Kwamadan Sojojin Iran da Ya Addabi Isra'ila Ya Bayyana bayan 'Kashe' Shi a Yaki
- Bidiyo ya nuna shugaban Rundunar Quds, Esmail Qaani, a taron murnar harin Iran kan Isra'ila da sansanin Amurka a Qatar
- Esmail Qaani ya bayyana ne bayan ikirarin cewa an kashe shi a harin Isra’ila, amma sababbin bayanai sun musanta hakan
- Rahotanni sun ce Tehran na cigaba da gudanar da bincike kan yadda Isra’ila ke iya samun bayanai daga cikin dakarun Iran
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Rahotanni daga kafafen watsa labarai sun tabbatar da cewa shugaban rundunar sojin Iran ya bayyana bayan rade radin kashe shi.
Bincike ya nuna cewa shugaban rundunar Quds ta Iran, Esmail Qaani ya bayyana a wani taron gangami a Tehran.

Source: Getty Images
Legit ta hango Esmail Qaani ne a cikin wani bidiyo da Iran Nuances ta wallafa a X yayin murna bayan tsagaita wuta a yakin da ta yi da Isra'ila.
Taron dai an shirya shi ne a ranar Talata domin murnar harin makamai da Iran ta kai kan sansanin sojojin Amurka da ke Qatar.
Harin na ɗaya daga cikin farmakin ramuwar gayya da Iran ta kai kan hare-haren da Isra’ila da Amurka suka kai mata.
Bayanin rasuwar kwamandan rundunar Iran
A makon da ya wuce, New York Times ta wallafa rahoto da ke cewa an kashe Qaani a wani harin Isra’ila da aka kai Iran.
Fitowar bidiyo da kuma bayyanuwar Qaani a bainar jama’a na iya zama wata hujja da ke rushe wannan rahoto, tare da tabbatar da cewa yana raye kuma yana ci gaba da shugabanci.
Kwamandan Iran ya fara aiki a 2020
Esmail Qaani ya karɓi shugabancin rundunar Quds bayan kashe Qasem Soleimani a wani harin da Amurka ta kai a Bagadaza a shekara ta 2020.
Rahoton Jerussalem Post ya nuna cewa rundunar Quds na daga cikin sassan sojojin juyin juya halin Iran da ke hulɗa da ayyukan tsaro da ya shafi kasashen waje.
Tun cikin watan Oktoban 2024, ba a sake ganin Qaani a bainar jama’a ba, lamarin da ya jefa fargaba game da makomarsa.
A cigaba da shiga rudani game da shi musamman bayan harin da Isra’ila ta kai a Beirut, wanda ya kashe shugaba mai jiran gado a Hezbollah, Hashem Safieddine.
Iran na zargin samun bayanan tsaro daga Isra’ila
Iran na gudanar da bincike mai zurfi a cikin rundunar juyin juya halin, musamman bangaren da ke aiki da Hezbollah a Lebanon, saboda shakkun cewa Isra’ila na leƙan asiri a cikinsu.

Source: Getty Images
Wata majiya daga cikin binciken ta bayyana cewa:
“Iran na zargin cewa Isra’ila ta samu nasarar sanya 'yan leƙanta cikin dakarun Iran, musamman a ɓangaren Lebanon.
Abubuwan da suka faru a yakin Iran da Isra'ila
A wani rahoton, Legit Hausa ta tattaro muku wasu muhimman abubuwa shida da suka faru a kwana 12 da aka shafe ana yaki tsakanin Iran da Isra'ila.
Kai harin da Amurka ta yi kan cibiyoyin nukiliyar Iran na cikin manyan abubuwan da suka ja hankalin al'umma yayin yakin.
Batun rufe hanyar ruwan Hormuz ya ja hankalin duniya ganin cewa ta hanyar ake bi wajen isar da kaso mafi tsoka na danyen mai zuwa kasashe.
Asali: Legit.ng

