Bayan Yaƙi da Isra'ila, Shugaba Trump Ya Faɗi Abin da Amurka Za Ta Tunkari Iran da Shi
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya nanata cewa yaƙi ya kare tsakanin Isra'ila da Iran domin kasashen biyu sun galabaita a kwanaki 12
- Trump ya bayyana cewa Amurka za ta koma teburin tattaunawa da wakilan Iran a mako mai zuwa domin ɗorawa daga inda aka tsaya
- Ya ce ba ya sha'awar ci gaba da tattaunawa game da makamashin nukiliyar Iran domin Amurka ta riga an lalata shirin ƙasar gaba ɗaya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
USA - Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya kara jaddada cewa yaƙi tsakanin Isra'ila da Iran ya kare bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.
Shugaba Trump ya sanar da cewa abu na gaba shi ne Amurka za ta gana da jami'an ƙasar Iran domin fara tattaunawa kan wasu muhimman batutuwa a makon gobe.

Source: Getty Images
Donald Trump ya bayyana haka ne yayin hira da manema labarai a taron kungiyar tsaro ta NATO wanda ya gudana a ƙasar Netherlands, cewar rahoton Al-Jazeera.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amurka za ta koma teburin tattaunawa da Iran
Trump ya yi bayanin cewa Amurka za ta zauna da wakilan Iran, domin ci gaba da tattaunawa kan nukiliya, wanda ɓarkewar yakin Isra'ila, ya dakatar a kwanakin baya.
“Ina mai tabbatar maku da cewa za mu tattauna da jami'an Iran mako mai zuwa, wataƙila ma mu sa hannu kan yarjejeniya, ban sani ba,” in ji Trump.
Wannan kalamai na Trump na zuwa ne bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Iran, ƙasashen da suka shafe kwanaki 12 suna musayar wuta.
Yaƙin ƙasar Isra'ila da Iran ya ƙare
Tun farko an fara musayar wutar ne ranar 13 ga watan Yuni, lokacin da Isra'ila ta kai farmakin ba-zata kan sojoji da cibiyar nukiliyar Iran.
Isra'ila ta yi ikirarin cewa ta ɗauki wannan matakin ne domin kare kanta daga barazanar shirin nukiliyar Iran, wanda ta ce yana iya ruguza ta gaba ɗaya.
Jim kaɗan bayan haka ne, Iran ta fara kai hare-haren ramuwar gayya kan Isra'ila, lamarin da ya yi sanadin kashe mutane da dama da jikkata wasu a ƙasashen biyu.
A daren Litinin da ta gabata, Shugaban Amurka ya sanar da cewa ƙasashen biyu sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta bayan kwanaki 12 da fara yakin.

Source: Getty Images
Me Amurka za ta tattauna a taronta da Iran?
Da yake jawabi a taron NATO yau Laraba, Trump ya ce ba shi sha'awar ci gaba da tattaunawa da Iran, yana mai jaddada cewa an rusa shirinta na mallakar makaman nukiliya.
Ya ce a halin yanzu yaƙi ya kare domin ƙasashen biyu duk sun galabaita, abu na gaba shi ne Amurka za ta zauna da wakilan Iran domin ci gaba da tattaunawa, in ji rahoton CNN.
Isra'ila ta sha wuta a hannun ƙasar Iran
A wani labarin, kun ji cewa Donald Trump bayyana cewa makamai masu linzami da Iran ta harba sun ragargaji Isra'ila sosai musamman a kwanakin karshe na yakin.
ShugabaDonald Trump ya jaddada cewa ba za su taɓa yarda jamhuriyar musulunci ta Iran ta ci gaba da haɓaka makamashin nukiliya ba.
Rahotanni daga Tehran sun nuna cewa Iran na tunanin ficewa daga yarjejeniyar hana yaɗuwar makamashin nukiliya (NPT).
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

