Yakin Isra'ila: Babban Sirrin da Iran Ta Ɓoye wa Duniya Ya Fara Fitowa, Masani Ya Yi Bayani
- Alamu sun nuna akwai yiwuwar Iran na da wani wuri da ya fi ko'ina sirri wanda duniya ba ta sani ba a kudancin cibiyar nukiliyar Fordow
- Wani masani ya bayyana cewa wurin wani tsauni ne mai girma, kuma ana zargin Iran ta haƙa rami mai zurfi a cikinsa
- Wannan na zuwa ne a lokacin da ake ta ce-ce-kuce kan hare-haren da Amurka ta kai cibiyoyin nukiliyar Iran, wasu na ganin an kwashe na'urorin wurin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Tehran, Iran - Amurka ta yi iƙirarin lalata duka muhimman cibiyoyi uku da Iran take shirin kera makamin kare dangi watau nukiliya.
Sai dai kwanaki biyu kafin jiragen Amurka su jefa bama-bamai mafi girma da aka yi amfani da su tun bayan yaƙin duniya na II, an ga motocin ɗibar kaya a kusa da cibiyar nukiliyar Iran ta ƙarƙashin kasa da ke Fordow.

Kara karanta wannan
'Ba haka ba ne,' Iran Ta yi martani bayan Trump ya ce zai zauna da ita kan nukiliya

Source: Getty Images
Jaridar Daily Mail ta tattaro cewa cibiyar Fordow ita ce mafi muhimmanci da ke tattare da muhimman kayayyakin kera makamin nukiliya a Iran.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amurka ta yi ikirarin ruguza cibiyar Fordow
Hotunan tauraron dan adam sun nuna dimbin motocin daukar kaya a wajen bakin ramin dutse da ke shiga babban sansanin nukiliyar Iran da ke cikin tsauni.
Donald Trump ya dage cewa an lalata shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran cikin hare-haren da ya ba da umarnin kai wa.
Haka nan kuma Hukumar Leken Asiri ta Amurka watau CIA da takwararta ta Isra’ila sun mara masa baya, suna mai cewa an lalata shirin Iran gaba ɗaya.
Amma kafin jiragen yakin su kai farmaki, an ruwaito cewa Iran ta yi gaggawar kwashe na’urorin ƙera nukiliya da sindarin uranium mai matukar hadari daga wurin.
Babbar tambayar da Ma’aikatar Tsaron Amurka ke yi a yanzu ita ce: “Ina suka kai kayan?”
Wane sirri ne Iran ta ɓoye wa Duniya?
Ɗaya daga cikin hasashen da masana suka yi shi ne da yiwuwar Iran ta mayar da su zuwa wata cibiyar sirri da ke cikin wani tsauni, wanda ke da nisan mil 90 daga Kudancin da Fordow.
Rahotanni sun nuna cewa wannan wuri dai ana kiransa da "Tsaunin Doom," ko tsaunin Pickaxe, kuma shi ne ake ganin wuri mafi sirri da Iran ta ɓoye wa duniya.
Tsaunin yana cikin tsaunukan Zagros a tsakiyar Iran, a gefen wani sansanin nukiliya na Natanz.

Source: Getty Images
Christoph Bluth, Farfesa a fannin harkokin kasa da kasa da tsaro daga Jami’ar Bradford, ya bayyana cewa:
“Mai yiwuwa Iran ta kwashe na’urorin ƙera nukiliya da uranium zuwa wasu wurare masu sirri kafin a kai hare-haren kwanan nan, ciki har da yiwuwar sun kai kayan tsaunin Pickaxe.”
Ya kara da cewa, tun da can, bayanan leken asiri sun nuna ana haƙa rami mai zurfi a tsaunin tare da wasu abubuwan da ke nuna yana da alaka da wata sabuwar cibiyar kera nukiliya.

Kara karanta wannan
Iran ta faɗi gaskiya kan illar da hare-haren Isra'ila suka yi wa cibiyoyin nukiliyarta
“Wurin na iya zama mai zurfin mita 100 daga saman kasa. Don haka akwai yiwuwar an boye na’urorin kirkirar nukiliya a can, amma a halin yanzu babu wata hujja kai tsaye da ke tabbatar da haka," in ji shi.
Iran ta hukunta yan leƙen asirin Isra'ila
A wani labarin, kun ji cewa ƙasar Iran ta hukunta wasu mutane da aka kama da laifin taimakawa hukumomin leƙen asiri na Isra'ila.
Rahotanni sun nuna cewa a kwanaki 12 da ta yi tana musayar wuta da Isra'ila, Iran ta yanke wa mutanen hukuncin kisa kuma ta zartar da shi.
Iran na zargin cewa bayanan sirri da aka bai wa Isra’ila na da nasaba da wasu kashe-kashen manyan jami’an gwamnati da suka faru a lokacin yakin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
