Wace Ƙasa Ta Yi Nasara tsakanin Iran da Isra'ila? Netanyahu Ya Yi Jawabi bayan Tsagaita Wuta

Wace Ƙasa Ta Yi Nasara tsakanin Iran da Isra'ila? Netanyahu Ya Yi Jawabi bayan Tsagaita Wuta

  • Firaministan Isra'ila ya yi ikirarin cewa ƙasarsa ce ta yi nasara a yakinnta da Iran, wanda ya shafe kwanki 12 ana musayar wuta
  • Benjamin Netanyahu ya ce Isra'ila ta yi nasarar ruguza barazana biyu a Iran, shirin nukuliya da ƙera makamai masu linzami 20,000
  • Wannan kalamai na Netanyahu na zuwa ne kwanaki kalilan bayan Iran da Isra'ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Israel - A cikin wani jawabi da ya yi a ranar Talata dangane da yaƙin da aka gwabza da Iran, Firaminista Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yi ikirarin samun nasara.

Netanyahu ya bayyana cewa Isra’ila ta samu “nasara ta tarihi” kan Iran, wadda za ta kasance abin tunawa har tsawon zamani.

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu.
Netanyahu ya yi ikirarin cewa Isra'ila ce ta samu nasara a yaki da Iran Hoto: Getty Image
Source: Getty Images

Jaridar The Times Of Israel ta ce wannan kalamai na zuwa ne bayan an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta shiga tsakani domin kawo ƙarshen rikicin da ya ɗauki kwanaki 12.

Kara karanta wannan

Kwana 1 da maganar tsagaita wuta, Isra'ila ta jajubo gagarumin zargi kan Iran

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace nasara Isra'ila ta samu kan Iran a kwanaki 12?

Benjamin Netanyahu ya ce Isra’ila ta kawar da "barazana guda biyu da ke iya hallaka ta," barazanar makaman nukiliya da kuma makamai masu linzami guda 20,000 da Iran ke shirin kerawa.

Firaministan ya ƙara da cewa Isra’ila na fuskantar barazanar rugujewa nan gaba kadan “da ba mu ɗauki mataki a yanzu ba.”

Ya kuma yaba da yadda Shugaban Amurka Donald Trump ya ɗauki mataki don kare Isra'ila daga barazanar nukiliyar Iran.

Netanyahu ya bayyana cewa wannan mataki da Amurka ta ɗauka na shigarwa Isra'ila faɗa, sakamako ne na zaman lafiya da abotar da ke tsakaninsu.

Benjamin Netanyahu ya yabawa sojojin Amurka

Ya ƙara da jinjinawa sojojin Amurka da suka lalata cibiyar habaka nukiliyar Fordo da ke karkashin ƙasa a Iran.

“Isra’ila ba ta taɓa samun aboki kamar Shugaba Trump ba, kuma ina matuƙar godiya da irin hadin gwiwar da muka yi,” in ji Netanyahu.

Kara karanta wannan

Iran ta faɗi yawan mutane da ta rasa da masu raunuka bayan yaki da Isra'ila

Ya yi wannan kalamai ne mintoci kaɗan bayan da Trump ya caccaki Isra’ila bisa harin da ta kai Iran duk da cewa an riga an sanar da tsagaita wuta, rahoton Yahoo News.

Benjamin Netanyahu da jagoran addinin Iran.
Gwamnatin Ista'ila ta yi ikirarin lalata cibiyoyin nukiliyar Iran Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Gwamna Isra'ila ta yi ikirarin illata Iran

Sai dai Netanyahu ya jinjina wa harin da Isra’ila ta kai wa Iran da safiyar Talata kafin tsagaita wutar ta fara aiki, wanda shi ne harin da Trump ya nuna fushi da shi a bainar jama’a.

Firaministan ya ce Isra’ila ta rushe shirin kera makaman linzami na Iran tare da jefa "mummunan raunuka mafi girma a tarihin gwamnatin Iran.

"Mun shafe shirin nukiliyar Iran, idan wani a Iran ya yi ƙoƙarin farfaɗo da shirin, za mu sake ɗaukar mataki da irin wannan ƙuduri domin dakile shirin nan take.”

Iran ta kawo karshen yaƙi da Isra'ila

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian ya tabbatar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninsu da Isra'ila bayan kwanaki 12.

Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa yaƙin na kwana 12 da Israila ta tilasta musu shiga domin kare kai da mayar da martani ya zo ƙarshe.

Sai dai gwamnatin Iran ta ce za ta kara kaimi domin farfaɗo da shirin nukiliyarta bayan wannan yaƙi da Isra'ila ta jawo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262