Bayan Amincewar Saudiyya, an Sanya Ranar da za a Binne Aminu Dantata a Madina

Bayan Amincewar Saudiyya, an Sanya Ranar da za a Binne Aminu Dantata a Madina

  • Hukumomin Saudiyya sun amince a binne Alhaji Aminu Alhassan Dantata a birnin Madina, inda ake sa ran zai makwabtaka da matarsa
  • Za a shirye binne fitaccen dan kasuwar ne a Masallacin Annabi a ranar Litinin, 30 ga Yuni, 2025, wanda ke nuna girman darajar Dantata
  • An gudanar da jana'izar Ga'ib a Kano, inda dubban mutane suka halarta, tare da tunawa da dumbin gudummawar sa ga ci gaban ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Hukumomin Saudiyya sun amince a binne Alhaji Aminu Alhassan Dantata, fitaccen ɗan kasuwa kuma mai taimakon jama'a a Madina.

Za a binne marigayi Aminu Dantata a birni mai tsarki na Madina, don cika burinsa kwanciya kusa da kabarin marigayiyar matarsa, Rabi'a, wacce ta rasu a 2023.

Saudiyya ta amince a binne marigayi Alhaji Aminu Dantata a birnin Madina
Marigayi Alhaji Aminu Dantata ya rasu yana da shekaru 94 a duniya. Hoto: @SasDantata/X
Source: Twitter

Za a binne Dantata a birnin Madina

An shirya binne marigayi Dantata ne da sanyin safiyar Litinin, 30 ga Yuni, 2025, a Masallacin Annabi, Masjid an-Nabawi, ɗaya daga cikin wurare mafi tsarki a Musulunci, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Ɗan ƙasar Isra'ila ya yanke jiki ya fadi a otel ɗin Abuja, ya mutu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan gata na musamman, ganin tsauraran dokokin Saudiyya kan binne waɗanda ba mazauna ƙasar ba, ya nuna girmama Dantata da ake yi a duniya.

Mustapha Abdullahi Junaidu, sakataren Dantata, ya sanar da amincewar a ranar Lahadi, 29 ga Yuni, yana mai cewa:

"Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulilah Alhamdulillah, na samu amincewa daukar Aminu Alhassan Dantata daga Abu Dhabi zuwa Madina, za a binne shi gobe da safe da yardar Allah."

An samu tsaiko wajen tabbatar da hakan saboda matsalolin takardu, yayin da ofisoshin Saudiyya suke a rufe a ƙarshen mako, wanda ya jinkirta shirye-shiryen da suka dace.

Gwamnatin Najeriya ta taimaka wajen samun izinin jigilar gawar Dantata daga Abu Dhabi, inda ya rasu a ranar Juma'a, 27 ga Yuni, bayan gajeriyar rashin lafiya yana da shekaru 94.

An yi wa Dantata jana'izar Ga'ib a Kano

An gudanar da jana'izar Ga'ib, a ranar Asabar a Masallacin Umar Bin Khattab da ke Kano, Najeriya, karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Khalil, shugaban m ajalisar malaman Kano, tare da Sheikh Ibrahim Daurawa na hukumar Hisbah ta Kano.

Kara karanta wannan

An yi babban rashi: Fitaccen ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Aminu Ɗantata ya rasu

Dubban mutane ne suka halarci, ciki har da manyan jami'an gwamnati irin su mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau Jibrin.

Sauran wadanda suka halarta sun hada da 'yan majalisar zartaswa ta jihar Kano, da kuma manyan ƴan kasuwa, wanda ke nuna zurfin tasirin Dantata a jiha da kasa baki daya.

Sheikh Khalil ya bayyana marigayi Dantata a matsayin mai son addini kuma jagoran al'umma wanda taimakonsa ya shafi rayuka marasa adadi ta hanyar ba da kuɗi ga makarantu, asibitoci, masallatai, da cibiyoyin tallafi a faɗin Arewacin Najeriya.

An bayyana Alhaji Aminu Dantata a matsayin mai tausayi da ya taimakawa al'ummar Arewa
Marigayi Alhaji Aminu Dantata ya rasu yana da shekaru 94 a duniya. Hoto: @SasDantata/X
Source: Twitter

Tasirin Dantata ga Arewa daga Najeriya

Dantata, kawun attajirin Afirka, Aliko Dangote, ya gina daular kasuwanci ta hanyar kamfanin Alhassan Dantata & Sons, wanda ya haɗa da gine-gine, masana'antu, noma, mai da gas.

Ya kafa kamfanin Express Petroleum & Gas Company Ltd. kuma ya taka rawa wajen kafa bankin Jaiz, bankin Musulunci na farko wanda ba ya karɓar riba a Najeriya.

Gudummawarsa ga kwamitin tsara kundin tsarin mulkin Najeriya na 1979 ya ƙara ƙarfafa sunansa a matsayin mai gina ƙasa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sake ɗauko mutumin Buhari, ya ba shi babban muƙami a gwamnatinsa

Alhaji Aminu Dantata ya rasu a Abu Dhabi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, fitaccen ɗan kasuwar Kano, Alhaji Aminu Ɗantata, ya rasu a daren ranar Juma'a, 27 ga Yuni, 2025, yana da shekaru 94.

Ɗantata ya rasu ne a Abu Dhabi, babban birnin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, a cewar ɗaya daga cikin makusantansa Sanusi Dantata.

Tsohon mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya ce Kano da Najeriya sun yi babban rashin dattijo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com