Gabas Ta Tsakiya Ta Sake Rikicewa: Isra'ila Ta Kashe Kwamandan Hamas a Zirin Gaza

Gabas Ta Tsakiya Ta Sake Rikicewa: Isra'ila Ta Kashe Kwamandan Hamas a Zirin Gaza

  • Sojojin Isra'ila sun tabbatar da kashe babban kwamandan Hamas, Hakham Muhammad Issa Al-Issa, a wani harin sama a Gaza
  • An kashe Hakham, wanda ya kafa reshen soji na Hamas, a wani aiki na haɗin gwiwa tsakanin IDF da hukumar tsaro ta Isra'ila
  • IDF ta ce Hakham ne ya tsara kisan kiyashin da aka yi wa Isra'ilawa a ranar 7 ga Oktoba kuma ya taimaka wajen gina sojojin Hamas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Isra'ila - Sojojin Isra'ila sun tabbatar da kashe babban kwamandan Hamas, Hakham Muhammad Issa Al-Issa, a wani harin sama da suka kai a Birnin Gaza.

An ruwaito cewa an kai harin ne kan Hakham Muhammad Issa Al-Issa, wanda yake ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa Hamas da kuma reshenta na soji.

Isra'ila ta tabbatar da cewa ta kashe Hakham Al-Issa, kwamandan sojan Hamas
Hakham Muhammad Issa Al-Issa, daya daga cikin manyan kwamandojojin Hamas da Isra'ila ta kashe. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Sanarwar IDF a shafinta na X ya nuna cewa an kashe Hakham ne a wani aiki na haɗin gwiwa tsakanin rundunar tsaron Isra'ila (IDF) da hukumar tsaron Isra'ila a ranar Juma'a a unguwar Sabra.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sake ɗauko mutumin Buhari, ya ba shi babban muƙami a gwamnatinsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matsayin Hakham a Hamas da ayyukansa

A cewar IDF, Hakham na ɗaya daga cikin sauran manyan shugabannin Hamas a Zirin Gaza, kuma ya yi aiki a matsayin shugaban hedikwatar tallafin yaƙi na Hamas.

Rahoton Hindustan Times ya nuna cewa Hakham ya taka muhimmiyar rawa a tsare-tsaren soji na Hamas kuma ya shiga cikin gina da horar da sojojinta.

An kuma rahoto cewa Hakham ne ya taimaka wajen tsara harin ranar 7 ga Oktoba, 2023, a kan Isra'ila, wanda ya kashe mutane sama da 1,200 kuma ya kai ga sace wasu sama da 250.

Duk da cewa IDF ba ta ba da cikakkun bayanai game da rawar da ya taka ba, jami'ai sun ce ya ci gaba da taimakawa wajen kai hare-hare kan Yahudawa da sojojin Isra'ila a kwanakin baya.

Isra'ila ta zargi Hakham da kitsa harin kisan kiyashin da aka yi wa Isra'ilawa a ranar 7 ga Oktoba.
Shugaban kasar Isra'ila, Benjamin Natanyahu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Abin da rundunar Isra'ila ta ce kan kisan Hakham

Rundunar IDF ta wallafa a cewa:

Kara karanta wannan

Isra'ila ta fadi yadda ta shirya kashe jagoran addinin Iran, Ayatollah Khamenei

"An kashe Hakham Muhammad Issa Al-Issa — ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa reshen soji na Hamas.
"Issa ya jagoranci kafa sojojin Hamas, horar da su, da kuma ya tsara kisan kiyashin da aka yi a Isra'ila a ranar 7 ga Oktoba.
"A matsayinsa na shugaban rundunar kai dauki a lokacin yaki, ya ci gaba da kai hare-hare ta sama da ta ruwa kan Isra'ilawa.
"IDF da ISA za su ci gaba da gano da kawar da duk 'yan ta'addar da suka shiga cikin kisan kiyashin ranar 7 ga Oktoba."

Isra'ila ta hallaka shugaban Hamas

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kasar Isra'ila ta kara kai mummunan hari zuwa birnin Beirut na kasar Lebanon a karshen watan Yulin 2024.

Hukumomin Isra'ila sun tabbatar cewa harin ya yi mummunar barna a inda sojojin Iran ke jiran ko-ta-kwana ciki har da kashe babban kwamandan kungiyar Hamas.

Harin na zuwa ne bayan bayanai da suka nuna cewa ana zargin Isra'ila da kashe jagoran Hamas, Isma'il Haniyeh a wani harin da ta kai Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com

iiq_pixel