Iran Ta Bude Wuta kan 'Yan Leken Asiri bayan Yakin Kwanaki 12 da Isra'ila

Iran Ta Bude Wuta kan 'Yan Leken Asiri bayan Yakin Kwanaki 12 da Isra'ila

  • A cikin kwanaki 12 na yakin da aka gwabza da Isra'ila, Iran ta aiwatar da hukuncin kisa ga mutane shida bisa zargin aiki da Mossad
  • Wannan na zuwa bayan an damke mutane akalla 700 da ake zargin suna tattara bayanan sirrin Iran zuwa ga Isra'ila don kai mata hari
  • Lamarin ya jawo damuwa a tsakanin kungiyoyin kare hakkin dan Adam da ke zargin cewa Iran na amfani da karfi a kan wadanda ta kama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Iran – Hukumomin Iran sun gudanar da jerin kame da zartar da hukuncin kisa ga wasu mutane da ake zargi da alaka da hukumomin leken asirin Isra’ila.

Wannan mataki ya biyo bayan abin da jami’an Iran suka bayyana a matsayin “cin karo da tarihi” da hukumomin leken asiri na Isra’ila suka yi wajen kutsawa kasar.

Kara karanta wannan

'Ba haka ba ne,' Iran Ta yi martani bayan Trump ya ce zai zauna da ita kan nukiliya

An fafata tsakanin Iran da Isra'ila
Iran ta kama mutane da dama da ake zargi da leken asiri Hoto: Getty
Source: Getty Images

BBC ta wallafa cewa hukumomin Iran na zargin cewa bayanan sirri da aka bai wa Isra’ila na da nasaba da wasu kashe-kashen manyan jami’an gwamnati da suka faru a lokacin yakin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Isra’ila: Yadda aka kashe manya a Iran

Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewa daga cikin wadanda suka rasa rayukansu akwai manyan hafsoshi daga rundunar IRGC da kuma masana kimiyyar nukiliya da aka kai wa hari a Iran.

Kasar ta danganta wadannan hare-hare ga jami’an leken asirin Mossad na Isra’ila da ake zargin suna aiki a cikin kasar.

A lokacin rikicin kwanaki 12, hukumomin Iran sun kashe mutane uku da suka zarga da leken asiri domin Isra’ila.

A ranar Laraba - wato kwana daya bayan kiran dakatar da yakin - an sake aiwatar da hukuncin kisa ga wasu mutane uku bisa irin wannan zargi.

An kama daruruwan mutane a kasar Iran

Rahotanni sun ce tun daga wannan lokaci, hukumomi sun sanar da kama daruruwan mutane a fadin kasar bisa zargin leken asiri.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito: Trump zai shawo kan Iran da dala biliyan 30, manyan alkawura

Gidan talabijin na gwamnatin Iran ya haska wasu da aka kama da su ka amasa laifin cewa suna yiwa Isra'ila leken asiri a kasar.

Kasar Iran
Iran ta zartar da hukuncin kisa a kan wasu da ake zargi da leken asiri Hoto: Getty
Source: Getty Images

Lamarin ya sa kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun bayyana damuwa kan matakan da Iran ke dauka, inda aka yi zargin tana tilasta wa wadanda ake zargi amsa laifin da ba su aikata ba.

Rahotanni sun ce tun bayan harin Isra’ila kan Iran a ranar 13 ga Yuni, rukunin leken asirin Isra’ila ya kara aiki sosai a cikin kasar wajen tattara bayanai.

Hukumomin tsaro na Iran sun bayyana cewa sun kama “fiye da mutane 700 da ake zargi da alaka da wannan rukunin”.

Iran za ta sake gina makamin nukilya

A baya, mun wallafa cewa Iran tana ci gaba da tantance girman barnar da Isra’ila ta yi wa shirin nukiliyarta, bayan kwana 12 na hare-hare da suka shafi cibiyoyin bincike da kera makaman.

A cewar shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran, Mohammad Eslami, an fara shirin farfado da wuraren da aka lalata da zarar an kammala daukar kididdigar barnar da aka yi.

Amurka ta jefa makamai masu linzami kan muhimman cibiyoyi guda uku da ke da nasaba da shirin makamashi na Iran, lamarin da ya dakile ci gaba a fannin kera makaman.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng