Iran Ta Faɗi Yawan Mutane da Ta Rasa da Masu Raunuka bayan Yaki da Isra'ila
- Kasar Iran ta sanar da wadanda suka mutu da kuma masu raunuka tun bayan harin Isra’ila da aka fara 13 ga Yunin 2025
- Ma'aikatar lafiya ta kasar ta ce mafi yawan mamatan fararen hula ne, ciki har da yara 13 da likitoci biyar da ma’aikatan ceto
- Shugaba Donald Trump na Amurka ya sanar da yarjejeniyar zaman lafiya, amma an ce ƙasashen sun sake kai wa juna hari
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Kasar Iran ta bayyana yawan mutane da suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka samu raunuka yayin fada tsakaninta da Isra'ila.
Iran ta ce an kashe fararen hula 610, wasu fiye da 4,700 kuma sun jikkata tun da yaƙi da Isra’ila ya fara ranar 13 ga Yunin 2025.

Source: Getty Images
Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma'aikatar lafiya, Hossein Kermanpour ya tabbatar, cewar The Economic Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda Trump ya nemi sulhu a tsananin Iran/Isra'ila
An ruwaito cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Iran.
A cewar shugaban, ƙasashen biyu sun amince da tsagaita wuta a matakai, Iran za ta fara tsagaita harin cikin awa shida masu zuwa.
Trump ya ce Isra’ila za ta bi bayanta da awa 12, sannan kowane ɓangare zai mutunta ɗayan yayin da ake cikin lokacin tsagaita wuta.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa Iran ta kai hari kan Isra’ila sa’o’i kaɗan bayan sanarwar da Trump ya yi game da tsagaita wutar.
Yawan mutane da suka mutu a Iran
Sanarwar ta ce mafi yawan wadanda aka rasa a Iran fararen hula ne da wasu ma'aikatan lafiya.
Sanarwar ta ce:
“Dukkansu fararen hula ne, ana cigaba da bayyana sabon adadin asarar rayuka."
“A cikin kwanaki 12 da suka wuce, asibitoci sun fuskanci abubuwan ban tausayi sosai."

Source: Getty Images
Likitoci da yawan yara da Iran ta rasa
Ma’aikatar lafiyar ta ce cikin waɗanda suka mutu har da yara 13, mafi ƙarancin shekaru na cikinsu shi ne dan wata biyu, cewar rahoton Tribune.
Iran ta ce sauran da suka mutu sun haɗa da likitoci biyar da ma’aikatan ceto, yayin da wasu asibitoci da motoci na gaggawa suka lalace.
An lalata asibitoci guda bakwai da motoci na gaggawa tara sakamakon harin da Isra’ila ke kaiwa, kamar yadda hukumar lafiya ta Iran ta tabbatar.
Fani-Kayode ya fadi darasin da Isra'ila ta koya
A baya, mun ba ku labarin cewa tsohon minista a Najeriya, Femi Fani-Kayode ya yi magana kan abin da ke faruwa tsakanin Iran da Isra'ila.
Fani-Kayode ya jinjinawa Iran bisa martanin da ta yi kan harin Isra'ila, yana cewa sun ci karensu ba babbaka tare da nunawa Isra'ila da sauransu tukuna.
Tsohon ministan ya ce Iran ta koyawa Isra'ila darasi mai tsauri, inda ya kara da cewa wannan ne mafi munin abin da ya taba faruwa da ita tsawon shekaru 77.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

