Bayan Tsagaita Wuta, Iran Ta Kama Masu Yi wa Isra'ila Leken Asiri 6, Ta Kashe Su

Bayan Tsagaita Wuta, Iran Ta Kama Masu Yi wa Isra'ila Leken Asiri 6, Ta Kashe Su

  • Iran ta fara babban samame kan waɗanda ake zargi da leƙen asiri ga Isra'ila, inda ta kashe shida kuma ta kama daruruwan mutane
  • Hukumomi sun ce samamen martani ne ga "kutsen tsaro na Isra'ila," wanda ya ba da damar kashe kwamandojin IRGC da masana kimiyya
  • Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama sun nuna damuwa kan saurin kashe-kashe da kama mutane da Iran ke yi ba tare da shari'ar adalci ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Iran - Iran ta fara wani babban samame kan waɗanda ake zargi da haɗa kai da jami'an leƙen asiri na Isra'ila, inda ta kashe mutum shida kuma ta kama daruruwan mutane.

Hukumomi sun bayyana wannan a matsayin yaƙin cikin gida da Iran ke yi don kare tsaron ƙasar biyo bayan yaƙin kwanaki 12 da yi da Isra'ila.

Kara karanta wannan

Iran ta bude wuta kan 'yan leken asiri bayan yakin kwanaki 12 da Isra'ila

Iran ta kara zafafa samamen da take kai wa wadanda take zargi suna yi wa Isra'ila leken asiri
Shugaban kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu tare da Shugaban Iran, Ali Khamenei. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jami'ai sun kuma ce wannan samamen martani ne ga abin da suka kira "kutsen tsaro ta hanyar 'yan leƙen asirin Isra'ila da ba a taɓa gani ba," inji rahoton Reuters.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tasirin fitar da bayanan sirrin Iran

A cewar gwamnatin Iran, bayanan sirrinta da aka fitar sun ba da damar kashe manyan kwamandojin rundunar IRGC da masana kimiyyar nukiliya a lokacin rikicin.

Iran ta danganta waɗannan ayyukan ga babbar kungiyar leken asirin Isra'ila, watau Mossad, wacce ta yi zargin tana aiki tare da masu leken asirin cikin gida.

Kamfanin dillancin labarai na Fars ya ruwaito, wasu majiyoyin IRGC da ba a bayyana sunayensu ba suna cewa:

"Kungiyar leƙen asirin Isra'ila ta samu bayanan sirri masu yawa a Iran. Tun lokacin da Isra'ila ta kai hari kan Iran a ranar 13 ga Yuni, an kama mutane sama da 700 da ke da alaƙa da wannan cibiyar."

Kara karanta wannan

Gaza: An gano yadda mutane 870 suka mutu a kwanaki 12 na yaƙin Iran da Isra'ila

An rahoto cewa an kashe maza uku da ake zargi da leƙen asiri ga Isra'ila a lokacin yaƙin, kuma an rataye wasu uku a ranar Laraba, kwana ɗaya kacal bayan yarjejeniyar tsagaita wuta.

Yaƙi da masu leƙen asiri a Iran

Ma'aikatar leƙen asiri ta Iran ta bayyana lamarin a matsayin "yaƙi marar ƙarewa" da take yi kan masu leƙen asiri na ƙasashen waje.

A cikin wata sanarwa, da Arise News ta rahoto, ma'aikatar ta ce:

"Muna yaki ne da makirce-makircen da hukumomin leƙen asiri na Yammacin Turai da kuma na Yahudawa ke yi don kawo tashin hankali a ƙasarmu."

Sai dai, ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama sun nuna damuwa game da saurin kashe wadanda ake zargi da Iran ke yi da kuma kamen da ta ke yi ba tare da shari'a ba.

Ana zargin Iran na kashe wadanda ake zargi da leken asiri ba tare da an yi shari'a ta adalci ba
Shugaban koli na kasar Iran, Ali Khamenei. Hoto: Getty Images
Source: AFP

Kungiyoyin kare haƙƙin Bil'adama sun magantu

Wata ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta duniya ta ce:

“Wannan tsarin yana nuna al’adun Iran na tsawon lokaci na tilasta wadanda aka kama yin bayani don amsa laifinsu da kuma gudanar da shari’o’in da ba babu adalci a cikinsu."

Kara karanta wannan

Rufa rufa ta ƙare: An gano mummunan halin da Iran ta jefa Isra'ila bayan tsagaita wuta

Wani mai sharhi kan siyasa, ya shaida wa BBC cewa:

"Jami'an tsaro yanzu sun koma kama marubuta, sojojin baka, masu fada aji da kuma iyalan wadanda suka yi zanga-zanga a baya, ba wai iya wadanda ake zargi da leken asiri ake kama wa ba."

Iran ta rataye dan leken asiri, Shayesteh

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Iran ta rataye Mohammad-Amin Mahdavi Shayesteh a ranar Litinin, bisa zargin leƙen asiri ga Isra'ila da kuma alaƙa da gidan talabijin na ƙasashen waje.

Wannan ya biyo bayan kisan wani da ake zargin wakilin Mossad ne, Majid Mosayebi, a ranar Lahadi. Hukumar shari'ar Iran ta ce za ta gaggauta shari'o'in tsaro.

Kungiyar Amnesty International ta nemi Iran da ta dakatar da duk wani zartar da hukuncin kisa, tana mai zargin cewa Iran tana take haƙƙin waɗanda take kamawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com