zafi?: Trump na Barazanar Korar Attajirin Duniya Elon Musk daga Amurka

  • Shugaba Donald Trump ya gargadi Elon Musk da cewa yana dab da rufe harkokinsa a Amurka, ya koma Afirka ta Kudu
  • Musk ya yi barazana ga sanatocin da ke goyon bayan dokar "Big Beautiful Bill", yana mai cewa zai hana su lashe zaɓen fitar da gwani
  • Sai dai Trump ya ce Musk ya dogara da tallafin da Amurka ke ba shi, kuma ba tare da hakan ba, ba zai iya ci gaba da kasuwanci ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya fitar da wani gargaɗi kan korar tsohon mai ba shi shawara, Elon Musk, daga Amurka.

Trump ya yi barazanar cewa Elon Musk, wanda shi ne mafi kudi a duniya a yau, ya kusa rufe harkokinsa a Amurka ya koma Afirka ta Kudu.

Kara karanta wannan

An taso Firaministan Isra'ila a gaba bayan gama yaƙi da Iran, ya fara roƙon arziƙi

Elon Musk na fuskantar barazanar kora daga Amurka saboda adawarsa ga dokar 'BBB'
Donald Trump, shugaban Amurka, ya magantu kan shirin mayar da Elon Musk Afirka ta Kudu. Hoto: Chip Somodevilla
Source: Getty Images

Trump ya wallafa wannan gargaɗin ne a shafinsa na Truth Social a ranar Talata, yana mai cewa Elon Musk, na iya barin ƙasar sakamakon adawarsa ga dokar "Big Beautiful Bill".

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Elon Musk na adawa da dokar 'BBB'

Rikici ya sake barkewa tsakanin Musk da Trump bayan shiru na wasu makonni da suka yi tun bayan fadan su da ya kai ga fito-na-fito a bainar jama’a.

Yayin da majalisar dattawan Amurka ke muhawara kan dokar “Big, Beautiful Bill” a ranar Litinin kafin kada ƙuri’ar ƙarshe, Elon Musk ya yi barazana ga 'yan majalisar da ke goyon bayan dokar.

Elon Musk ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin cewa:

“Abin kunya ne a ce dukkanin ‘yan majalisar da suka yi yaƙin neman zaɓe kan rage kashe kuɗi, yanzu sun koma suna goyon bayan dokar da za ta jawo ƙaruwar bashi mafi girma a tarihin ƙasar!”

Kara karanta wannan

Jagororin adawa sun dura a kan Trump, an gargade shi kan shiga shari'ar Netanyahu

Ya ƙara da cewa:

“Zan tabbatar sun fadi zaɓen fitar da gwani mai zuwa, ko da kuwa shine abin ƙarshe da zan yi a duniya.”
Elon Musk ya ci gaba da wallafa saƙonnin da ke sukar dokar har yana barazanar wallafa hotunan 'yan majalisar da ke goyon bayanta.

Trump ya yi martani ga Elon Musk

A martaninsa, Trump ya ce tun farko Elon Musk ya san cewa yana adawa da shirin hana amfani da motocin lantarki, tun ma kafin ya mara masa baya a lokacin zabe.

A baya, Trump ya zargi Musk da ƙin yarda da dokar ne kawai saboda ta na da wani sashe da zai iya cire tallafin da ake ba kamfanonin EV, amma Musk ya musanta hakan.

Elon Musk ya yi barazanar hana duk wani sanatan Amurka cin zaben fitar da gwani idan suka goyi bayan dokar 'BBB'
Shugaban kamfanin Tesla, dandalin X, Elon Musk. Hoto: @elonmusk
Source: Getty Images

Trump ya bayyana cewa:

"Ba mu da matsala da motoci masu amfani da lantarki, amma a ce sai an tilasta kowa ya yi amfani da su, wannan ne ba za mu yarda da shi ba.

Kara karanta wannan

Sabuwar matsala: Isra'ila za ta gurfanar da Netanyahu, Trump ya nemi afuwa

"Elon zai iya samun tallafin da babu wani dan Adam da ya same shi a tari, amma idan har muka cire tallafin nan, to fa sai dai ya rufe shagonsa ya koma asalin kasarsa, Afrika ta Kudu."

Trump ya kara da cewa:

"Idan muka dakatar da harba rokoki zuwa sama, ko tauraron dan Adam, ko muka daina hada motoci masu amfani da lantarki, lallai kasarmu za ta samu rarar kudi masu yawa.
"Ina ga akwai bukatar mu ba hukumar DOGE damar yin nazari kan wannan tunanin, ta yi nazari mai zurfi, kamar sai ya fi ko? Za mu samu rarar kudi masu yawa."

Elon Musk ya yi nadamar fada da Trump

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Elon Musk, attajirin duniya, ya bayyana nadamarsa kan wasu kalaman da ya taba yi game da shugaban Amurka, Donald Trump.

Musk ya amince cewa ya yi amfani da kalmomi masu tsauri fiye da kima, musamman lokacin da ya zargi Trump da ƙirƙiro kasafin kuɗi da zai janyo illa ga tattalin arzikin ƙasar.

Rigimar tsakanin su ta sake ɗaukar zafi bayan Trump ya bayyana cewa ba shi da niyyar sulhu da Musk, yana mai cewa attajirin ya ɓata masa rai matuƙa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com