'Mun Shirya': Khamenei Ya Gargadi Amurka da Isra'ila, Ya Ce Komai na Iya Faruwa a Gaba
- Jagoran addini a Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya yi magana bayan shafe kwana fiye da 10 ana yaƙi da Isra'ila wanda ya jawo asarar rayuka
- Ayatullah Ali Khamenei ya ce kasar tana da damar kai hari ga muhimman cibiyoyin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya da ke fama da rikice-rikice
- Ya ce Iran za ta iya sake kai irin wannan hari a nan gaba idan suka ga dama kuma babu wata ja da baya a kan haka
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Tun bayan sanar da shirin tsagaita wuta, jagoran addini, Ayatullah Ali Khamenei ya yi magana a karon farko.
Khamenei ya yi magana ne kan yakin da ya barke tsakanin Iran da Isra'ila inda ya ce sun samu gagarumar nasara.

Source: Getty Images
Jagoran da ke da mutunci matuka a Iran ya bayyana haka ne a yau Alhamis 26 ga watan Yunin 2025 a shafinsa na X.
Ana dakon matsayar Khamenei kan sulhu
Wannan gargadin na zuwa ne bayan shugaban Amurka, Donald Trump ya bukaci zaman sulhu tsakanin Iran da Isra'ila bayan arangama tsakanin kasashen biyu.
Sai dai jagoran addini a kasar, Ayatullah Ali Khamenei bai fitar da wata sanarwa ba kan lamarin zuwa yanzu da yaki ya lafa.
Hakan ya jefa shakku a zukatan al'umma da dama da suke tunanin makomar shirin tsagaita wuta duba da tasirin Khamenei a Iran.
Khamenei ne ke da ikon yanke shawara kan manyan lamura, hakan ya sa mutane da dama ke jiran jin matsayarsa game da tsagaita wutar.

Source: Getty Images
Khamenei ya fadi tasirin Iran a yaki da Isra'ila
Jagoran ya ce a yanzu Jamhuriyar Musulunci tana da damar kaiwa muhimman cibiyoyin Amurka hari a yankin.
Khamenei ya ce kuma kasar ta Iran za ta iya daukar mataki duk lokacin da ta ga dama a nan gaba.
Amma ya ce hakan zai faru ne idan gwamnati ta ga dacewa inda ya ce za ta sake daukar irin wannan matakin ba tare da jinkiri ba.
"A yanzu Jamhuriyar Musulunci tana da damar kaiwa muhimman cibiyoyin Amurka a yankin kuma za ta iya daukar mataki duk lokacin da ta ga dama inda ya ce babban lamari ne.
"Irin wannan mataki na iya maimaituwa a nan gaba idan har wani hari ta faru, makiyanmu tabbas za su dandana kudarsu."
Yan Isra'ila sun fadi wahalar da suka sha
A wani labarin, kun ji cewa wasu mazauna birnin Beersheba sun bayyana irin wahalar da suka shiga lokacin da Iran ta kai masu hari a Isra'ila wanda aka shafe fiye da kwana 10 ana yi.
An ce Yahudawan sun tabbatar da cewa duk da sun gudu sun shiga wuraren da aka gina don kariya, amma ƙarar faɗowar makamin ta gigita su wanda ya jawo asarar rayuka.
Daga cikin wadanda suka yi magana akwai wata mata mai suna, Merav Manay ta ce ta ɗauka mutuwa ce ta tunkaro su, tana mai cewa harin ya yi masu mummunar illa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
